← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 36

Sashe 9

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi ya yi ya barta zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina. Amina ya watsa ma magungunan ya ce "Gashi nan ki bata yanzu ta sha dan ba tsayawa ta yi akayi allurar ba.

Abba na fadin haka ya juya ya koma wajan aikinsa.

Amina Kuma wajan Mansura ta koma, inda ta iske Mansura ta koma ta kwanta ta Kuma lillibe duka jikinta saboda sanyin da take ji.
Amina zama ta yi bakin gadon ta ce "Mansura, ki tashi ki sha magani dan Allah, kin ga Yaya Abba ya ce baki tsaya ya yi miki allurar ba."

Mansura cikin rawar sanyi ta ce "A'a ni dai ba zan sha ba." Babu yadda Amina ba ta yi da Mansura ba Amma taki shan maganin, daga ƙarshe ma da ta dameta kuka tasa mata.

Amina wajan mahaifiyarta ta je ta sanar da ita abin da ke faruwa.

Mahaifiyar Amina cikin takaici ta ce,
"Ka ji min shirman banza, ki ce itama shashasha ce kamarki, ba ta son Allura Kuma ba ta son magani.mu je in sameta."

Mahaifiyar Amina na zuwa da kanta ta tada Mansura, ta bare magunguna ta mika Mata tare da ruwa ta ce "Maza ki amsa ki shanyesu."
Mansura amsa ta yi tana raurau da ido.

Rufe idonta ta yi ta watsasu duka a bakinta. Amma Ina ko ciki basu kai ba ta dawo dasu.
Mansura sai da ta amaye kaf abinda ke cikinta.

Mahaifiyar Amina da takaici take kallan Mansura na amaye magungunan da ta yi. Cikin takaici ta ce "Mansura, yanzu kin fi son a barki da ciwan kenan? Haba Mansura ana ciwo ba a shan magani ne?."
Mahaifiyar Amina haka tai ta yi ma Mansura fada-fada nasiha akan kin shan maganinta.
Amina yaye bargon ta yi ta Kai bathroom dinsu ta wanke tas. Sannan ta je ta hado Mata ruwan tea. Amma Babu yadda Amina ba ta yi ba Mansura taki tashi bale ta sha tea din dole ta rabu da ita.

Mansura na nan kwance har dare gashi har yanzu zazzabin bai sauka ba, hakan ya sa jikin nata ya yi taushi sosai.

Abba kamar yadda ya sa ba dawowa aiki, haka yauma ya dawo.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Abbana, ya aikin. "Alhamdulillah mama, aiki babu dadi Kuma ba a fatar a bari."
Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce"Gaskiya ne Abbana. Dan Allah ka je ka duba jikin yarinyar nan, magungunan dakabada a bata tana sha ta amayar dasu, yanzu haka ba ka ji jikin nata ba kamar wuta, na ce ko ruwa zaka sa Mata ne, inda na ga dazu ka zo da shi."

"Mama, ku shirya ku kaita asibiti kawai, ni ba zan iya dubata Yarinyar nan ba. Mutum ace baya son Allura Kuma baya shan magani to ya take so a yi Mata. "Abba ya fadi maganar yana tashi.
Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "Abba idan Amina ce ya za mu yi haka nan za mu lallabata ta sha, dan haka wannan dinma daurewa za ka yi ka sake dubata."

Abba juyawa ya yi zai fita ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama bari in watsa ruwa sai in zo in dubata."
"A'a Abbana, dazu da na taba jikinta ya yi taushi sosai, ka dubata kafin"

Abba ba tare da ya musa ma mahaifiyarshi ba ya juya ya nifi bangaran su Mansura.

Amina na zaune ta yi ta gumi ta tasa Mansura gaba tana kallo. Abba gefan bed din ya zauna, hannu ya sa ya yaye bargon da Mansura ta rufa, wanda har yanzu jikinta zafi rau.

Abba tashi ya yi ya fita. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ganin zai fita ta ce "Abbana, ba dai har ka dubata?."
"A'a mama, sai an sa Mata ruwa Ina zuwa bari in je chamist layin nan in siyo.

Abba bai dade da fita ba ya dawo. Kwance ya samu Mansura kamar yadda ya barta. Allurai ya hadama drip din, kafin ya kamo hannun Mansura yana naiman jijiyar da zai jona mata ruwan. Mansura naiman janye hannunta take ganin allurar da Abba yake ƙoƙarin sa Mata ta Karin ruwan da zai Mata.

Abba bai Sanda ya buga Mata wata uwar tsawa ba ya ce "Wallahi kika kauce jijiyan nan da na samo, ta kubuce za ki ga abin da zan miki."

Mansura tsabar tsoro ga tsawar da Abba ya yi mata kasa tsayar da hannunta ta yi ya yi ta rawa. Abba hannu ya daga zai wanke ta da mari, Amina ta yi saurin rike hannun Abba ba tare da ta san ta yi ba. Da wani mugun kallo Abba ya bi Amina, kafin ya nuna Mata hanyar fita da hannunsa. Amina har tana tuntube garin sauri ta fita.

Kallan Mansura ya yi ya ce "Kina son in tsira miki ita a cikin ido?."
Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka."
"Yauwa tom, idan har baki so tom ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba zan mareki Wallahi, Kuma akwai Allurar ta jijiya da zan miki idan na sa miki ruwan, gara ma ki natsu.

Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ai ba da gangan nake rawa da hannun ba, shi ne yake rawa."
"Ki rufe idonki, har sai na ce ki bude ki bar gani."

Mansura rufe idonta ta yi kamar yadda Abba ya umarceta ta mika mai hannun.

Abba cikin lallabawa ya kama hannunta ya tsira mata allurar drip din."

Mansura tsabar tsoro ko zafin allurar ba ta ji ba.

Abba da sauri ya hada ta jijiyar zai tsira Mata ta bude ido jin shiru-shiru har yanzu ba a yi ba, ba ta san har ya sa mata ta Karin ruwan ba, wata zai Kuma yi mata.

Mansura da sauri ta janye hannunta, Abba na gaf tsira Mata ta jijiyar.

Abba kallanta ya yi ya ce "Me ye haka kuma ba na ce sai na ce ki bude idonki ba za ki bude ba?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom har yanzu ba ka yi min ba."
Abba nuna Mata hannunta ya yi Wanda ya jona mata Karin ruwan ya yi.

Mansura da mamaki ta zaro ido, jin ba ta ji shigar allurar ba.

Abba umartar ta ya yi da ta sake rufe idanta.

Mansura kamar dazu cikin tsoro ta sake rufe idon. Kasan cewar allurar jiji na da zafi, Kuma ita kadan-kadan ake sa ruwanta har ya gama shiga jiji, hakan ya sa ruwan na fara shiga jikin Mansura da sauri ta bude idanta tana naiman fuske hannunta.

Abba da karfi ya rike hannun Mansurar ya ce "Wallahi idan baki tsaya ba allurar ta goce sai na sake miki wata." Hakan ya sa Mansura tsawa ba ta shirya ba.
Abba na gama mata ya fita ba tare da ya Kuma tanka Mata ba, dan duk ta bashi haushi yadda ta ci mai alokaci abin da ya kamata ace tuni an angama ✍🏻

Fadila Sani Bakori ce

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK

⭐ABBANA⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

P 11-12

Zaune ya iske mahaifiyarshi da Amina da a falon. Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Ta tsaya ka yi mata alluran ko?." Eh, na sa Mata wasu a drip din, daya ce aka yi mata ta jijiya, yanzu sai wadda za a rika mata kullum sau biyu kwana uku." Ma Sha Allah, tom Allah ya sawake."Ameen." Abba ya ce ya fita zuwa bangaransa.

Amina Kuma bangaransu ta koma in da ta iske Mansura na ƙoƙarin yaye bargon da ta rufe da shi. Amina da sauri ta yaye mata bargon tana cewa "Alhamdulillah, da alama zazzabin ya sauka."

Amina zama ta yi tana jiran ruwan da aka sama Mansura ya kare ta cire mata, barci ya dauketa. Mansura ko dama tana nan ta tasa ta tsare tana jiran ruwan ya kare ta zare abinta, yana karewa ta zare tana mai ciccije baki.
Mansura kasa kwanciya ta yi saboda wata uwar yunwa da take ji. Tashi ta yi ta shiga kitchen din ta sa ruwan tea, ta hada tea ta sha kafin ta kwanta.

Washegari, Abba kasan cewar 8:00AM yake fita aiki, hakan ya sa yana tashi, bayan ya zo sun gaisa da mahaifiyarsa ya ce "Mama, allurar yarinyar nan guda biyu ce a rana, idan ta tashi zan yi mata kafin in wuce" Abba suna cikin maganar Amina ta fito da shirinta na fita aiki itama.
Amina da fara'arta ta gaida Abba, dan ta ji dadin haduwarsu dan ko ba komai zai rage mata hanya.
Bayan Abba ya amsa gaisuwar Amina ya ce "Yarinyar nan ta tashi in yi mata allurarta"
."Kai, Aiko ba ta tashi ba, bari in tadata. "A'a, ki rabu da ita kawai" Abba ya fadi maganar yana tashi.

Mahaifiyar Abba Kai ta girgiza ta ce "A'a Abbana, bari in tadata, ai tsallaken bashi da amfani, Kuma ka ga zazzabin ya bugeta sosai karya dawo mata gara a yi." Mahaifiyarsu Amina na fadin haka ta tashi ta nufi bangaransu Amina.

Tana zuwa ta ji motsin ruwa a toilet. Zama ta yi tana jiran Mansura ta fito, dan ta San in ta koma ta sanar da Abba ta shiga wanka tafiyarshi zai yi. Mahaifiyar Amina na nan zaune Mansura ta fito. Mansura cikin fara sakin jiki a gidan ta gaida mahaifiyar Amina. Mahaifiyar Amina Kuma tashi ta yi ta ce "Ki yi sauri ki shirya Abba na falo yana jiranki zai miki allurarki ta safe."
Mansura da ba ta son allura bata fuska ta yi ta ce"Mama, na fa warke."
Mahaifiyar Amina ko kanta ba ta koma ba ta ce "Bana son sakarci shi baisan kin warke bane, ki sa ko hijab ne gashi nan zuwa." Mahaifiyar Amina na kaiwa haka ta fita.

Mansura Kuma kamar za ta yi kuka ta dakko hijab din sallarta ta zura, tana zama Abba na shigowa.
Chapter 9 · 0% Book details