← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 36

Sashe 26

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab bangaran Abba ta nufa, kwance ta iske Mansura sai kuka take. Auny Zainab tsaye ta yi kan Mansura tama rasa abin da zata ce Mata. Hannun Mansurar ta kama ta ce "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka, tashi mu tafi ke ake jira." Mansura tashi ta yi ta rufe kanta da mayafinta kamar wata Amarya a haka suka karasa wajan motar da Aunty Zainab, Aunty Zainab da kanta ta bude ma Mansura motar ta shiga, kafin itama ta zagaya ta shiga. Suna shiga Abba ya ja motar suka tafi.

Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta yi shiru ba, ya ce "Ki yi shiru Mana, kanki fa zai iya ciwo."

Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura ba za ki yi shirun ba sai kanki ya yi ciwo kenan."

Mansura da kyar ta lallaba kanta ta yi shiru daga nan barci ya dauketa.

3:00PM Abba suka shiga cikin gidan Ahmad dake cikin garin Kaduna.

Yan'uwan Ahmad tarba mai kyau suka yi ma kawayan Amarya da yan'uwanta.

Bayan an ci ansha sun huta, dangin Amarya suka shirya lafiyayyar walima a gidan Amarya. Sosai Walimar ta kayatar saboda ta hada da Amarya da ango kamar yadda ta zo a musulinci, an fadi hakin Mata akan miji, an Fadi hakin miji akan Mata, sai gaf magariba aka tashi daga walimar.

Amina ba ta tashi lura Aisha bata zo ba sai dare, duk suna zaune suna hira ta lura Aisha ba ta zo ba. Amina sosai fargaba ta kamata dan tasan Aisha ta yi fushi ne.
Amina suna zaune suna hira Abba ya Kira wayarta lokacin 8:30PM, banji mai Abba ya ce ba sai ji na yi ta ce "Bari in fada Mata."

Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Saurayinki na Kira." Mansura da yake tasan Abba Amina ke nufi hakan ya sa ta ce "Wallahi ban fita tun da kikace haka."

Amina ido ta zaro ta ce "Ki rufa min asiri karyace ban fadamiki ba, dan Allah ki je." Da kyar Amina ta samu Mansura ta fita.

Mansura can harabar gidan ta hango Abba tsaye a jikin motarsa yana danna wayarsa.

Mansura da sallama ta karasa inda Abba yake.

Abba dagowa ya yi Yana kallan Mansura yana murmushi ya ce .... ✍🏻

Karku manta bana update weekend, sai mun hadu Monday in sha Allah.

Littafin ABBANA na kudi ne 400 kafin a gama free pages my number 08063830828

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 31-32

Abba dagowa ya yi yana kallan Mansura Yana murmushi ya ce "Ke ce farko, Kuma ki ce karshe, bishirnan mai girma wadda da kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe, burina in rayu da ke har numfashin ƙarshe...."
Mansura rufe ido ta yi tana murmushi ta ce "Yaya Abba da alama kana son wakar nan?." Kai Abba ya girgiza ma Mansura ya ce "Ni ba waka na yi ba, sirrin dake cikin zuciyata na fada."
Mansura da bata gane abin da Abba yake nufi ba ta ce "Yaya Abba wakace sirrin zuciyarka." Kai Abba ya girgiza ma Mansura.

Mansura shiru ta yi dan bata gane abin da yake nufi ba, hakan ya sa ta wuce maganar ta ce "Yaya Abba Amina ta ce kana kirana gani."
Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Gaki, irin in baki abin da zan baki ki wuce ko?." Mansura Kai ta daga ta ce "Dare fa ya yi Kuma na gaji, sannan barci nake ji." Shiru Abba ya yi baice komai ba ya zuba ma Mansura idanu. Ya jima Yana kallanta kamar hoto, Mansura baki ta turo ta ce "Ni dai Yaya Abba Allah zan tafi." Ki tafi ai na baki sakon." Abba ya fada yana kallan Mansura.
Mansura ido ta zaro ta ce "Kaban sakon Kuma? Yaya Abba Wana sako?."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Da farkon zuwanki wajan nan me na ce?." Shiru Mansura ta yi da alama tana son ta tuna Abin da Abba ya ce, sai zuwa can ta ce "Yaya Abba baka ce komai ba, waka ka yi fa." A wakar me na ce?."
Mansura bata fuska ta yi alamun ta gaji da tambayoyin kafin ta ce "Tom ai ni ban iya wakar ba." Shi kenan zan tura ma Amina wakar ta WhatsApp ki ce mata ta baki ki ji sakona ne zuwa gareki."
Mansura murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba sakon waka?." Eh, ki je ki ji gobe ma yi magana akai, sai da safe."

Abba yana tsaye sai da ya ga shigewar Mansura kafin ya koma part din Ahmad inda zasu kwana tare da Ahmad.

Mansura lokacin da ta shiga Amina na waya da ango, ta shiga ba jimawa suka yi sallama inda shima bangaran angon abokin hirarshi wato Abba ya shigo.

Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Aunty Mansura kin dawo." Eh, na dawo Aunty Amina ya aka yi?." Cewar Mansura.
Amina baki ta rike ta ce "Wallahi Aunty Mansura bakinki ya fara budewa fa."
Mansura hararar Amina ta yi. Kiran da akai ma Amina a waya ya sa ta fasa fadar abin da zata fada, Amina daga Kiran ta yi tana saurar abin da yayan nata ke cewa, da "Okay bari in duba."

