Sashe 40
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Tana fitowa ta samu La Mama zaune akan sallaya tana lazimi, sunkuyawa tayi da nufin ta zauna La Mama ta tsaida ita ta hanyar fad'in "zaman me za kiyi kuma? ki wuce kije ki deb'o abinci kici, kinsan yanzu mijinki zai zo d'aukarki."
Cikin sanyin jiki ta wuce in da La Mama ta bita sa ido tana zancen zuci "Allah yasa ba wannan dalanb'ayar kike masa a gidan ba."
Tana fitowa ta zauna gefen La Mama ta aje plate d'in dake hannunta, hannu tasa ta fara cin tuwon, kallonta La Mama tayi tace "Ummi wannan abincin ne kika deb'o ki ci?"
Kamar zatayi kuka tace " ya isheni haka La Mama."
Cike da tausasawa La Mama tace "kinga Ummi, kefa yanzu bake kad'ai bace dole kina buk'atar cin abinci ko dan lafiyar d'anki, koke baki so ki haifi yaro d'an dumul dumul?"
Cike da mamaki Ummi tace "La Mama, wai waya fad'a maku ina da ciki? nifa bana da komai har yanzu."
Haka ma La Mama cike da mamaki tace "ban gane ba, kina nufin ba kyada ciki, to kenan miye kike da da har yasa ki rashin lafiya har da amai?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "wancen lokacin ma fa kawai saboda naci abinci mai yawa ne, amma ni bana da komai."
Kallonta sosai La Mama tayi kafin tayi k'asa da muryarta tace "Ummi, kin tabbata kina bawa mijinki duk wani hakk'inshi?"
Shiru Ummi tayi na yan dak'ik'u kafin tace " La Mama ba zan iya tabbatar maku ba saboda ban san zuciyar yaya, amma ina tunanin ina k'ok'ari a kanshi yanda ya kamata."
"Kash Ummi, kinga ni kuma ba haka naso ba, Ummi naso ace kin yarda da kanki ta hanyar bawa kanki tabbacin cewa kina kula da mijinki yanda ya dace, bai zama lallai ace kin mashi yanda yake so ba d'ari bisa d'ari, amma koba komai ya dace ace ke kiji a ranki cewa kin kai duk in da wata mace maiji da kanta ta kai wurin."
"Ummi ina so ki k'ara k'ok'ari ta yanda ko wuk'a aka d'ora maki a wuya zaki iya cewa ke kinyi abinda ya dace, amma ba kice kina tunanin haka ba, gaskiya ki dad'a zage damtse kinji ko."
Cikin ladabi Ummi tace "nagode La Mama, kuma insha Allah zan k'ara k'ok'ari wajen ganin ban baki kunya ba, haka ma wajen ganin na kula da yaya yanda ya dace."
"Yawwa 'yar albarka nasan zaki iya in dai kinsa kanki, Allah ya maki albarka." tana fad'a ta mik'e ta shiga d'aki, Ummi kuma ta ci gaba da cin abincinta.
Duk tayi wani shiru da ita jikinta babu k'wari, haka su Islam suka shirya suka tafi wajen lessons yayi saura ita kad'ai zaune a falon, har saida tayi sallah isha sannan La Mama ta fito cikin kwalliya mai birgewa wanda ta dace da dattijuwa mai kamala, Ummi ba tayi mamaki dan ta san mahaifiyarta dama ko kad'an bata yarda Abbansu yaga wani abu marar kyau daga jikinta ba, kamar yanda bata gamsu mijinta ya shak'i wani abu da ba k'amshi ba daga jikinta ko gidanta.
Abba na shigowa Ummi da La Mama kusan a tare suka mike suna nufeshi da fara'ar su suna mashi sannu da zuwa, kan Ummi ya dafa yana fad'in "Mamana dama baki tafi gidanki ba?"
Kanta k'asa cike da kunya tace "Eh, Abba ban tafi ba amma yanzu zasu zo mu tafi."
