← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan sallah isha ta kama hanya, saida ta biya ta d'auki Salman sannan suka wuce gida cikin farin ciki da nishad'i abinsu.
```Fans```
26/03/2019
11:20 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
*SHEKARA BIYU BAYA*
Ummi ce zaune a tsakiyar gado tana ta ruzgar kuka iya k'arfinta, Salman ne gefenta ya k'ura mata ido yana kallo dan ya gaji da rarrashinta, ganin kukan bana k'arewa bane yasa sake gyara zama yace "Ummi na baki hak'uri yafi cikin carbi amma kink'i hak'ura, ban san ya kike so dani ba."
K'ara fashewa tayi da wani kuka yayin da ya d'ora da cewa "dan Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, kinfi kowa sanin bana k'aunar ganin kukanki, amma shine ki keyi dan ki d'aga min hankali."
Bata kulashi ba hakan yasa ranshi ya b'ace ya daka mata tsawa "ke, wai ba dake nake magana ba kina jina kinyi banza dani, miye haka raina nine ki kayi ko me? wallahi idan baki daina kukan nan ba to ranki zai b'ace fiye da tunaninki."
Tunda ya mata tsawa ko shed'a ba tayi ba saboda tsorota da tayi, cikin shashek'ar kuka tace "dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ba laifina bane zuciyata ce ta kasa hak'uri, ban san yanda zanyi ba."
Cikin fad'a yace "to me yasa ba zaki taushi zauciyar taki ba, haka zamu zauna kullum in dai kinji anyi haihuwa sai kin tayar da hankalinki kisa kanki damuwa, haka kawai ki dinga kuka kina d'aga min hankali saboda baki haihuwa, shekara shida ce fa, kinsan wasu lokacin da suka d'auka basu haihu ba."
"To wai in tambayeki, shin haihuwar nan waye ke bayar da ita?"
Cikin kuka tace "Allah."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da janyota jikinshi yace "to kuma kinsan da haka amma shine kike bawa kanki wahala, kuka ba naki bane addu'a ce taki, mu dage da addu'a insha Allah muma wata rana za muga jininmu a duniyar nan, har yanzu ban cire rai da samun haihuwa ba kuma koda Allah bai ban ba, toni zan zauna dake ba tare da tsangwama ba ko na had'aki da wata saboda rashin haihuwa, ki daina damun kanki hakan babu kyau dan kamar kin kasa hak'uri da k'addarar Ubangiji ne, koda Allah bai bamu haihuwa ba idan mukayi duba da rayuwar mu za kiga akwai abinda Allah ya bamu wanda bai bawa kowa ba, shin ko zaki iya fad'a min miye wannan abun?"
Saida ta k'ara lafewa a k'irjinshi cikin muryar kuka tace "farin ciki da kwanciyar hankali had'e k'aunar junanmu."
"Ahan, to in dai har hakane meye zaisa mu tada hankalinmu saboda wani abu da Allah bai bamu ba, wanda ko dashi in har babu wad'ancen abubuwan na baya to akwai matsala, da wannan nake cewa ki k'ara hak'uri, kuma tunda naga abin hakane to gaskiya ba zaki bikin Nadiya ba gobe idan Allah ya kaimu."
D'aga kanta tayi ta kalleshi tace "a'a dan Allah kuyi hak'uri karku hanani, wallahi ba zan sake ba daga yau nayi alk'awari."
Tunda tace tayi alk'awari yasan zata daina, ko bata daina ba to zata kiyaye dan haka yace "shikenan to tunda kinyi alk'awari, Allah ya kaimu gobe."
A haka bacci ya d'aukesu, cikin dare Ummi ta farka jikinta lullub'e da zazzab'i da ciwon kai, gudun karta tayar da Salman daga bacci yasa ta lallab'a ta tashi drower ta bud'a ta d'auki magani tasha, tana komawa ta kwanta sai ko taji abu ya taho mata da sauri ta tashi zaune tana shirin tashi da nufin ta shiga toilet, tuni aman ya taho mata bata ankara ba, a firgice Salman ya tashi cikin bacci ya fara tambayar ta lafiya, maganin da tasha gaba d'aya ta maidoshi hakan yasa tayi tunanin maganin da tashane kawai ta maido.

