← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansura tsayawa ta yi gefan Abba, kamar yadda Amina take can gefan Ahmad. Abba take ma Mansura kafa ya yi da dan karfi, Mansura Kai ta dago ta kalli Abba tana turo baki. Daidai nan maihoton ya dauka. Abba Kuma kanne ma Mansura ido ya yi. Mansura ganin Abba da gangan ya takata hakan ya sa ta fara buga kafa tana Kara turo baki Wanda daga mai daukar hoton da Amina da angon da Aisha duk suna kule dasu ba kamar Aisha ba.

Abba cikin kunnan Mansura ya rada Mata ya ce "Maganin wanda bai iya gaisuwa ba kenan."

Ahmad tabo Abba ya yi, Abba waigowa ya yi yana kallan Ahmad, Ahmad Kuma a hankali Aminace kadai ta ji abinda ya ce ya ce "Amaryarka na kallanka dan haka ka kula malam."

Abba harar Ahmad ya yi baitanka masa ba.

Haka aka ci gaba da hotunan Wanda Abba shi dai gaba daya hankalinsa na kan Mansura, ya kasa iya rike kansa akan Mansurar, ta yi mai kyau sosai gashi ta saki ranta.

Abba ya yi masu hotuna masu yawa shi da Mansura. Mutane da dama sun dauka budurwarsa ce, wa inda suka ji labarin saranarsa Kuma sun dauka ita zai aura.

Aisha daga ka kalleta Kamar ta fasa kuka Amma ta daure tana yake ne kawai. Amina lura da hakan da ta yi ta sanar da Ahmad ta ce "Yaya Ahmad dan Allah ka yi ma Yaya Abba magana mana Allah haka cin fuska ne fa, ya za ai ya yi ta hotuna da Mansura a gaban Aisha haka ai ba zata ji dadi ba."

Abba zuwa ya yi ya jawo Abba gefa ya ce "Abba meye haka ne za fa ka hada yaran nan fada ne abin da kake yi, Taya za ka zo kana hotuna da wata macan a gaban matar da zaka aura, gaskiya haka bai kamata ba cin fuska ne Wallahi."

Abba bata fuska ya yi ya ce "Duk Mai gulma ya je ya yi ni kallan da nake ma Amina shi nake ma Mansura. Hoto Kuma kafin in yi da Mansura ai da ita na fara yi." Ahmad duk yadda ya so Abba ya fahince shi yaki hakan ya sa dole ya rabu da shi.

Bayan an gama hotuna Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Ku shirya nan da 1hour zamu zo mu dauke ku." Kai Mansura ta jinjina ma Abba, Abba har ya juya zai tafi ya kalli Mansura ya ce "Ki rike wayar Amina a hannunki zan kiraki." Mansura Kai ta daga ma Abba ya ja motarsa suka tafi.

Hassana ce ta sanar da sauran kawayansu akan kowa ya sa lass din ankosa 5 za a zo daukarsu zuwa party.

Bangaran Aisha waje ta samu ta zauna ta yi tagumi. Khadija da dawowarsu kenan kallan Aisha ta yi dake zaune ita kadai ta yi tagumi. Khadija karasawa inda Aisha take ta yi ta cire mata hannun da ta yi tagumi dashi ta ce "Aisha, lafiya kika zo nan kika yi tagumi kekadai?." Aisha dago manyan idanunta ta yi tana kallan Khadija kafin ta ce "Baba komai." Shi kenan." Khadija tace suka tafi.

Khadija bayan ta shiga falon Aunty Zainab, Hassana ta naima dan ta fita kusa da Aisha tana tunanin in itace kila za ta iya fada mata damuwarta.
Kasancewar wajan da mutane ya sa Khadija hannun Hassana ta kamo har zuwa inda Aisha take. Zama suka yi gefan Aisha, kafin Khadija ta ce "Hassana kawarki na gani cikin damuwa na tambayeta ta ce min ba komai shine na kiraki kila ke ta fada miki."
Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, Aisha akan Ina komai ya faru gaskiya harda laifinki, lokacin da kika je kina ma Yaya Abba magana baikwalasheki ba, hasali ma har hoto naga kunyi tare amma yarinyar nan na zuwa Ina lura da ke kika janye jikinki kika koma gefa, ma'ana kin bar mata shi kenan. Aisha idan har kina son Yaya Abba da gaske kamata ya yi ki tsaya ki yi yaki ki kauci soyayyarki."
Hassana ta dade tana ba Aisha shawarwari kafin suka tashi suka shiga ciki domin canza kayansu zuwa lass Wanda za suje wajan partyn dashi.

5:00PM motocinsu Abba suka cika kofar gidan Aunty Zainab zuwa daukar kawayan Amarya zuwa wajan party.

Kawayan Amarya kowace ta cakare fatar kowacce ace babu kamarta. Ga lass din peach color da dige-digen fari-fari, sai kalar ta haska kowa, hakan ya sa duk sai suka yi kyau.

Mansura da Aisha suka rike Amina har zuwa wajan motar da Ahmad yake ciki. Wanda babban abokin anko wato Abba shi zai ja motar.

Abba kallan Aisha da Mansura ya yi ya ce "Babbar kawar Amarya ta shiga gaba mu tafi."

Abba Kiran wani abokinsa ya yi ya ce "Habibu, ga Mommyna nafi yadda da tukinka ka taho min da ita." Haka din da Abba ya yi sai ya rage ma Aisha zafin da take ji, inda ko mahaifiyar Amarya tana jin tana Kiran Mansura da babbar kawar Amarya har dilka ma tare aka yi masu.

A cikin motar Amarya ko Abba ya kure volume din motar da wakar Hanta da jini. Tafiya suke Abba na karkada kafa da Kai. Mansura dai mamaki ya isheta ganin yadda Abba kebin wakar.