Cike da jin dad'in yanda yaji Ummi ta girmama mijinta yace "ah to yayi kyau ma hakan."
Har suka zauna saman kujera Abba yana fad'in "Mamana banji dad'in abinda ki kayi ba dazu, amma kuma da kika bada hak'uri sai naji dad'i, kuma kinga Abbanki (Abban Salman) ma cewa yayi yaji dad'i dan baiga laifinki ba."
K'ara sunkuyar da kanta tayi tace "kuyi hak'uri Abba, ba zan sake ba daga yau."
"Yawwa yarinyar kirki, Allah ya maki albarka ya k'ara maki hak'urin zama da mutane a duk in da kika samu kanki."
Cike da jin dad'in addu'ar mahaifin nata tace "ameen ameen Abba nagode."
Sai lokacin ya kalli La Mama suna had'a ido ta galla masa wata harara ta kau da kanta gefe, murmushi Abba yayi dan yasa akwai rikici, cike da zolaya Abba yace "Mamana kinga ganinki yasa ban ko kula mamata ta ba ko, gashi yanzu kinsa ta fara hushi."
Dariya Ummi tayi ta kalli La Mama data rumgume hannayenta a k'irji wai ita a dole hushi take, kallon Abba tayi tace "Abba ai nasan yanzu zaku shirya in dai kune."
Tana fad'a ta tashi ta koma d'akinta, matsowa Abba yayi ya dafa kafad'ar La Mama yace "haba uwar gidana meya faru ne haka ake min wannan kumburin? kofa murmushin yau ban gani ba."
Ture hannunshi La Mama tayi ta kalleshi tace "au, ko murmushin kenan ma baku gani ba? duk wanda na maku tun shigowarku, dama ai na sani in dai kuna tare da Ummi to baku ganin kowa."
Murmushi yayi yace "haba wane ni na kasa ganinki dan tana tare dani, kawai dai shak'uwace ta d'a da uwa."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi, jin ba tayi magana yasa yace "dan Allah to kimin murmushin nan na gani mai sanyaya min zuciya ko naji k'arfin jikina."
Wani hamshak'in murmushi La Mama ta saki tare da cewa "in dai wannan ne zaisa kaji k'arfin jikinka, to ka d'auka kullum zaka kasance cikin k'uruciya."
Hannunta ya kama yana kallon fuskarta yace "ko rantsuwa nayi nasan ba zanyi kaffara ba kan cewa nafi kowa sa'ar mata a duniyar nan, a wajen wasu AUREN HA'DI masifa ne kuma bala'i, amma a wajena wallahi yafi komai dad'i, da ace zab'in zuciyata nabi ban san ya zata zama a gareni ba, watak'ila ta zama ita ce tension d'inta da wannan nake k'ara godewa Allah daya had'ani dake."
Murmushi tayi tace "nima haka ina godiya ga ubangiji daya bani ku a matsayin abokin rayuwa kuma uban 'ya'yana, dan haka yanzu ku tashi muje kuyi wanka kuzo kuci abinci."
Sun mik'e da nufin shiga d'aki Salman ya shigo da sallama, tsaye sukayi har ya k'araso suka gaisa kafin Abba yace "to inaga abar wankan nan har muci abinci koko?"
La Mama cewa tayi "ko baku fad'a ba nasan ba zaku rabu ba in har ba dare ku kaga yayi ba."
Dariya sukayi tare suka d'unguma izuwa dinning, Salman da kanshi ya zuba ma Abba abincin shima ya zuba suka fara ci suna hira ta kasuwanci La Mama na jinsu ita dai, dan dama tana zaune ne saboda ya zamar mata jiki ta zaune kusa da mijinta musamman lokacin da yake cin abinci.
A hankali La Mama ta kalli Salman da hankalinshi ya tafi kan hirar da suke tace "d'ana"
Cike da kulawa ya kalli La Mama yace "na'am"
"Dama ina so naji komai lafiya a gidan naku babu wata matsala?"
