Sashe 10
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mansura Kara bata fuskarta ta yi, zabar razanar allura ko gaida Abba ba ta yi ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce"Ina ledar magungunan take Alluran na ciki?."
Mansura Kauda da fuska ta yi tana turo baki ta nuna ma Abba ledar da hannu.
Abba kallanta ya yi da mamaki, amma sai baice mata komai ba ya je ya dakko ledar magungunan. Zama ya yi ya hada allurar, kafin ya umarceta da ta miko hannunta.
Mansura goge hawayan ta yi da ya zibo Mata ta na tunawa da Abbanta da ta yi, duk ciwan da za ta yi baya bari ayi mata allura saboda ya san bata son Allura.
Abba da mamaki ya kalli Mansura yana zaro ido ganin tana kuka akan Allura. Da katawa ya yi da kamo hannunta ya ce "Lafiya? Me akai miki?."
"Ni dai bana son allurar." Mansura ta fada tana goge hawayanta.
Abba kallanta ya yi ya ce "Idan kina da kudin da za ki biya na alluran shi kenan, sai in fasa miki kin ga ban yi asarar kudina ba." Tom, ka bari Amina idan ta dawo zan amsa in baka."
Abba hannun Mansura ya jawo ya ce "Ki bari idan ta dawo kika amshi kudin kika ban na zubar da sauran."
Mansura kuka ta fasa ilahirin jikinta na rawa.
Abba tsayawa ya yi yana kallanta, dan ya ci karo da masu tsoran Allura da dama Amma nata azimin ne. Abba ganin za ta bata mai lokaci ya ce "Kin San Allah ko ki bar rawa da hannun ko Kuma in yi miki ita a cikin ido."
Mansura jin Abin da ya ce yarfe hannu ta yi tana cewa "Wayyo Allah na ba fa nike rawa da hannun ba shike rawa da kansa."
Abba hannun ya Kara kamowa, Mansura ta Kuma fusgewa tana cewa "Tom ka tsaya in shirya." Ta fadi maganar tana mai kara gyara zamanta, Wanda daga gani dai duk cikin razanar allura ne.
Abba shi dariya ma taso ta bashi, ganin sai ciku-ciku take wai tana shiryawa. Abba ganin ciku-cikun yaki karewa kallanta ya yi ya ce "Kin gama shiryawa?."
Kai Mansura ta girgiza kamar za ta yi kuka ta ce "Bari in daura dankwalina."
Abba da mamaki ya kalleta ita dake sanye da hijab. Amma sai ya tsaya ya ga ikon Allah. Mansura tashi ta yi ta je ta dakko wata doguwar riga ta d'aga hijab dinta ta zira, sannan ta kama naiman hular da za ta sa. Abba ganin abin bana kare bane ya ce "Madam ke fa nake jira."
Mansura kallan Abba ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Hulata nake nema in sa."
Abba wurga mata wata hula ya yi da ya gani a kan bed din nasu, ya ce"Ga wata ki sa." Wannan fa ta yi datti."
Abba ganin in dai ya biye ma Mansura bata da ranar shiryawa, inda ya fahimci allurar take so ta zukemawa , hakan ya sa ya tashi ya karasa inda take din ya kamo hannunta ya ce "Malama na makara zo in miki kin ga sai ki ji dadin naiman hularma a natse."
Mansura kamar za ta fada ihu ta ce "Wallahi Allah yunwa nake ji."
Abba Kai ya girgiza ya ce "Minti goma ya yi yawa ai, yanzu zan Miki, idan kuma kika aata min lokaci kin ji na ce Allah biyu zan Miki, Amma idan kika tsaya yanzu zan miki shi kenan."
Mansura jin Abin da Abba ya ce mika mai hannun ta yi tana rufe idonta dake zubar da hawaye.
Abba cikin dabara ya tsira mata allurar, Wanda tsananin tashin hankalin ya sa ko zafin allurar ba ta ji ba, sai ji ta yi ya saki hannunta yana cewa "Ki liliya wajan."
Abba na fadin haka ya fita.
Mansura Kuma dagewa ta yi tana liliya hannun.
Abba Koda ya zo falon ba kowa, Amina ta yi tafiyarta, mahaifiyar Amina Kuma tana kitchen. Abba har kitchen din ya bita ya yi Mata sallamar ya tafi aiki.
Amina kamar yadda ta saba dawowa aiki yauma haka ta dawo. Tana zuwa ta iske Amina zaune a falon tana cin Abinci. Amina ido ta zaro ta ce "Da alama dai Yaya Abba har da maganin cin Abinci ya hada miki."
Mansura turo baki ta yi tana kallan Amina ta ce "Wallhi dear nima na fara tunanin haka, tom Amma Kuma ban sha maganin ba ko daya ba, kodai allurar da ya yi min tana sa cin Abinci ne?."
Amina ido ta zaro ta ce "Wai kina nufin ba kisha maganin ba?." Ni Wallahi bana shan magani ni fa ko allura ba a taba yi min ba sai a nan, Abbana ma ko ban da lafiya idan akasa da Allura cirewa yake."
Amina da yake itama ba gwanar shan maganin ba ce hakan ya sa ta ce "Ke kinsan Allah ban ga laifinki ba, nima fa haka nake, akwai ranar da ban da lafiya Mama ba ta nan ta je Kaduna biki, daga ni sai Yaya Abba, naki shan magani ya yi min duka ya Kuma ban maganin na sha, tun daga ranar idan ya ban magani na bar yi mai musu."
