← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 49

Sashe 45

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Wa zamu gani in ba Salman ba da Islam ta kirashi a k'ofar gida saboda gani da tayi abin yak'i k'arewa, idonshi ne suka kad'a sukayi ja sai huci yake, cikin tsananin b'acin rai ya fara magana "dan ubanki waya aikeki fad'a mata haka, an fad'a maki kowa kece shi yasa har kike tunanin ta sadaukar da mahaifarta, to naji ta sadaukar saime ai buk'atarta ta kuma biya tunda ta samu abinda take so."
D'an yatsa ya nuna mata yace "wallahi daga yau sai yau kar na sake ji ko ganin ki tareta da makamanciyar wannan maganar, in dai har bake ke bayar da haihuwar nan ba ba kuma uban wani yake bayarwa ba to ku rabu da ita kinji na fad'a maki."
Juyawa yayi ya kalli Ummi data dafe kanta yace "kije ki samu wuri ki kwanta, karki sake kula duk wani da zai d'aga maki hankali."
Kallonshi tayi sai dai gani tayi ya rabu kusan gida hud'u sai gaba d'aya d'akin taga yana juya mata saboda jiri, hannunta ta mik'a mashi kamar makauniya dan ba ida yake ta mik'a hannun ba, kamo hannun yayi yace "lafiyarki k'alau kuwa?"
Ba tare da maganarta ta fito ba tace "kaini gida, ba zan iya...." luuuu tayi baya zata fad'i Salman yayi saurin tallabota, Kareema ce ta shigo dan haka Salman ya d'auketa suka kaita d'akin yaran Nadiya suka kwantar da ita anan ta fara dubata.

Gaba d'aya iyaye da kakanni fad'a sosai suka ma Soumayya, hakan yasa ta bar gidan cikin b'acin rai ta koma gidanta, su Jawahir ma haka ransu ya b'ace sosai kuma sunyi mamakin yanda Ummi bata kaima Soumayya bugu ba, dan ita bata juriyar magana har k'wara kaji hannu a maimakon bakinta.

Tunda Kareema ta tambayeta yaushe rabonta da ganin aladarta tace wata biyu, tun nan ta fara jiyo k'amshin alkairi amma saida tasa aka siyo jeux test ta gwada fitsarinta sannan ta tabbatar, wai da gudu ta fito daga d'akin tana k'walla kiran "yaya Salman, yaya Salman."
Su Jawahir dasu Mama ne a k'ofar d'akin dan haka suka tambayeta lafiya, bud'ar bakinta cewa tayi "Mama, La Mama ba zan fad'a ba sai kun ban goron albishir?"
Cikin rashin fahimta suka ce "goron me kuma, meya faru da Ummi ne?"
Cike da tsantsar farin ciki ta rumgume La Mama tana fad'in "wallahi juna biyu ne da ita har wata biyu."
_Tab', farin ciki fassara irin wanda akayi ma b'ata lokaci ne da kuma b'annan ruwan birona
ah to._
Sujuda Salman bai san adadin da yayi ba ta godiya ga ubangiji, Ummi ta zubar da hawaye na farin ciki tare da godiya ga Allah, anan aka tayar da abinda ya faru tsakaninta da Soumayya ana mai k'ara girmama al'amuran ubangiji, shi yasa babu kyau shishigi ga al'amarin Allah, gashi dai ta bud'e baki tana fad'a akan wai ta jima har take goranta mata akan rashin haihuwa, ashe ma rashin lafiyar d'aukan cikin ne ya tsayar da ita.

Daga wannan rana daga wannan lokaci Ummi ta fara rainon cikinta tare da taimakon duk wani d'an uwa makusancinta mai k'aunarta, haka kuma daga wannan lokaci sai Ummi ta dinga taka tsantsan da kowa in ba 'yan uwanta kuma aminanta ba, sosai take samun kulawa daga wajen danginta da kuma oga Salman dan yanzu ko goyonta ya daina yi haka kuma duk wani abu da yasan idan yayi zaisa tayi gudu, to ya daina duk dan kula da lafiyar abinda yake cikinta, Ummi kam yanzu in banda hutu da motsa jiki babu abinda take, dama dai mutuniyar mutane ce kama daga mak'ota 'yan uwa abokan arziki kowa na baibaye da ita, hakan ne yasa idan Salman ma ya fita baya da damuwa yasan akwai masu kula mashi da ita.

Idan kuma sukayi tafiya tare, to tana wajen mak'otansu in zai fita dan sun saba dasu an zama kamar 'yan uwa na jini, gasu da kulawa da kirki mutanen shi yasa Ummi ke jin dad'in zama dasu.

Cikinta na wata biyar lokacin kuma suna Cotonou, gashi lokacin ana sanyi sosai kullum cikin kayan sanyi take duk abin ya isheta, ranar tana zaune a gidansu Sara sunata hira abinsu tana kallonsu sunata kai da kawo, Salman ne ya kirata a waya tazo gashi ya dawo gida da gudu ta tashi ta shiga gidan.