Dafe kanta tayi a lokacin da aman ya tsagaita mata tana sauke numfashi, saida taga Salman a gabanta yana gyara wurin data b'ata, kallonshi tayi tare da mik'ewa tsaye tana fad'in "na tasheku ko? wallahi zazz..."bata k'arasa ba ta shiga toilet da gudu wani aman.

Toilet d'in ya shiga ya sameta tsaye tana kurkure bakinta, saida ta juyo da nufin fitowa yace "me yake damunki ne haka, ko wani abu kika ci?"
"Wallahi zazzab'i ne kawai naji ya rufe ni, shine nasha magani kuma gashi ina amayarwa."
Abu kamar wasa sai Ummi ta dinga tsula amai ba k'akk'autawa, kafin gari ya waye ta galabaita sosai Salman kuma ya jikkata saboda tausayinta, ga amai ga ciwon kai ga zazzab'i mai zafi safiya nayi Salman yace su tafi asibiti, amma Ummi tace kawai ba zata je ba haka ya dinga lallab'ata amma tak'i yarda sutafi dan allura kawai ta tsana.

Ganin ta dage akan ba zata je asibitin ba yasa ya kira Kareema (yayar Nadiya) dan tazo gida ta dubata, yana fad'a mata tace masa tana kasuwa siyan kayan cefanai na abincin biki, amma sai tace masa idan zai yiyu ya kawo Ummi gidan bikin saita duba nan, Ummi najin haka tace Eh ta yarda ya kaita dan dama zuwan take so, ba dan yaso ba haka suka shirya suka tafi gidan bikin da sunan ya kaita biki ne.

K'ofar gida ya zauna tare dasu Khamis ita kuma ta shiga ciki, Mama da La Mama da Mama Hawa ta fara karo dasu suna hira zaune, durk'ushe tayi akan tabarmar da suke suka gaisa kafin La Mama tace "Ummi sai yanzu kika taho har an fara kiran sallah azahar?"
Saida ta had'iye wani d'aci da take ji a bakinta cikin sanyin murya tace "wallahi La Mama da bama zanzo ba, bana jin dad'i yanzu ma aunty Kareema nake jira tazo ta duba ni."
Cikin tashin hankali Mama tayi karaf tace "subhanallah, Ummi ba kida lafiya amma kuma kika zo nan!"
La Mama cewa tayi "to meya sameki?naga jiya lafiyarki k'alau da kika biya can kuma ki kace nan zaki zo."
Fuskar nan a yamutse tace "wallahi La Mama zazzab'i ne ga ciwon kai ya takura min sosai, sai amai da nake fama dashi tun jiya da dare."
Abun mamaki kallon juna sukayi tare da murmusawa kafin Mama tace "to Allah ubangiji yasa rashin lafiyar alkairi ce, yanzu kije ciki ki samu wuri ki kwanta kafin ta shigo."
Da k'yar ta tashi tana shiga falo tayi karo da wasu 'yan uwan sunata hira, ciki ciki ta gaishesu da "sannunku da hira."
Wucewa taje tayi d'akin mai bikin sai muryar Sumayya taji ta bayanta tana fad'in "aikin banza aikin wofi, wai har mu za'a ma d'aukar kai, da bamu san asalin balbela ba da sai tace mana daga misra take, wai dan iyayi da ganin kinfi kowa ace sai yanzu kika zo bikin 'yar uwarki, mtssss."ta k'arashe da jan dogon tsaki.

Cikin yanayi marar dad'i Ummi ta jiyo tana kallonta tace "aunty Soumayya lafiyarki k'alau, meya faru?"
Wani tsaki ta kuma ja kafin tace "asibiti ce a kaina iyakar rashin lafiya, ko nima ci mun mutumci za kiyi ne?"