Mansura ido ta zaro ta ce "Ki ce Allah ya taimakan, dazu da kila ma nima duka zai min?."
Kai Amina ta girgiza ta ce "Ai Mama na nan, ba zai bigeki ba."
Amina tashi ya yi ta ce "Bari in watsa ruwa."
Amina gaf la'asar ta shiga kitchen ta dora masu tuwan dare, sai dai ta yi mamaki ko da ta fito kitchen din ba Mansura. Amina na cikin aikin ne mahaifiyarta ta yi sallama ta shigo.
"Sannu da dawowa mama, ya jikin Aunty Zainab din?." Mahaifiyar Amina da murmushinta ta ce "Ta haihu, ta tafi da namiji." Ma Sha Allah, Wallahi mama bacin yamma ta yi da yau na je naga jariri." A'a, ki bari nasan kila gobe Abba zai je sai kuje tare." Amina ido ta zaro ta ce"A'a, gaskiya ba zan bi Yaya Abba ba, daga anje ya ce a tafi." Shi kenan, kin tafi ke kadai ai."
Amina na nan falon suna hira da mahaifiyarta, ta na yi tana duba girkinta, a haka har ta gama.
Amina ba ita ta koma bangaransu ba sai da za ta Sallah Magriba. Koda ta shiga kwance ta iske Mansura ta lillibe da bargo. Amina ganin yadda Mansura ke rawar sanyi cikin damuwa ta ce "Mansura, zazzabin ne ya dawo?."
Mansura kai ta daga ma Amina. Amina shiru ta yi, kafin ta ce "Ki tashi ki daure ki sha maganin Mana."
Mansura Kai ta kuma girgiza ma Amina ba tare da ta yi magana ba."
Amina alwalla ta yi ta ta gabatar da sallar Magriba, kafin ta nufi site din mahaifiyarta, in da ta isketa zaune kan Sallaya ta idara da Sallah itama. Amina zama ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Mama, zazzabin mansura ya dawo, ashe tun dazu tana kwance."
Mahaifiyar Amina bayan ta shafa addu'arta kallan Amina ta yi cikin fara damuwa da lamarin Mansurar ta ce "Amina, Wallahi na fara damuwa da matsalolin yarinyar nan, ace baka da lafiya ka ce Kuma ba za ka sha magani ba Kuma ba za a yi maka Allura ba, to ya take so a yi da ita. Daga ganinta ma dai irin shagwababbun yaran nan ce."
Mansura turo baki ta yi jin mahaifiyarta kamar tana naiman kushe kawartata ta ce "Mama, magani fa ba shi da dadi." Tom ai shi kenan, sai ta zauna ta warke a haka."
Amina ta san halin mahaifiyarta ko itace ta ce ba zata sha magani ba babin takanta za ta yi ba, hakan ya sa ta tashi bata Kara cewa komai ba ta fita."
Bangaran Abba yau da wuri ya dawo gidan, dan yana gidan ma aka yi sallar magariba, bayan ya dawo daka masallaci ya shiga bangaran mahaifiyarsa, ganin bata a falon hakan ya sa ya nufi bedroom dinta.
Zaune ya isketa tana duba majama'ul baharaini. Mahaifiyar Abba na ganin Abba ta rufe littafin, tana murmushi ta ce "Abbana yau 'yar wuri ce kenan?." Eh mama Ina nan ma aka yi Magriba, fatan Kuna lafiya, ya masu jegon."Suna lafiya Lau, ta fada maka kenan." Eh mama mun yi waya."
Abba kallan wayarshi ya yi dake ringing, dagawa ya yi yana kanga wayar a kunne, ban ji mai aka ce ba na ji ya ce "okay gani a gidan ma." Yana fadin haka ya kashe wayarsa.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce"Lafiya?." Amina ce ta kirani wai zazzabin yarinyar nan ya dawo."
Mahaifiyar Amina cikin takaicin rashin son maganin Mansura ta ce "Ba dole zazzabi ya dawo ba, maganin da ka bata fa in Banda Wanda na bata ta amayar dashi, daga shi ko daya ba ta kara sha ba, to taya zazzabi ba zai dawo ba."
Abba Kai ya jinjina ya ce "Mama ko daya kika ce bata sha maganin ba?." Wallahi Abba, ga zazzabin nan ma ya dawo."
Abba baice komai ba tashi ya yi ya nufi bedroom din su Amina.
Amina na nan zaune ta yi tagumi ta sa Mansura gaba tana kallo, cikin tsananin tausayi, Abba ya yi sallama ya shiga. Kallan Amina ya yi ya ce "Ina laidar magungunan?." Amina dakko ledar ta yi ta mika ma Abba.
Abba sosai ya yi mamakin ganin magungunan suna nan yadda suke. Kallan Amina ya yi ya ce "Me ya sa ba ta sha ba?."
Amina yadda Abba yake mata magana ya sa ta fahimci tuhumarta yake na rashin shan maganin Mansura, bi ma'ana dai tana da laifi.
Abba jin ta yi shiru ya Kuma cewa, "Ba da ke nake magana ba, na ce me ya sa ba ta sha ba?." Yaya Abba, ita ce bata sha ba."
Abba zama ya yi gefan gadon da Mansurar take ya ce ma Amina kawo min ruwa."
Amina da sauri ta je ta kawo ma Abba ruwan. Abba bare magungunan ya yi sannan ya umarci Mansura da ta tashi.
Mansura ta shi ta yi ta zauna tana mai kara kudindine jikinta da bargon, saboda sanyin da take ji.