Sashe 22
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina kalllan Aisha ta yi ta ce "Mommyna ya dai na ganki so silent." Aisha fashe ma Amina da kuka ta yi cikin kukan Aisha ke fada ma Amina ita ta hakura da Abba inda ta ga gaba daya hankalinsa ba akanta yake ba." Amina gudin Kar hankalin mutane ya dawo kansu ya sa ta jawo hannun Aisha da sauri suka nufi bangaran Abba, ganin sauran kawayansu a falon Abba ya sa Amina ta bude bedroom din Abba suka suka shiga. Amina zaunar da Aisha ta yi gefan katifar Abba, sannan ta zauna kusa da ita. Amina cikin damuwa da lamarin ta ce "Mommyna duk abin da zan fada maki ba lalle ki yadda ba, amma a iya sanina fara hidimar bikin nan nawa ne Yaya Abba suke magana da Mansura."
Aisha Kai ta girgiza ma Amina ta ce "Amina Allah na hakura da Yaya Abba saboda dama nike sonshi shi baya Sona, sannan maganar ace wai yaya Abba baya soyayya da yarinyar nan ba haka bane, kila dai ke ce baki Sani ba."
Amina shiru ta yi dan ta rasa yadda zata fahimtar da Aisha ta gane, Amina ta ce "Aisha Koda ma ace Yaya Abba na son Mansura kamar yadda kika ce kinsan dai sai ya aureki Koda zai aureta." Aisha Kai ta girgiza ta ce "Amina ba zan iya zama da wanda hankalinsa baya kaina ba Yana kan watane, da ace daga ni sai shi ne ina da tabbacin babu wata a ransa da zan iya hakura in auresa, amma yanzu Kam na hakura ina mai tabbatar miki yanzu haka daga na je gida zan sanar da Malama."
Amina hankalinta tashe ta kamo hannuwan Aisha ta ce "Mommyna Wallahi Allah kin ji na rantse miki Yaya Abba baya sa soyayya da Mansura idan baki yadda ba Bari in Kira Mansurar ki ji daga bakinta." Amina na fadin haka ba ta saurari ta fita. Babu jimawa Amina ta dawo tare da Mansura. Bayan Mansura ta zauna Amina cikin sanyi ta ce "Mansura Aisha wai ta fasa auran Yaya Abba saboda ita a zarginta Kuna soyayya da Yaya Abba ne, na yi ƙoƙarin in fahimtar da ita taki ganewa shi ne na kiraki ki fada mata da kanki ko zata fi yadda."
Mansura tabe baki ta yi kafin ta ce "Ni bansan meye ma wata soyayya da take magana akai ba, Yaya Abba ma ni sanadiyar bikin nan muka fara magana dashi, idan kin ce za ki fasa auranki da Yaya Abba ni babu ruwa." Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Kin ji ko mommy, Idan da tana soyayya da Yaya Abba ai da nafi kowa Sani, abinda kike tunanin Wallahi ba haka bane."
Aisha sai yanzu ta ji ta gamsu. Cikin sanyin muryarta ta ce "Shi kenan na fahimta."
Amina ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wai lallai sannu hajiyar kishi, ki gode ma Allah ma Yaya Abba bamai kula-kulan yan Mata bane, ki ce da munsha kallo."
Aisha murmushi ta yi Bata ce komai ba.
Da daddare kawayan Amina duk sun watse ya rage daga Amina sai Mansura, Wayar Amina ringing ta yi, bayan ta dauka, ta ce "Okay gani nan zuwa."
Aisha kallan Mansura ta yi ta ce "Ina zuwa Yaya Abba ke kirana, Allah dai ya sa ni ba aiki zai Sani ba."
Amina zaune ta samu Abba cikin motarsa, Abba umartar Amina ya yi da ta shiga, Amina bayan ta zauna ta kallli Abba ta ce "Yaya Abba ka kirani Kuma ka yi shiru. Murmushi Abba ya yi ma Amina ya ce "Ba wani abu bane Amina tambayarki zanyi, tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bata taba baki labarin wani na gidansu ba ko labarin mamanta ko babanta ba?."
Amina shiru ta yi tana kallan Abba, azuciyarta ta ce "Me Yaya Abba zai yi da bincikar labarin Mansura, ko dai da gaske ne suna soyayyar kamar yadda Aisha ta ce ." Abba ganin Amina ta fada duniyar tunani muntsilarta ya yi ya ce "Idan kin gama tunanin ina jinki."
Amina murmushi ta yi tana kallan Abba ta ce "Yaya Abba kasan Mansura bata magana ko labari ka kawo Mata daga eh, sai uhm, idan abun dariya ne ta yi murmushi shi kenan, kwanannan ne ma idan ina magana har take samun baki, Amma bata wata doguwar magana bare har ka ji sirrinta.
Abba shiru ya yi kafin ya ce "Amma ke me kika fahimta game da yarinyar?."
Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Wallahi Yaya Abba na kasa fahimtar komai akanta, amma dai koma meye iyayanta da alama attajirai ne." Kai Abba ya jinjina ya ce "Nima naga alamar haka. Amina gobe za a daura miki aure ina so yau din nan, ki zungureta da maganar ahalinta da kin ji me zata ce, Ina so ki min recording hirar taku, abin da nake so ki ce Mata, Mansura niko inata so in tambayeki wai wacece Fatima da kike yawan Kira a mafarkinki." Daga nan Kar ki ce mata komai."