Cikin dakakkiyar murya Ummi tace "bari har narar da ki kayi shi, in yaso saina ci."
Ciki da hassala tace "ranar da nayi me?"
"Wai dan Allah miye haka, shigowata fa kenan me yake damunki ne haka?"
Cikin gadara Soumayya tace "bikin 'yar uwarki ake fa, amma ace sai yanzu ana kiran sallah azahar zaki zo, saboda ke kina tunanin yanzu kin zama wata tsiya mijinki ma haka shi yasa kike yanda ki kaga dama."
Saida Ummi ta gyara tsayuwarta cikin rashin jin dad'i tace "uhum, to kinji dai maganar nan yanzu ta fito fili, amma ba saboda na jima bane kike wannan abun, naga akwai dayawa wanda har yanzu suma basu zo ba, sannan tsawon sati d'aya nayi ina zarya gidan nan, sannan kina ina daren jiya dana kusan raba dare a gidan nan.?

Cikin b'acin rai tace "miye ke raina to?gaskiya ce na fad'a danni ban iya b'oye b'oye ba, danni bana jin tsoronki kamar yanda sauran 'yan uwa da sarakuwarki da kuma shi mijin tacen suke tsoronki."
Cikin zafin nama Ummi taci kwalar rigarta tana fad'in "Mamana kike fad'a ma haka da mijina?"
Itama cikin zafin rai ta fincike rigarta tana fad'in "dallah sakeni malama, kinji wani d'aurin duniya wai Mamana da mijina, to an fad'a d'in ko k'arya nayi basa tsoronki, kije ki tambayesu kiji shin basa damuwa da rashin haihuwarki ne, amma saboda an riga an gama dasu yasa ko idon tuhuma babu wanda ya tab'a kallonki dasu duk sunja bakinsu sunyi shiru."
D'orawa tayi da fad'in "duk kunbi kun mallake mutane ke da 'yar uwarki da kuma uwar taku sai yanda ku kaga damar yi dasu, shi yasa tun yanzu nake ma d'an uwana (Abdul) kallon k'arshe dan tunda akace za'a hadashi da tsatsonku Islam da namu tsatson nasan nan da d'an lokaci kad'an zamu daina ganinshi."
Ummi da tuni hawaye suka wanke mata fuska bata iya cewa k'ala ba sai kallonta da take, da k'yar tace "tun yaushe kika fara jin haushina, tun yaushe kika fara hassada damu, tun yaushe kika fara bak'in ciki dani?"
D'orawa tayi da "koda yake babu amfanin sanin wannan d'in, dan nasan ba zai rasa nasaba da d'aya daga cikin biyun nan ba, kodai rashin auren da Allah bai nufa ba tsakanin mijina da 'yar uwarki, ko kuma rufin asirin da yayi mana, hakane ko?" ta tambayeta.

"Haushin me zanji, Allah ya kiyaye wallahi nafi k'arfin sama dukiyarki ido, domin ni Allah ya bani abinda ke kuma ba kida shi, wato haihuwa."
Wani murmushin takaici Ummi tayi tace "ai kinji aikin jahilci, gashi kuma ki kace abinda Allah ya baki wato haihuwa, hakan na nufin kenan kinsan da shine ke bayarwa, sannan kince abinda ni kuma banda shi amma sai ba kice abinda Allah bai min ba, dan Allah da tsayawa kina sawa rayuwar wasu ido da makaranta kika koma ki sake karatun tauhidinki dan akwai gyara a ciki."
Cike da jin zafin abinda ta fad'a mata tace "an fad'a maki bamu san komai bane, ai mata irinku 'yan neman duniya ido rufe kuna sadaukar da mahaifarku ne wa bokayenku da aljanu, kinga kuwa rashin haihuwarki ba zamu dan gantashi da All...."bata k'arasa ba taji wawan mari har guda uku a kumatunta.
Chapter 44 · 0% Book details