← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 36

Sashe 19

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Can bangaran Mansura Kuma suna tafiya ta tusa kanta atsakankanin cinyoyinta. Abba na lura da ita, hakan ya sa ya tashi ya koma inda take, Abba zama ya yi yana dago kan Mansura da ta tusa tsakankanin cinyoyinta. Kallan-kallo suka tsaya yima juna kafin Abba ya sa hannu ya goge ma Mansura hawayan da ke fita a idanunta, Abba cikin nuna damuwarsa ya ce "Ba za ki bar kukanba kenan, ya mu ka yi da ke?."
Mansura fashewa da kuka ta yi tana cewa "Yaya Abba ba fa kuka nake yi ba, nima bansan hawayan na zubarmin ba. Abba bubbuga bayan Mansura yake yi kamar ana lallashin karamin yaro ya ce "Shi kenan na ji ba yadda ba kuka kike ba, ya Isa yanzu ki bar kukan."
Mansura kasa tsaida kukanta ta yi, bisa ga alama ita kadai tasan zafi da kuncin da ke damunta. Abba ganin ya ba Mansura baki ta ki yin shiru hakan ya sa ya ya bude motar zai koma front seat ya rabu da ita.
Mansura rike hannun Abba ta yi ta ce "Na yi shiru Yaya Abba." Ta fada tana jan ajiyar zuciya tana goge hawayanta. Abba gaba daya yama rasa tunanin da zai yi akan Mansura, sun dade shiru kafin Abba ya ce "Daga nan har a yi bikin Aisha idan har kika Kuma yadda na ganki kina kuka tom zan bata da ke bazan sake shiga lamarinki ba inda bakya jin magana."
Mansura tana ƙoƙarin tsaida hawayanta ta ce "Ba zan Kuma ba Yaya Abba." Yauwa yar Albarka." Cewar Abba yana Kuma share ma Mansura hawayanta. Ganin ta bar kukan ya ce "Kina so in Samar miki teaching a school din da Amina ke yi? Kin ga bayan bikin Amina kin huta zama gida ke kadai inda Mama kullum tana Islamiya."
Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana so, ni ba zan iya hayaniyar yara ba." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura kafin ya ce "Tom in mai da ke school sai ki ci gaba da karatunki?." Nan ma dai Mansura Kai ta girgiza ma Abba alamun bata so. Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Tom fada min me kike so? Ina son in Samar miki wani abin ne wanda zai hanaki zaman gida baki daya." Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son komai, ni gara in ta zaman gidan ma." Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "A'a, idan baki son komai sai mu yi Miki aure shi kenan."
Mansura rufe idanunta ta yi kafin ta dago tana kallan Abba ta ce "Tom wa za ku aura min ni da bani da saurayi?." Ni da nake da abokai da yawa, baki ga Mansura bama cikin abokaina zata auri wani, ciki zan samo in aura miki kema."
Mansura bata fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai Yaya Abba bana son kowa, ni ba zan yi aure ba." Ai ko sai kin yi aure, akwai wani abokina ma ina jin zanma Mama magana bayan bikin Amina kema a yi naki." Take Mansura ta fashe ma Abba da kuka dan ta yi tunanin da gaske yake. Abba ido ya zaro yana cewa "Ke ni wasa nake miki aike ba za ki yi aure ba ai na sani duk wanda ya zo ya ce ma yana sonki sai na mishi kus'a." Abba ya fada Yana nushin Mansura a hankali a fuska yana gwada mata yadda zai yi ma duk wanda ya ce yana sonta.
Abin mamaki sai ga Mansura tana dariya... Daidai nan su Aisha suka dawo, da mai baro da ya dakko masu kayan siyayyar da suka yi. Hassana nocking ta yi ma Abba ganin bai kula dasu ba hankalinsa na kan Mansura dake dariyar kus'a din da zai ma wa inda suka ce suna sonta.

Abba fita ya yi yana kallan Hassana ya ce "Sanninku da dawowa." Hassana kallan Aisha ta yi irin kallan gingani ko ai abin da nake ce miki kenan.
Aisha dai ba ta ce komai ba, amma bisa alama ranta ya bace yana yin fuskarta ya sauya.

Abba bude boot din motarsa ya yi mai baron ya loda siyayyar da suka yi a ciki.

Aisha jikinta gaba daya yayi sanyi a haka ta zagaya ta koma wajanta ta zauna.

