Sashe 20
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yanda yake kallonta shima yasa tace " *WAYIWAN NEDIS*(ina kwana)"
Kallonta yayi sosai kafin yace "amma ai na fad'a maki bana jin buzanci ko, gwara kimin fulatanci ko indianci sunfi sauk'i"
Kallon rainin hankali ta masa kafin ta girgiza kai tace "Ok *EN VETII JAMNA*(antashi lafiya)?"
Kallonta yayi saidai baiyi mamakin jin fulatanci daga bakinta ba, domin kuwa yasha samun su ita da Mama tana koya mata, murmushi ya mata yace " *NOI CHOMRII*(ya gajiya)?"
Shiru tayi dan kuwa ta manta sauran darusan da Mama ta koya mata, maida hankalinta tayi ga tv tana kallo, ganin ba zata amsa ba yasa ya kalli tv ya kalleta yace " sai son kallon india amma baki jin mai suke fad'a"
Harya wuce yaji tace " *KAISE HO TUM*(ya kake)?"
Dawowa yayi kusa da ita yace" *HUM THEEK HOON*(lafiya lau nake), *AUR TUM*(ke fa)?"
" *HUM BILKUL THEEK HOON*"
Dariya yayi yace "lallai ba laifi, inaga zanje dake india idan na tashi tafiya" da sauri ta dafe mararta tare da cije leb'e tace "wayyo mara ta ciwo take"
Matsowa yayi kusa da ita yace "ya dai miyake damunki?" wani kallo ta masa tace "ba komai" tab'e baki yayi ya ficewarsa daga gidan, haka ciwon ya fara takura ta amma ta daure.
Salman na fita gida ya nufa dan Mama tace yaje ya karb'o masu abinci, yana shiga Mama ce kad'ai zaune a falo, da sallama ya shigo ya zauna yana fad'in "Mama ku kad'ai zaune?"
Saida tayi hamma sannan tace "wallahi ni kad'ai duk sun tafi makaranta"
"Ok ina kwana?"
"Lafiya lau, antashi lafiya?"
"Lafiya lau Mama, ya gida ya gajiya?"
"Ba gajiya, ya d'iyata da jikin kuma, ina fata dai da sauk'i?"
"Um da sauk'i Mama tana nan lafiya"
Kallonshi tayi da kyau tace "ina fatan dai kana kula da ita baka mata cutar nan daka saba ko?" dariya yayi yace "Mama kenan aini bana dukanta idan b
laifi tamin ba, ku kuma baku ganin laifinta, shiyasa kullum kuke ganin nine mai laifi ba ita ba."
"Hmm, kaidai ka saba da narkarta kawai ko babu laifin fari bana bak'i kana jin dad'in dukanta."
Jingina yayi a kujeran kamar zai kwanta yace "to Mama yanzu ai na bari tunda ita ma ta rage tunda babu k'afafu da hannu d'aya"
Waro ido Mama tayi tace "aw kenan ciwon data ji kad'ai yasa ka daina dukanta? shiyasa taji dad'in zamanta gidan Khamis."
"A'a Mama ba haka nake nufi ba, nasan dai yanzu zata rage tsokana tunda ta samu rauni, ba zata iya jan fad'a ta ruga a guje ba."
Tab'e baki Maman tayi lokacin data mik'e tsaye tana fad'in "kaidai kasani kaci gaba da dukanta tana matarka, akwai ranar horo ko kuma idan ka mata bugun da zai b'aran mata da ciki, ai kaga saika huta."
Da k'arfi ya d'ago daga zaman da yayi cikin d'aga murya yace "ciki Mama, tace maki tana dashi?"
Juyowa Mama tayi tace "saita fad'amin tana da, bayan rashin lafiyar da Jawahir tace tayi ta kwana biyu harda su amai."
Shigewa tayi danta d'auko mashi abinci, shi kam shiru yayi gaba d'aya tunaninshi ya tafi akan abinda Mamar ta fad'a, harta fito ta aje masa kwanukan guda biyu bai masan ta aje ba.
Zaune Mama tayi tana kallonshi, gyara zamansa yayi yana kallon Mama yace "Mama wai da gaske yarinyar nan ciki ne da ita?"
Tsaki Mama tayi tace "kaji wani rainin wayo, tana matarka amma bakasan tana da ciki ba duk da rashin lafiyar da tayi, kodan baka nan?"
Cikin mamaki yace "amma Mama aini na d'auka wannan rashin lafiyar saboda wata matsala ce dake damunta, amai kuma saboda taci abincin da yafi k'arfinta ne shiyasa ta aman.?"
Hararanshi tayi dan ita a ganinta yana so ya b'oyene saboda baya so a sani ko kuma kunya, cewa tayi "wace irin damuwa ce zata ja mata rashin lafiya, kuma dan anci abinci mai yawa sai ayi amai.?"
To ganin Mama tak'i yarda ta fahimceshi yasa yace "Mama wai kun duba kayan nan kuwa?"
"E na duba naga sunyi sosai, saura kud'in d'inkin kayan ko?"
"To Mama nawa ya dace a saka kenan?"
"To ai basai na fad'a maka ba, babu wanda ya kaika samun mata a b'agas, tunda gashi za'a kai mata Lefe tana d'auke da juna biyu, aiko kaga kai dan baiwa ne, dan haka tuwon girma miyarsa nama kayi bajinta kawai."
Cike da damuwa ya kalli Mama yace "Mamaa, bana so kina cewa tana da cikin nan, ba tada komai fa"
Tab'e baki tayi tace "kaidai kasa ni, ni dai ka hanzarta kawo kud'in dan a samu akai kayan da wuri"
Mik'ewa yayi yasa hannu a cikin aljihu ya ciro kud'i masu yawa ya bawa Mama, karb'a tayi tana kallon kud'in kafin tace "wannan kud'in haka har nawa ne?"
