← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 36

Sashe 34

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyar Abba wajan Mansurar ta matsu itama ta ce "Bari inji jikin nata?." Mahaifiyar Abba hannu sata cikin hijab din Mansura ta taba gefan wuyan Mansura, sanyi ta ji babu wata alamar zazzabi, hakan ya sa ta kalli Abba ta ce "Jikinta babu wata alamar zazzabi." Ya yanayin sanyi yake?." Abba ya tambaya Yana kallan mahaifiyarsa, mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce '"Kamar ya Kuma ya yanayin sanyi yake? Shi sanyin har wani yanayi garai, jikinta dai babu zafi sanyi ne a jikin."
Abba dafe kai ya yi ya ce "Mama ke ba likita bace ba zaki fahimci abin da nake nufi ba, akwai sanyin da idan ya yi yawa yake saukar da zazzabi."

Mahaifiyar Abba rigar da Mansura ta ciro zata sa ta dauka ta bata ta ce "Je kisa kayanki ki fito ya ji yanayin jikin naki."

Mansura dauka ta yi ta Koma bathroom din ta sa kayan kafin ta fito. Abba zuwa ya yi ya sa hannu a wuyan Mansurar. Waigowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ya ga idanta gaba daya akansa yake, Abba wayan cewa ya yi ya ce."Alhamdulillah, ta ji sauki babu zazzabin."

Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Ba nace maka ba zaka nuna min iyawa."

Abba dai baice komai ba ya juya ya tafi.

Bayan ya je aiki ya Kira Mansura a waya, Kira daya ko ta daga. Bayan sun gaisa Abba ya ce "Man's me ya sa jiya baki daga wayata ba?." Yaya Abba na yi barci da wuri ne fa."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Shi kenan, yau karki yi barci daga mama ta rufe ta tafi ki zo ki bude min." Tom." Mansura ta ce.

Bayan Abba ya dawo aiki ya zo sun gama fira da mahaifiyarsa kamar yadda ta saba bayan ya fita tasa ma kofar key.
Mahaifiyar Abba na rufe kofa Abba ya Kira wayar Mansura ta je ta bude masa, Abba ya lallaba ya shigo yana shiga ya rufe bedroom din Mansura da sauri.

Mansura kallan Abba ta yi tana dariya ta ce "Yaya Abba ka cika tsoro."
Abba ido ya zaro ya ce "Hmmm."
Abba zama ya yi yana ringumo Mansura suka karasa cikin dakin tare, Yana Zama Aisha na Kiran wayarsa, Abba bai daga ba jin tanace da Kira dama jiya ma ta Kira bai daga ba yau ma ya ga miss call dinta ya manta baibi ba, hakan ya sa Abba ya daga Kiran.

Abba na dagawa Aisha ta fashe da kuka.

Abba cikin sassauta murya yana satar kallan Mansura ya ce "Ya sallam, Momnyna meye na kuka tun da kika Kira wayata kika ji ban daga ba kinsan dai haka nan ba zanki daga kiranki ba, hankalina gaba daya yana akanki, yanzu yi hakuri ki fada min damuwarki ina jinki amaryata ya akai?."

Mansura a hankali ta kwace jikinta daga rikon da Abba ya yi Mata ta matsa can gefe tana fashewa da kuka."

Abba cikin sauri ya ce ma Aisha "Mommyna ina zuwa zan kiraki yanzu." Abba ya kashe wayar yana dawowa wajan Mansura.

Abba na taba Mansura ta bige mai hannu ta ce "Karka Kara tabani ka tafi wajan Amaryarka wadda hankalinka gabadaya yake akanta ni ka rabu dani."

Mansura ta fadi maganar tana Matsawa can karshen bed din tana fashewa da kuka, dan tasan bata ga komai bama sai Abba ya auro Aisha, inda ita ba wanda yasan da auranta.

Abba jin yadda Mansura ke kuka da karfi rufe Mata baki ya yi ya ce "Mansura dan Allah ki rufamin asiri cikin darannan Kar mama ta jiyo kukanki, kinsan zata ce zata shigo, Aisha Kuma da kike magana akanta sanin kanki ne idan Kuma baki Sani ba ki tambayi Amina bisa umarnin mama zan auri Aisha, kwanakin baya ta yi yunkurin fasa aurena saboda rashin kulawata akanta, idan haka ta Kara faruwa zata fasa Wanda haka daidai yake da tsinuwar mama akaina, ki yi hakuri kin ji."
Kai Mansura ta dagama Abb.

Can bangaran Aisha Kuma ji ta yi kamar kukan Mace kusa da Abba, hakan ya sa ta Kara Kiran wayar. Har wayar ta katse Abba bai daga ba, hakan ya sa Aisha ta tabbatar yana kusa da Mansura sukai waya.
Aisha tura ma Abba text ta yi kamar haka "Yaya Abba dole zaka ki daga wayata inda kana tare da Mansura."

Abba ganin text din Aisha rudewa ya yi yasan in dai bai Kira Aisha ba zata dauka hakan ne Kuma yasan yadda take kishi da Mansura inda akanta ma ta ce zata fasa auransa, hakan ya sa Abba ya kalli Mansura ya ce "Man's kin amince in kira mommy, wayar minti goma za mu yi dan Allah?."
Mansura kai ta dagama Abba.

Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa.✍🏻

Kamar yadda kuka Sani bana update weekend, sai Monday in sha Allah za ku jini.

Littafin ABBANA na kudi ne week din za zamu shiga zan kammala free pages idan kin shirya my number 08063830828

Fadila Sani Bakori ce.