Abba har ya isa gida babu wanda ya yi magana a motar. Abba bayan ya yi parking umartarsu ya yi da su shiga da duk abin da suka siyo cikin gida. Gaba daya dauka suka yi inda duk suka dauki manya ledoji ban da Mansura da ta dauki 'yar Karama, har ta juya za ta bi su Aisha Abba ya kirata ya ce "Wannan Yar ledar zaki dauka? Zo ga wata in dora miki."
Abba amsar ledar da Mansura ta dauka ya yi ya dora mata wata babbar leda akai. Yana dora mata Mansura ta durkushe har kasa tana turo baki ta ce "Yaya Abba ya fa yi min nauyi Wallahi ban iya tashi."
Abba Kai ya girgiza ya ce "Wa'inna yan kayan ne za su yi miki nauyi, maza ki tashi Wallahi bana son ragonta." Mansura Kuma turo baki ta yi tana durkushe da ledar akanta ta ce "Allah Yaya Abba sun min nauyi." Allah karya ne ba su yi miki nauyi ba." Abba ya fada yana Mika Mata hannunsa ya ce "Kama ki Mike." Mansura kama hannun Abba ta yi ta miki daga durkusan da take.

Bangaransu Aisha ko, suna tafiya Hassana ta ce "Kinga ni ai abinda nake fadamiki, dazu daga gani dama ni nasan lafiyarta Lau, amma ke kika naimi ki kareta wai bata son hayaniya. yanzu gata can tsaye ai suna fira a gabanki ko kunyarki ma bata ji ba."
Fadin gata can din da Hassana ta yi ya sa Aisha juyawa, Hassana ma ganin waigawar ta yi daidai nan Mansura ta rike hannun Abba ta tashi daga durkusan da take, ta yi taga-taga zata fadi Abba ya riketa ya na mata dariya.

Da sauri Aisha ta juyo, take taji wani irin bakin ciki da tsanar Mansura aranta.

Hassana Kuma ta ci gaba da cewa "Wallahi tun kafin lokaci ya kure miki ki sanadar da Amina abin da ke faruwa na kwacan da yarinyar nan ke shirin miki ta take Mata burki.

Aisha dai bata ce komai ba hassalima Kara saurinta ta yi.

Suna shiga da gudu Aisha ta yi sight din Amina jin kukan dake ƙoƙarin kufce Mata. Mahaifiyarsu Amina dake falon da mamaki ta bi Aisha da kallo tana kallan Hassana ta ce "Hassana lafiya me ya samu Aisha haka ta shigo tana kuka." Mahaifiyar Amina ta yi tambayar cikin damuwa."

Hassana cikin tsantsar nuna damuwa ga lamarin ta ce "Gaskiya mama akwai damuwa." Hassana ta fada tana shigewa bedroom din Amina ta bar Mahaifiyar Amina sake da baki.

Can Kuma Aisha na shiga ta fada bed din da Amina take zaune tana chatting ta fashe da kuka. Amina cikin tashin hankali ta wurgar da wayar hannunta tana kamo Aisha ta ce "Mommyna lafiya ya aka yi ke da wa?." Aisha shiru ba amsa sai kuka da take yi.
Amina kallan Hassana ta yi dake tsaye tana kallan Aisha. Amina cikin damuwa ta maida kallanta ga Hassana ta ce "Hassana wai lafiya? Ya aka yi ne ?." Hmmmm." Hassana ta ce ta zauna.
Ana haka ne mahaifiyar Amina ma tashi dakin da saurinta jin sautin kukan Aisha.

Mahaifiyar Amina ganin ba ta ga Mansura ba ya sa ta ce "Ina Mansurar, ko wani abun ne ya s..." Mahaifiyar Amina shiru ta yi jin sallamar Mansura. Mansura da mamaki ta bi Aisha dake kuka da kallo. Mahaifiyar Amina Kuma cikin damuwa ta maida kallanta ga Mansura da ta shigo yanzu ta ce "Mansura wai lafiya ya aka yi ne? Me ya samu Aisha take kuka ne?." Mansura cikin mamaki ta ce "Wallahi mama ban Sani ba, nima tambayar da zan yi kenan."
Mahaifiyar Amina da mamaki ta ce "Batare kuke bane?." Tare muke." Cewar Mansura.

Hassana Kuma dagowa ta yi tana hararar Mansura ta ce "Eh gaskiya fa dole kice baki Sani ba bacin kin manta snatching din saurayi."

Mahaifiyar Amina damamaki ta kalli Hassana ta ce "Kamar ya bangane ba Hassana?."
Mama Mansura soyayya suke da Yaya Abba."

Mahaifiyar Abba da tsananin mamaki ta ke "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abban na gidan nan mana..✍🏻

Fadila Sani Bakori ce

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 23-24

Mahaifiyar Abba cikin tsananin mamaki ta ce "Wana Yaya Abban?." Mama yaya Abba na gidan nan mana." Cewar Hassana.

Mansura ko tsabar al'ajabi shiru ta yi tarasa bakin magana, tana mamakin shairin da suka kulla Mata.
Chapter 19 · 0% Book details