← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 49

Sashe 23

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin La Mama bai nuna masa tasan da abinda ya faru ba, dan haka suka dinga hira har Islam ta fito daga d'aki cikin shirin riga da wando masu kyau, yana kallonta sai yaga sak ta masa kama da Ummi saidai ita tafi ummi dogon hanci, Ummi kuma ta fita jar fata da manyan ido, amma har girman jikin da yatsun k'afarsu masu kyau duka d'ayane.

Da gudu ta k'araso wajenshi ta fad'a jikinshi tare da fad'in "yaya Salman bonjour?" (ina kwana Yaya Salman)
Cike da sakin fuska yace "bonjour Islam, bien r
veill
." ( lafia lau Islam, kin tashi lafia )
Hannu ta zura ta d'auki cup d'in da yake shan kunu ta kai bakinta, tana fad'in "bien , o
est-Elle ?" ( yayi, ina take?)
Kallon idonta yayi yace " qui?" ( wa?)
Hararan wasa ta masa tace "aunty Ummi"
"Oho, elle est a la maison, elle va parfaitement bien ( tana gida, tana nan lafia k'alau)
Abba ne yace "Salman kana so ka mayar min da yarinya banasariya fa, ka dinga mata hausa mana tunda shine yaren mu."
Dariya yayi yace "Abba 'yar
cole ce fa, dole sai ana sirka mata danta dinga fahimtar abinda ake koya mata da wuri."
La Mama ce tace "ai kuma gashi nan tana iya yin frensh da kai, amma yanzu ko zan kasheta ba zata fad'amin ina kwana da yarena ba"
Gyara ma Islam zama yayi a cinyarshi yana kallon fuskar ta yace "lah bakya jin buzanci ashe?"
Turo baki tayi inda shi kuma yabi bakin da kallo, La mama ce tace "ai dama duk cikin su Ummi ce mai k'ok'arin son yare na da kuma yinshi amma fa idan tayi niyya, kuma abin mamaki idan taso zata iya yin hira mai tsawo da harshen, kuma kaga ko Inna babu abinda zata fad'a Ummi bata fahimce ta b
Shiru yayi idonshi na kallon k'asa, sai ya ji ta k'ara birgeshi, dan haka ya mik'e tare da Islam yace "to La Mama ni zan wuce, Abba sai anjima"
Islam ce ta k'ara rik'e hannunshi kamar mai shirin kuka ta kalli La mama tace "La mama zan bishi ya kaini wajen aunty Ummi ?"
Salman ta kalla tace "yaya Salman je vien avec toi, s'il te plais?"(zan tafi tare da kai),ta fad'a tare da zubo hawaye, durk'usawa yayi akan gwiwoyinshi ya share mata k'walla yace " kema saurin kuka kamar auntynki ko?"
La Mama ce tace "ina Islam aiko rabin kukan Ummi ba tayi ba, Ummi fa tana k'arama ko hararanta kayi sai hawaye, yanzu haka kuma da za tayi hamma sai ruwa sun zubo a idonta, ai ita saurin kukanta ma babu kamarta duk gidan nan, sai kuma d'an banzan rashin ji."
Murmushi kawai Salman yayi, dan kuwa saidai Ummi ba tayi niyyar kuka ba, yanzu ne hawaye zasu cika kuncinta.

Haka Salman suka lallab'i La Mama ta barshi ya tafi da Islam d'in, amma da alk'awarin zai dawo da ita gobe.

Ummi na zaune tana kallo Islam ta shigo da gudu tana kiran "aunty Ummi naaa"
Ummi na ganin Islam ta bud'e mata hannayenta ta rumgume ta suna murna, zaune tayi kusanta tace "Islam waya kawo ki?"
Kafin tayi magana Salman ya shigo, nan fa suka fara zuba ba k'akk'autawa, Islam na bawa Ummi labarin abokanan wasar data sake tunda tayi aure suka daina wasa tare.

Kular abinci dake hannunshi ya aje gaban Ummi sannan ya wuce ya d'auko plate da cuill
re da madara, tunda tafi sonta akan ruwa da jus, yana zuwa ya zuba abincin mai yawa ya aje.