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 41-42

Abba Kiran Aisha ya yi yana kanga wayar a kunnansa. Daga bankaran Aisha cikin raunanniyar murya wadda ke nuna almar saura kadan ta fashe da kuka ta ce "Yaya Abba ka ce min ka fasa auran Mansura amma bisa ga alama har yanzu kuna tare da ita, nifa Yaya Abba ka fahimceni zuciyata na da rauni bana jure abu ko yaya yake musamman akan abinda nake so, shi ya sa na ce maka na hakura dakai saboda bana son damuwa." Abba kallan Mansura ya yi wadda itama shi take kallo duk da bata ji abin da Aisha ke cewa.
Abba ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Mommyna tuntuni na fada maki na fasa Kuma saboda ke na fasa, ki bar dawo min da magana baya dan Allah, yanzu fada min meye damuwarki?." Mansura itace damuwata idan har kana tare da ita ba zan iya auranka ba, Kuma ko yanzu da na Kira na ji kukanta shi ne ka kashe wayarka."

Abba da ransa ya fara bacewa cikin daga murya ya ce "Idan kina ganin sai kin fi samun kwanciyar anhali in kika fasa auran nawa shi kenan ni ba zan miki dole ba." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.

Abba tashi ya yi zai nufi inda Mansura take, Mansura ta yi sauri ta kwanta tana juya ma Abba baya.
Abba hannu ya sa ya dago Mansura dake kwance ya ce "Afuwa meye Kuma na fushi bacin da amincewarki na yi waya da ita."
Mansura dai bata ce komai ba.
Abba jin ta yi shiru ya ce "Tom ya aka yi?." Ba komai." Mansura ta ce, amma a cikin ranta so take ta tambayi Abba akan Aisha amma ta kasa hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ƙarshe ma juyawa ta yi ta kwanta ta bar Abba nan zaune yana cike da fargabar maganar da ya fada ma Aisha, tsoran Kar Aisha ta aikata abinda ta ce ya sa ya tashi ya shiga bathroom din Mansura ya Kira Aisha. Kira daya ta daga, Abba tashin kukan Aisha ya ji. Shiru Abba ya yi yana sauraran kukan nata gaba daya ransa abace yake da ita, amma tsoran abinda zata aikata ya sa ya ce "Mommyna, tun yaushe nace miki na fasa auran Mansura, tun da kika fadamin ra'ayinki na sanar dake na fasa auran me ya sa Kuma yanzu zaki dawo da maganar baya, indai akan Mansura ne ki bar bata ranki kin ji?." Kai Aisha ta daga ta ce "Shi kenan na fahimta." Yauw Mommyna, Kinga dare ya yi ki kwanta ki yi barci sai da safe." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.

Abbana na gama wayar ya Kuma badroom din inda ya bar Mansura kwance ya sameta tana kuka. Abba da mamaki ya matsa wajan Mansurar da bai san Abin da take ma kuka ba.

Abbba hannu ya sa zai kamo Mansura Mansura ta daga ma Abba hannu ta ce cikin kuka "Ka fada Mata ka fasa aurena me ya sa ka aureni? Yaya Abba ka fada min me ya sa ka auran bacin ka yi ma wadda kake so alƙawarin ba zaka auran ba?."

Abba ido ya fara zarewa yana mamakin ya akai Mansura ta ji wayarsa, sai dai yana daga kai ya ga akwai window a wajan Kuma window bude yake zata iya jin duk abin da yake cewa.

Abba rasa abin da zaicema Mansura ya yi. Mansura Kuma cikin kuka ta ce "Sai yanzu na gane abinda kake nufi da ka ce mu yi auran sirri, dan Kar Aisha ta san ka aurene saboda ka yi mata alƙawarin ba zaka auran ba."

Abba magana zai yi Mansura ta nuna mai hanyar waje ta ce "Yaya Abba ka fita kawai nagama fahimtar abinda kake nufi dani."

Abba da mamaki ya kalli Mansura yadda take nunamai hanya ya fira alamun ba zama ta saurareshi ba, bacin aganinsa sanin kanta ne ita yake so ba Aisha ba, hakan ya sa Abba cikin bacin rai ya ce "Haba Mansura ki saurareni Mana nifa ba Aisha bace zabina ke ce zabina."

Mansura kunne ta toshe, ta ce "Yaya Abba ka fita dan Allah."
Mansura ta fadi maganar tana kuka.
Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ba zan fita ba sai kin saurareni."

Mansura da ranta ya gama baci, cikin fushi ta ce "Ki fita Wallahi ko in Kira Mama." Abba da zama ya yi bakin bed din Yana ma Mansura kallan mamaki.
Mansura ganin haka daga murya ta yi tana Kiran mahaifiyar Abba tana cewa "Mama! Mama!! Maa.."

Abba cikin tsoro ya tashi ya rufe ma Mansura baki yana zare ido cike da tsoro.

Mahaifiyar Abba da barci bai dade daukarta ba ta jiyo Kiran Mansura, mahaifiyar Abba bakin kofar Mansura ta zo tana Kiran sunan Mansura ta ce "Mansura, lafiya ya aka yi?." Mansura to take ta yi magana amma Abba ya rufe mata baki yadda babu yadda za a yi ta iya magana.

Mahaifiyar Abba Kiran sunan Mansura ta Kuma yi, jin shiru bata amsa ba ya sa ta dauka ko mafarki ta yi ta Koma ta kwanta.
Chapter 34 · 0% Book details