Green g hotel anan Abba ya kama wajan gudar da partyn bikin kanwarsa da babban abokinsa.

Mutane duk sun gama halartar a hall din, har iyayan Amarya duk an kawosu ya zamana Amarya da anko kawai ake jira.

Bayan Amarya da anko sun iso MC ya fara announcing na isowar Amarya da anko.

Kawayan Amarya da abokan ango suka je suka taro a Amarya da anko inda aka sasu tsakiya. Wasu daga cikin abokan manni kawai suke ma Amarya da angon a haka har suka karasa wajan zaman da aka tanada domin amarya da ango.

MC ya dade yana bayanansa kafin aka tada daya daga cikin akoban anko ya bude wajan da addu'a.

Bayan haka MC ya Kira Mansura babbar kawar Amarya yana son ganinta. Mansura kin tashi ta yi sai da wasu daga cikin kawayan Amarya suka kama hannunta suka rakata har wajan MC din kafin suka juyo. MC ya dade yana wasa Mansura, kafin ya Kira babban abokin Ango Abba. MC inda Mansura take tsaye ya nuna ma Abba ya tsaya kusa da Mansura, kafin ya ce "Jama'a dan Allah ku kallesu, ya kuka gansu dan Allah, a tafa ma babbar kawar amarya da babban abokin angonnan ." Rap-rap, haka hall din ya dauka. MC kallan DJ ya yi ya ce "DJ sa masu wakar da tadace tasu su bude Mana filinnan." Eye-eye eh-eh, a'a. Nasan so dashakuwa, jininmu ne yake ta haduwa, matso ki zo nasamu natsuwa, dannn kinhanaminni damuwa.oo'ooo oo'oo, laaaaaa oo-oo ."
Take hall din ya dau ihu ganin yadda Abba ya fara bin wakar.
"Wadda na damka amanata akanta na jaddada kalmanata, na fada zan nanata azuci nasata na riritata .... kamar wasa"
wata kallar rawa Abba ya fara irinta Mayan guy , breaking dance, daidai lokacin da aka fara " kullum inata fada miki sai ke." Abba ya fada yana nuna Mansura, ya ci gaba da cewa yana nunata "Kaunarkice ke yimin tsinke, tattarani ta sani a shinke, sai da ta sani a tsinke, Bata barni da yunwa ba, ba ta ki bani ruwan sha ba, baza nace Mata uffan ba domin agaran haka ribace."
Wani taku Abba ya yi yana dansewa har ya karaso wajan Mansura yana cewa "Mitazamanamu ba wa'adi, komai mukayo so ne sanadi, sa'in da ba kiciran wa'adi, rabo dake sai dai in na ji naga kaza ta yi kaho, mai kishina Ina sonki me zan baki na aureki, sonki yana ta ginan layi, mizamanmu atare acan ciki, acikin ciki can ciki."
Hall din gaba daya ya dau ihu anata taba masu Abba dan sosai abin ya kayatar ya tada ma wasu tsimin soyayyarsu.
Mansura dai tsaye take tana kallan Abba tana murmushi, wani wajan Kuma ta rufe ido.

Abokan Abba ko ku zo kuga yadda suke yi ma Abba liki.

Mansura ma wasu daga cikin iyayan Amarya sunyi Mata liki Amma kawaye ko daya babu wadda ta yi Mata liki.

Mc yabama abokan ango ya yi sosai ya ce "Ya haka ne? abokanka Abba sun yi Kara munsan kana da Abokai Amma kawar Amarya har yanzu bamu shaida tana da kawaye ba, dan duk su mamane suka yi Mata liki, Dj sa masu wata wakar da alama waccan Bata burge kawayan Amarya ba ne."

Dj waka nake so wadda ba zamu bar nan wajan ba sai abokin angonnan ya yi wuf da zuciyar kyakkyawar kawar amaryar nan."

Hall din gaba daya ihu ya dauka jin wakar da dj ya sa. Abba take ya fara bin wakar tare da rawa irin wadda ta dace da wakar. " Dubaaa akanki ana kallona majanuni." Abba ya nuna Mansura ya ci gaba da bin wakar" Babban burina ki kasance daf dani, in zaaki irga masoya naki kisanyo dani, duba akanki ana kallona majanuni, ni Kuma nacee indai kainaki ne ban fadi ba, Sako ya bayyanane tun daga zuciya, sannan kaunarki tana kaman zuciya, kin kaaamani kurwata tun jiya, har yaake matsayin bana samun lafiya." Abba gab Mansura ya matsa ya kureta da ido kamar irin wajan bakowa sai su kadai haka yake ji ya manta da kowa, kallan Mansura yake Yana cewa "Kin shiga Raina kin zauna dan kinsamu guri inata kiranki na amsa kuma nazo da wuri, ki ce farko Kuma ki ce karshe bishiyar nan maigirma wadda kikai minni dashe, bana ji bana gani bana son mai kushe burina in rayu dake har numfashin ƙarshe."
Abba nuna ma Mansura ya yi Yana cewa " kinkirkita dukka tunanina."
Abba Hannu ya hada alamun roka lokacin da aka zo baitin "Taimakaki bani gurin kwana, sanki ya hanamini barcina, Ina ganki har a mafarkina, sonkiii yanaiii min dadi ban son mu rabu, kijaddada jaarumta taki karmu rabu, bani da kowa sai ke inatafe ba wani..."
Abba dakatawa ya yi da bin wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gaba daya sai ya ji rauni shima, hakan ya sa ya kama hannun Mansura yana rungumota suka bar cikin hall din da sauri...✍🏻
Chapter 24 · 0% Book details