Amina Kai ta jinjina ma Abba alamun za ta yi, kafin Amina ta ce tana wasa a hannunta alamun maganar kamar ta yi mata nauyin fada ta ce "Yaya Abba kana son Mansura ne?."
Abba hararar Amina ya yi ya ce "Dan na yi miki wannan maganar akanta shi kenan ina sonta, Kinga ke aure zaki yi mama Kuma kullum tana Islamiya, shine nake so mu ji wacece ita in ta kama mu maidata gidan iyayanta sai mu maidata kamar zaifi."
Amina turo baki ta yi ta ce "Allah sarki Yaya Abba tashin hankalin Mansura kenan akan auran nan nawa zaku ce ba za ku iya zama da ita ba, gashi nan tun kafin in yi auran Kun bayyana min hakan, inda gashi kana maganar maidata gidansu."
Abba da mamaki ya kalli Amina dake goge hawaye ya ce "A'a Amina ya zamu koreta bayan kin riga kin maidata Yar gida, kawai dai Yana da kyau mu San wacece ita din." Shi kenan Yaya Abba zan tambayeta yanzu daga na shiga ciki, duk yadda muka yi da ita zan tura maka ta WhatsApp." Amina fita ta yi daga motar ta koma bangaran Abban da yake can zasu kwana.
Amina kwance ta samu Mansura kamar yadda ta barta. Zama ta yi gefan Mansura tana kallanta ta ce "Na zaci zan dawo in iske Kun yi barci, in fara jin labarin Fatima, kinsan har so nake ki rigani yin barci dan in ji labarin Fatima, wai wacece Fatimar nan ne da kika dameni da kiranta a barcinki?." Tun da Amina ta fara magana Mansura ke aikin zazzare ido tashi Mansura ta yi daga kwancan da take ta ce "Dan Allah me nake cewa?."
Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ina tambayarki wacece Fatimar da kike Kira a barcinki kina tambayata me kike cewa."
Mansura tari ta kama ta dafe karjinta da take jin kamar zai fito, take idanunta suka kada suka yi jajir, har yanzu Kuma ba ta fasa tarin da take ba, take hankalin Amina ya tashi ganin yadda Mansura ke tari gata rike da kirji.
Amina dafa Mansura ta yi tana mata aikin sannu. Mansura dago idanunta ta yi da duk haskansu sai da suka kada suka yi ja ta ce "Amina dan Allah ki yi shiru koda ace kin ji bakina ya furta wata kalma akan Fatima dan Allah karki tambayan akanta, zuciyata ta yi raunin da bana iya bayani akan komai."
Amina Kai ta daga ma Mansura tana danasanin tambayar da ta yi mata ganin yadda take ta birkice Mata.
Amina ruwa mai sanyi ta kawo ma Mansura ta ce "Dear ki sha ruwan sanyi." Kai Mansura ta girgiza ma Amina hakan ya sa ta aje ruwan cikin sanyi.
Amina tsabar yadda jikinta ya yi sanyi da halin da taga Mansura ya sa ko takan Abba ba ta biba da yake jiran ta tura mai recording din da ta yi mai na firarta da Mansurar.
Abba da ya ji shiru text ya tura ma Amina na ya ji shiru, Amina sending recording din ta yi ma Abba ta WhatsApp.
Abba koda ya gama sauraran daukar bai fahimci komai ba game da Mansura, sai rudin da ya fahimci tambayar ta je fa Mansura, dan ko yananin yadda Amina ke magana ya nuna hankalinta atashe take ma Mansura magana. Abba bai gama jin ƙarshen daukar ba ya kashe ya Kira wayar Amina.
Amina na dagawa Abba ya ce "Ba Mansura Wayar." Amina tashi ta yi ta kanga ma Mansura wayar a kunnanta.
"Hello, Mansura kina jina." Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Eh Yaya Abba ina ji." Abba shiru ya yi kafin ya ce "Ya na ji muryarki kamar kina kuka?."
Mansura sanin ta yi ma Abba alƙawarin ba zata Kara kuka ba ya sa ta ce "A'a ba kuka nake ba." Kin tabbata." Eh Allah Yaya Abba ba kuka nake yi ba." Okay gani a wajan get fito in gani." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.
Mansura tashi ta yi tana Kuma goge hawayanta ta kalli Amina ranta alamun bace ta ce "Ke kika ce ma Yaya Abba ina kuka?."
Amina kallan Mansura ta yi ta ce "kin ji na yi waya dashi ne?." Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Tom ni ya zanyi hawayena ya tsaya?."
Amina tashi ta yi ta zauna tana kallan Mansura ta ce "Bari in Kuna miki kira'a ki saurara ranki zai yi sanyi."
Mansura turo ma Amina baki ta yi ta ce "Yaya Abba fa ya ce inje in ya gani in ba kuka nake ba, Kuma na yi mai alƙawarin ba zan Kara kuka ba." Okay, ki dauraye fuskarki ki shafa powder ba zai gane ba."
Mansura fuskarta ta dauraye ta zo Amina ta shafa Mata powder kafin ta fita.
Abba na zaune ckin motarsa ya hango Mansura hakan ya sa ya fito daga cikin motar ya jingina da motar.
Mansura na wasa da hannuwanta ta karaso inda Abba yake.
Abba hararar Mansura ya yi ya ce "Baki iya sallama ba ko ?."
Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba ya ce "Shi kenan inda ba zaki yi min sallama ba wace ki tafi."