Amina WhatsApp ta hau tana bude data sakon Abba yana shigowa. Amina kallan Mansura ta yi tana murmushi ta ce "Aunty Mansura Yaya Abba ya turo miki sako ya ce abaki."
Amina playing wakar ta yi, tare da Mansura suka saurari wakar har ta kare. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Wani abun sai Masoya, Allah sarki sai na tuna soyayata da Yaya Ahmad, ranar da zai fara furta min kalmar so wata waka ya tura min ta Auta MG boy, labari a zuciya ke ce soyayyace taki ta yi tasiri 'yan mata. Kinsan Allah lokacin sai da ya zamana babu wakar da nake so kamarta, da ita Yaya Ahmad ya bayyana min kalmar so ba da bakinsa ba."

Mansura shiru ta yi jin kalaman Amina, hakan ya sa ta dago idanunta ta suka fara tara kwalla ta ce "Amina idan na fahimci abin da kike nufi kina nufin nima Yaya Abba ya sanar min da sakon soyayyarsa ne dawakar nan?."
Shiru Amina ta yi, kafin ta ce "Mansura bahaushe ya ce wai ido ba mudu ba amma yasan kima, yanzu ki a shekarunki ba za ki iya fahintar in Namiji na sonki ba? Tom zan sanar miki da abin da yaya Abba ke ƙoƙarin fada Miki ta waka ni zan fassara miki abin da yake nufi. Mansura Yaya Abba ya kamu da soyayyarki mai tsanani Wanda Ina jin shi kanshi bai san yaushe ya fara ba, amma Yana miki so mai girma wanda ya kasa boyuwa a cikin kwayar idanunsa..."

Shashshekar kukan Mansura ya sa Amina ta dakata, ta tsaya tana kalan Mansura, Amina kallan Mansura ta yi damamaki ta ce "Me ye abin kuka aciki."
Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Nima ban Sani ba, ji na yi kawai Ina kukan."
Kai Amina ta girgiza ta ce "Ki rika addu'a kin ji Mansura, Allah zai miki maganin koma meye, yanzu idan Yaya Abba ya tambayeki kin amshi ta yin soyayyarsa wata amsa zaki bashi?."

Mansura cikin sanyi ta ce "Ni ba zan yi aure ba." Kai Amina ta girgiza ta ce "Ba wannan na tambayeki ba, shima ba maganar aure ya yi ba maganar soyayya wadda take kaiwa matakin aure ya yi, me za ki ce mai?." Amina ta fada tana kafe Mansura da idanunta.
Mansura kasa ta yi da Kai kafin ta ce "Bansan me zancemai ba Amina." Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Mansura kina son Yaya Abba?."
Mansura Kai ta dago tana kallan Amina wadda itama ita take kallo, Mansura cikin sanyi ta ce "Ban Sani ba."
Murmushi Amina ta yi ta ce "Mansura ni macece matashiya kamarki, zan iya yadda da furucinki wata soyayyar takan dade a zuciyarka kafin ka fahimci irinta, kai Karan kanka bare Kuma Wanda yake sonka, shi ya sa wata soyayyar sai ki ji cikin masoyan wani na cewa nakasa gane kan wance, alhalin ita kanta ma har yanzu ta kasa gane kan ainihin zuciyarta, idan na Fadi haka a wani wajan ana karyatani ace wai kana sanin sirrin zuciyarka, ni Kuma nasan zuciya ba ko yaushe take ba mai ita damar sanin sirrinta ba, dan haka na fahimceki na taba riskar zuciyata a matakin nan. Yanzu idan Yaya Abba ya ce ki fadi Mai amsar tambayarshi ki yi amfani da kalar salonsa ki bashi amsa, Ina da wata waka zan baki ki bashi amsa da ita kema."

Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Da wata wayar?." Amina murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Kin manta Yaya Ahmad ya sa min waya a lefe, da ita zan fara amfani zan baki wayata ki tafi da ita ta rika tayaki hira inda kin zabi zaman gida."Na gode."
Mansura ta ce.
Amina sun jima suna fira da Mansura kafin suka kwanta.

Washagari Abba ya Kira wayar Aunty Zainab ya sanar da ita su shirya da wuri, hakan ya sa Aunty Zainab da wuri suka tashi suka Kara gyagygyara dakin Amarya, suna cikin gyaran ne Abba ya da sauran abokan Ahmad da zasu maidasu gida suka zo, Abba fada ya yi ganin duk basu gama shiryawa ba, haka dai suka shirya da sauri-da sauri suka tafi. Lokacin da suka gama shiryawa za su rafi Amina rungume Mansura ta yi tana kuka taki sakinta, haka suka rungume juna suna kuka, Aunty Zainab da Hassana kawar Amarya babu yadda ba su yi ba amma sunki sakin juna. Abba jin shiru bayan sunce gasu nan fitowa number Aunty Zainab ya Kira Yana fada, Aunty Zainab cikin sanyi ta ce "Yaya Abba ya zanyi dasu gasu sun rungume juna mun yi munyi sunki sakin juna." Abba tsaki ya yi ya kashe wayar ya shigo har falon Aminar, Abba da kyar ya samu ya banbare Mansura jikin Amina, Mansura kuka take har da Majinarta tana "Wayyo Yaya Abba niba zan tafi ba ku barni."
Chapter 26 · 0% Book details