Dariya yayi yace "Mama kuda gasunan a hannunku, ku irga mana"
"Kai bazan iya ba, idan ma na fara ba'cewa zanyi ka fad'amin kawai"
" Mama kenan, to d'ari biyar ne (500.000F CFA)"
Baki Mama ta washe tace "kai amma naji dad'i, yanzu ka tabbatarmin da kai mai yaba kyauta ne, gaskiya naji dad'i Allah ya maku albarka, Allah ya albarkaci aurenku, Allah ya bata lafiya ya rabata da abinda yake cikinta lafiya."
Ganin Mama tak'i fahimtarshi yasa sukayi sallama a haka, ya d'auki abinci ya kama hanyar gida zuciyarshi cike da wasi-wasi.
Yana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya mik'a mata tare da zaunawa kusa ita yana k'are mata kallo, wai mai ciki "to cikin wa?" ya tambayi kanshi.
Ummi kam dan danan ta cije leb'e saboda ciwon da mararta keyi, saida ta malmalo lomar fankasu daya sha jar miya zata kai bakinta, cak ta tsaya tare da kallon Salman.
Tunawa tayi jiya yace yana jin yunwa da Hajia tace ya d'auketa, kuma a iya saninta bata ga sanda yaci wani abu ba da idonta, dan haka ta mik'a masa plate d'in tace "ci"
Cike da mamakin abinda tayi ya girgiza mata kai yace "kici kawai"
Shagwab'ewa tayi tace "dan Allah kaci nasan kana jin yunwa, tun jiya baka ci komai ba."
Kallonta kawai yake kafin yace "ki fara ci, idan kin ida zanci"
Kai ta girgiza masa tace "bazan iya ciba yaya Salman"
Idonshi akan tv yace "parce que (saboda)?"
A ranta kam cewa tayi "saboda kana jin yunwa" amma a fili sai tace "saboda bazan iya ci ba alhalin kai baka ci ba."
K'yar idon Salman a kanta kamar zai had'iyeta, mamakin furcinta yake sosai da k'yar yace "Ummi miyasa kika damu da sai naci, bayan kema nasan kina buk'atarsa.?"
Shiru tayi tana tunani, ba zata iya fad'a masa haka kawai taji tana so ya fara cika cikinsa kafin ita ba, a hankali ta d'ora hannunta akan mararta tana matse fuska, karb'a yayi ya yanko loma mai kyau, a hankali ya nufi bakin Ummi da ita tare da cewa "haa."
Bud'a baki tayi ya saka mata, kallon junansu kawai suke, Salman ya had'a ido da ita ne saboda yana so ya gano wani abu a tare da ita, kallon ne yayi yawa yasa Ummi k'asa da idonta, amma duk da haka bai bar bata abincin ba shima kuma yana sawa nashi bakin, haka har suka gama.
Suna idawa ya maida kwanukan ya aje ya d'auko mata madara daga nan zaune tana kurb'a, shi kuma ya fita ya bar gidan zuciyar shi nata tunanin juna biyun da Mama ta fad'a masa wai Ummi tana da.
Gidan Ummi ko kad'an bai tsagaita ba saboda tururuwar da 'yan uwa suka dinga yi a gidan kamar ana biki, Ummi tsabar farin ciki kamar ta k'urma ihu, bayan hana 'yan uwanta da Alhaji yayi zuwa gidanta, yau gashi dangi sun cika gidanta saboda zuwa ganinta.
Sai misalin 22:30 kad'ai gidan yayi shiru ya rage Ummi kad'ai a gidan, sai lokacin ta fara jin ciwon mararta yana dad'a taso mata, haka tayi ta murk'ususu har bacci ya d'auketa daga nan kan kujera.
23:40 Salman ya shigo gidan, saida ya k'are mata kallo daga sama har k'asa, durk'usawa yayi yana kallon cikinta daya lafe a mararta, tsintar kansa yayi yana murmushi kafin ya mik'e tsaye yana fad'in "ta yaya za ace akwai ajiyar yaro anan wurin, bayan a shafe yake."
Tsaf ya d'auketa ya direta akan gado tare da ja mata zanin rufa, sannan ya tofeta da addu'a ya shafa kanta yace "saida safe".kamar tana jinshi.
Ciwon mara ne ya tayar da Ummi daga bacci, yarfa hannu kawai take gashi ba lafiya bare ta samu damar murk'usawa da kyau, haka ta dinga cizar leb'e har taji Salman na k'ok'arin shigowa d'akin, da sauri ta kwanta ta rufe ido kamar mai bacci.
Kallo d'aya Salman ya mata ya gane idonta biyu, dan daga yanda take sauke numfashinta da sauri sauri,tsaye yayi a kanta yace " tashi ko malama"
Da k'yar ta tashi ba tare data kalleshi ba, zaune yayi kusa da k'afafunta yace "miyake damunki wai"
Ko kad'an ba zata iya fad'a masa tana ciwon marar jinin al'ada bane, dan haka tace "ciwona ne kemin ciwo"
Kallonta yayi kamar mai son gano wani abu a tare da ita, ajiyar zuciya ya sauk
yace "kinsha maganinki?"
"Bansha na dare ba gaskiya"
Harara ya dalla mata yace "zan d'auko maki yanzu kisha, amma wallahi idan kika k'isha to ranki zai mugun b'aci a daren nan." fita yayi falo ya d'auko ledar magungunan tare da ruwa.