Murmushi yayi yace "lafiya k'alau La Mama babu komai wallahi, muna zaune lafiya."
Cikin rashin yarda La Mama ta kalleshi tace "nasan ba zaka fad'amin ba dama saboda baka so na d'auki mataki."
"Wallahi gaskiya na fad'a La Mama, ai yanzu Ummi ta kimtsu kamar ba ita ba idan tayi wani abu."
Mik'ewa tayi tsaye tace "bari na kirata ku wuce, dan dare nayi."
Tana shiga Ummi ta gani kwance akan gado ta lak'ume kamar mai bacci, daddab'ata tayi tana fad'in "tashi ke ku tafi mijinki ya zo."
Idonta ta bud'e lokacin da gabanta ya shiga fad'uwa saboda firgici, ganin bata tashi ba yasa La Mama d'aga murya tace "dan Allah ki tashi ki wuce mijinki na jiranki ko."
Tashi tayi zaune tana kallon La Mama data ci gaba da cewa "nifa bana san wannan sanyin jikin, komai ki dinga saka kasala a ciki ta yaya zaki birge miji a haka."
Wani irin d'aci ne Ummi take ji dan haka kawai ta rik'e hannun La Mama ta fashe da kuka, jikin La Mama ne yayi sanyi dan haka ta zauna kusanta ta dafata tana tambayarta "Ummi lafiya me yasa kike kuka?"
Bata bata amsa ba shi yasa ta sake fad'in "ki fad'a min mana Ummi, ko wani abu Salman d'in ke maki a gidan?"
Nan ma shiru "haba Ummi ya zaki d'aga min hankali, ko ba kya san zuwan gidan naki ne?"
Kai ta d'aga alamar Eh, dan haka La Mama tace "to me yasa, wani abu mijin naki yake maki ne a gidan?"
Bata ce komai ba dan haka La Mama tace "kinga kiyi hak'uri ki tashi ki koma gidanki, can d'in yafi maki nan daraja a can zaki fi samun sukuni da farin ciki fiye da nan, abu d'aya zan fad'a maki shine, ki zama jaruma kuma gwarzuwa sannan ki zama mai jajircewa akan duk wani abu daya danganci mijinki, sannan ki d'ora da hak'uri dan sai dashi zama keyin dad'i."
"Ummi ki dage sosai wajen farantawa mijinki rai, wallahi in ki kayi haka zaki ci riba a duniya sannan kici riba a lahira, Ummi ki zama mai biyayya ga mijinki sannan ki kiyaye ganinshi da jinshi da ma iskar shak'arshi, ma'ana karki bari mijinki yaga k'azanta a jikinki ko gidanki, sannan karki bari mijinki yaji gurb'atanciyar kalma ko magana marar dad'i daga bakinki, sannan ki kula sosai karki kuskura ki bari mijinki ya shak'i k'amshi a jikinki ko a cikin d'akinki ko ban d'akinki ke dama duk wani sassa na gidanki wanda ba kamshi mai dad'i ba."
Kai ta d'aga tace "nagode La Mama, Allah ya bar mana ke."
Suna fitowa zaune suka samesu kai kace abokaine, hira suke sosai har da tab'a hannu suke idan tayi dad'i, cikin ladabi Ummi tace ma Salman "sannu da zuwa yaya."
Cikin dariya yace "yawwa sannu, ya gidan?"
Cikin shagwab'a tace "ni gidan ma nake so na kwana."
Kallonta yayi yace "to ki kwanta mana idan kina so, nima saina koma gidanmu na kwana."
Take murmushi ya bayyana a fuskarta tana fad'in "da gaske yaya ka yarda na kwana a nan?"
Tsakin da La Mama tayi tare da jefarta da wata harara yasa tace "muje kawai na fasa."
Haka suka baro gidan dukansu suna ji kamar karsu rabu da iyayen nasu, saida Salman ya tsaya a hanya ya siya masu fruits da chocolat wa Ummi da kuma madararta sannan suka wuce gida.