Tun kafin ta shiga d'akin Salman ya taso da gudu ya rik'eta yana fad'in "miye haka kuma Ummi? gudu fa kike sai kin fad'i ki jamin bala'i."
Cikin shagwab'a tace "kuyi hak'uri, na daina."
Bai tankata ba sai zif d'in rigarta daya cire mata tare da aje rigar gefe, ta d'auka buk'atar tane yake amma sai taga ya cire mata kayan sanyin ya saka mata wanda suka fisu girma da nauyi, hular sanyi ya saka mata da cash coux tare da siririn glass fari sannan ya duk'a ya saka mata takalma k'afa ciki sannan ya mik'e tsaye ya kalleta daga k'asa har sama sannan yace "yah, haka yayi ba?"
Turo baki tayi tace "to wannan so kuke na mutu ko, ni gaskiya ku mayar dani gida wallahi na gaji da saka kayan nan kullum."
Dariya yayi yace "to muje dama ciren ticket d'in zamu je ki raka ni."
Cike da farin ciki ta nufeshi da k'arfi da nufin ta rumgemeshi, hannun ya d'aga mata tare da fad'in "tsaya tsaya, dan Allah ki dinga yi a hankali kinji saboda abinda ke cikinki."
Kukan shagwab'a tasa tana fad'in "ni wallahi ku mayar dani gidanmu wajen Mamana tunda yanzu kun bar sona tunda na samu ciki sai shi kuke so."
Janyota yayi ya rumgume yace "haba Mamar 'yan biyuna, ni na isa na daina sonki ai sai dai in babu numfashi na."
Kafin tayi magana yayi sama da ita suka fita daga d'akin sannan ya ajeta ya rufe d'akin suka wuce, sosai Ummi taji dad'in fitar dan yawo sukayi sosai har bakin ruwa saida ya kaita, sunyi farin ciki sosai saida yamma sannan suka hau taxi suka ciro ticket sannan suka dawo gidan hannun Ummi d'auke da ice cream da bonbon mai tsike, dan kuka ta saka mashi da yak'i ya siya mata ice cream d'in, amma gashi har yanzu bata ko lasa ba bare tasha.

Tunda ciki ya shiga wata na shida sai laulayi ya dawo mata sabo pil a leda, cikin wata shida kamar na wata takwas sosai yayi girma, haka ta dinga fama kullum da abinda zata ji sabo ga nauyin jiki kasala duk ta hargitse kamar ba ita ba, duk wani abu na jikinta bata san tab'ashi hakan yasa kanta ta daina kitso yankan farata kuma Salman ne ke mata dan bata iyawa, wanka kawai take da k'ok'arin yin saboda bata so mijinta yaji wani odeur daba k'amshi ba a jikinta, shima babu sabulu sai dai tayi tsaye ta kunna panpo ruwa na zuba in ta gaji ta kashe ta fito ta shafa turare, Salman ne ke mata da sabulu in zaiyi, kaya kam ko kad'an yanzu ko atamfa ta daina sawa bare less ko shadda kullum cikin dogayen riguna take na kantie marasa nauyi.
```CIKI SAYIN MATA```
Kwana tashi a wajen Allah babu wuya, haka har cikin Ummi ya shiga wata na *TARA* daga lokacin kuma Mama ta hana tafiya tare da suke tunda lokacin haihuwarta ya kusa, shi ma kuma tunda ta shiga watan haihuwarta ya tsaida duk wasu harkoki da zasu sa saiya bar gari ya maida hankalinshi akan jaririyarshi.

Masha Allah cikin Ummi shine rigani kwana, dan yanzu kam idan ta zauna to sai an had'a da addu'a take tashi tsaye, sosai sosai cikinta yayi girma ga tsini k'afafu kam sukace ja bani wuri saboda kumburi kai kace iska ne aka busa mata, amma duk da haka sai cikin yasa tayi kyau a fuska ga haske kamar wacce bata da jini a jiki, Mama da Salman tausayinta suke kullum haka suka duk'ufa wajen rok'on Allah ya sauketa lafiya, kuma har yau Salman Mamar 'yan biyu yake kiranta dashi.

Koda taje likita aka fad'a mata nan da sati biyu zata iya tsammanin jiran haihuwa, koda tazo gida ta tada hankalin Salman saiya kaita gida ta haihu acan, bai mata gardama ba ya kaita gida wajen La Mama, daga ranar suka tare can da zama har Salman d'in, yau ta kama asabar d'in k'arshen wata ana reunion gidan Alhaji, amma La Mama ta hanata tafiya saboda ganin yanda tayi wata iri da ita kamar dai ace mata ta haihu kuma ta haihun.

Haka akayi r
union Ummi kuma bata damu ba dan ita tasan abinda take ji, ana sallah la'asar su Jawahir Nadiya Khairat Hafsat suka zo wajen Ummi anan suke fad'a mata wani sabon tsari da taji dad'inshi sosai, wai Alhaji ya dakatar da auren Islam da Abdul dan yaji abinda Soumayya ta fad'a watak'ila kuma maganar daga manyanta taji shi yasa ta fad'a ita ma, Abdul kam yana son Islam sosai hakan yasa baiji dad'i ba yaji kuma Soumayya ta bashi haushi, abin mamakin ma shine cewa da Alhaji yayi idan Islam d'in tana da wanda take so ta fito dashi tunda babu wani matashin saurayi daya isa aure, hakan ba k'aramin k'ara b'atama wasu rai yayi ba dan a ganinsu yanzu ma shige da ficen ne akayi shi yasa haka ta faru.

Sun jima suna tattaunawa kafin suka tafi La Mama kuma ta shigo, tunda taga Ummi tasan lokaci ya kusa tunda dama kwana goma sha d'aya kenan a cikin sati biyun da aka bata, kallonta kawai take tana yamutsar fuska tare da cije leb'e amma ba tace mata komai ba, har bayan sallah isha Salman ya shigo gidan ya zauna kusanta ya mik'e k'afafu yana kallonta cike da tausayawa, ganin yanda zufa keta keto mata har ta kai fitowa take, ko uffam ta kasa cewa sai jujjuya kai take yi haka har La Mama ta kawo masu dafaffen naman kai data dafa.
Chapter 45 · 0% Book details