Hannayen Ummi ya kama ya sauko da ita k'asa sannan yace ma Islam "to sauko muci abinci"
Haka suka keyawa suna cin abincin Islam na hira suna dariya tare da kallon juna jefi jefi, Islam ce tace "aunty wai yanzu kina jin dad'in zama anan keda yaya Salman?"
Ummi kallon Salman tayi shima ita yake kallo, murmushi tayi tace "sosai kam ina ji, amma miyasa kika tambaya?"
Kallon Salman tayi tace "to ai naga yaya Salman bai iya irin wasar da muke ba nida ke a gida"
Salman kam da yayi mamakin amsar data bawa Islam yace "wace irin wasa kuke a gidan?"
Nan fa ta fara zayyana masa suna dariya, harda cewa "kuma yaya Salman muna wasan goyo goyo, muna da d'iyan wasa muna masu kwalliya mu masu d'aki, kuma muna wasan ruwan amma La Mama fad'a take mana bata barin mu."
Salman kam Mamaki ne ya cika shi dan haka yace "to amma tun yaushe kuke wannan wasar haka?"
Cikin nuna rashin damuwa Islam tace "ai da Alhaji ya mata aure ne shikenan sai muka daina, yanzu gashi bana da abokin wasa, kuma fa yaya Salman har rawa mukeyi"
Salman kam sauraran ikon Allah kawai yake, haka har suka gama cin abinci ya shiga d'akinshi, turaren ya fiddo daga aljihunshi ya aje akan madubinshi yana k'are masa kallo, a hankali ya tambayi kanshi "wai miyasa na d'auko wannan turaren, me zanyi dashi?"
Tab'e baki yayi yace "ko ma dai miye ina son k'amshin, kuma zanci gaba da ajiyarshi anan."
Yana fitowa Sa'adat ya samu zaune suna gaisawa da Ummi cikin farin ciki, k'arasowa yayi suka gaisa da ita, Islam yaga nata faman hararan Sa'adat dan haka yace,
"Islam miye haka wannan ba yayarki bace?" turo baki tayi tace "to ni ina ruwana da ita, ai bata sona."
Cikin tsawatarwa yace "ke Islam bana san haka fa, ki kiyaye ni" Sa'adat ce tayi dariya tace "ai yaya Salman daka daina b'ata yawun bakinka, in dai nida Islam ce mun saba, dan ita dama duk wanda baya wasa da ita to mak'iyinta ne, bana sak
mata kuma idan suna shirme ita da abokiyar shirmen ina magana, shiyasa take cewa bana sonta."
Kallon Islam d'in yayi saiya ganta mak'ale a k'irjin Ummi kamar d'iyarta, ko kuma zata bata nono harda daddab'ata take tana fad'in "ke rabu da ita dama tazo ne dan ta b'ata mana rai"
Murmushi kawai Salman yayi ya fita,yana shiga mota tuk'i kawai yake kamar baya so, ga favorite music d'inshi na tashi a hankali tana ratsa sassan jikinshi yana kuma biyar wak'ar kamar shi yayi ta .

Ko kad'an Ummi bata da matsala, kawai dai tana da taurin kaine da raini ga wanda ta raina.

Wani abu yaji yana k'ara narkuwa a cikin zuciyarshi, farin ciki yake ji har k'asan ranshi.

Sa'adat ce ta kalli Ummi tace ".
05/03/2019
17:32 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
"Ummi nifa wani abu ya ban mamaki, mijinki naga ya fita amma ko kalllonshi ba kiyi ba, bare ki masa addu'ar Allah ya tsare ko sai ka dawo.?"
Turo baki tayi ba tare data kula taba, cikin b'acin rai Sa'adat tace "Ummi anya kuwa kinyi hankali? ga dukkan alama har yanzu baki gyara halinki ba, amma ba komai wallahi za kiyi nadama in har kika ci gaba a haka."
Kallonta Ummi tayi a shek'e tace "nadama, akan me fa?"
"Hmmm, lallai Ummi ba kisan ciwon kanki, shin ko kinsan irin tururuwar da 'yan uwa keyi akan mijinki?"
"Ko kinsan yanda iyayenmu suke 'ko'karin had'a 'yayansu da mijinki saboda dacewarshi da wuyar samun namiji kamarshi.?"
"Ummi ki nutsu kisan abinda ya dace dake tun kafin lokaci ya k'ure maki, namiji kamar yaya Salman ba irin mazan da ake samu bane arha, amma ke gashi kin samu duk da cewa kinsan yaya Salman yafi k'arfinki ta wani b'angaren, musamman idan ana maganar kyau."
"K'anwata ki nutsu ki kama mijinki da kyau ta hanyar kyautata masa dayi masa biyayya, zamanin nan abin tsoro ne 'yan mata suna nan bila adadi a gari, wasu ido bud'e suke neman mazan aure sannan idan sun samesu su kyautata masu kota wace irin hanya.

"Kama daga hanyar data dace dama wacce bata dace ba,Ummi kin tashi a gaban mahaifiyar mu kinfi kowa sanin yanda ya kamata mace tama mijinta, dan tun muna k'anana muke gani a wajen mahaifiyar mu, na tabbata kina da sani sosai akan yanda zaki kula da yaya Salman amma shashanci ya hanaki tsayawa ki kula dashi."
"Ummi ko kinsan cewa aunty Hawa (mamar Khamis) tana k'ok'arin cusa ma yaya Salman Rumana dan ya aure ta, haka ma aunty Rabi (kishiyar Hawa) tana so ta mak'ala masa Nuseiba tazo a matarshi ta biyu."
"Kuma fa duk suna hakane saboda tabbacin da suke dashi a kanki na sanin ba zaku tab'a zaman lafiya, saboda sanin yar tsamar dake tsakaninku dashi, to in hakane miyasa ba zaki bawa mutane kunya ba ki rik'e mijinki hannu bibbiyu ta yanda zaki bawa kowa mamaki."
"Ummi kisan fa duk abinda kika yi to zai iya shafar mutuncin Mamar mu, kuma Allah ma shaida ne akan cewar mahaifiyar mu tayi iya abinda zata iya yi akan mu, kuma kema kin sani irin maganganun da ake akan mahaifiyar mu cewa wai ta mallake mahaifinmu har yanzu ita kad'ai ce a gidan."
"Bafa komai bane yasa ake fada mata haka sai dan iya kula da miji dayi masa biyayya, dan haka 'yar uwata ki maida hankalinki kiyi abinda ya dace dake kafin ranar da zata zo kiyi nadama ko kuma kiyi kuka da hawayenki, dan ko kad'an su aunty ba suda nufin alkairi a kanki idan d'aya daga cikin 'yayan nan ta shigo gidan nan."
Tana fad'a ta gyara zamanta ta maida hankalinta ga tv tana kallo, Ummi kam duk jikinta yayi sanyi tunani take in har akace za'a rabata da yaya Salman a yanda take jinshi a yanzu, ba lallai bane ta iya daurewa.
Chapter 23 · 0% Book details