Sashe 1
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
⭐ABBANA⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar👇🏻
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Fadeela
*Abdurrahim
*In da rai
*Daga Allah ko dora ma Kai
*So ne sila
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi.
By FADILA SANI Bakori
GARGADI
Ban yadda ba, ban kuma laminta ba, wani ko wata ya canza min labari, ko ya yi min amfani da shi ba tare da amince wata ba. Yin hakan kuskure ne babba dan haka a kiyaye.
P 1-2
Bismillahir rahmanir rahim.
Garin Kaduna, safiya ce, 8:00AM wanda ya yi daidai da 9/7/2025. Amma sakamakon tsananin hadarin da yake garin ya sa garin ya yi hudu.
Gudu take Wanda babu waiwaye acikinsa bare kuma alamar gajiyawa, sai uban haki da take yi. A yanayin yadda take gudin kadai zaka kalla ka san ba cikin hayyacinta take gudin ba. Ga garin ya yi duhun hadari Wanda har an fara sakin ruwa kadan-kadan. Bisa ga alama, hakan ya sa mutane su ka yi Karan ciki a hanyar, duk an yi gudun ruwa. Zan iya cewa ita kadaice a hanyar wadda baka jin komai sai shashshekar hakin da take yi. Ja ta yi ta tsaya dan tsananin ruwan da ake yi ya sa har ba ta ganin hanya. layi ta fara kamar wadda ta sha ta bugu. Daga karshe dai jirine ya dibeta ta yanke jiki ta fadi a wajan. Ya zamana ruwan saman nan gaba daya kanta yake sauka. Bisa ga alama Kuma kamar ba a suma ta yi taba, dan tana jijjuya hannunta wanda da alama ta bugu da shi ne.
"Yaya kalli can ka gani kamar mutum?" Cewar wata matashiyar budurwa da suke cikin mota wanda da alama tsananin ruwan da ake yi ne ya sa suka yi parking. Da kallo ya bi in da Amina ta nuna mai. Shiru ya yi yana kallan matashiyar budurwar da ke kwance a wajan, ga ruwa na sauka kanta babu alamar za ta tashi.
Motarsa ya fara ƙoƙarin ja ya bar wajan, Amina da suke tare ta ce "Yayana, mutum fa na ce maka a kwance, Kuma kana ƙoƙarin jan mota."
"Amina, me za mu yi mata ana ruwan nan? Wana irin taimako za mu iya yi mata mu da ba yan garin nan ba?." "Ko Asibitin garin nan Yaya sai mu biya mu mikata Mana, daga can sai mu wuce."
Kallan baki da hankali ya yi Mata ya ce "Amina kin san Allah babu inda zani, zai yi wahala ma ba mahaukaciya ba ce, in da dai babu yadda za ai mai hankali ya kwanta a kasa a titi ruwa na bugunsa."
Yana gama fadar haka ya ja motarsa ya bar wajan sakamakon ruwan saman ya fara tsagaitawa.
"Laaa, Yaya kalli tana daga hannunta, Wallahi daga gani taimako take naima dan Allah mu tsaya mu yi magana da ita ko damuwarta mu ji Mana."Cewar Amina.
Tsaida motar Abba ya yi, yana kallan Amina, ya ce "Ki je ki dubata ki yi maganar da za ki yi da ita babu inda zani."
Amina sauka ta yi tana tafiya dari-dari kamar mai jin tsoran za a kamata, a haka har ta karasa in da matashiyar budurwan nan take kwance. Amina cikin tsoro ta ce "Baiwar Allah Lafiya kika zo nan kika kwanta?."
Da sauri matashiyar nan ta tashi kamar zautatta ta rirrike Amina tana cewa "Ki taimaka min dan Allah, ki taimaka min." Amina tsayawa ta yi tana kare Mata kallo, a iya fahimtarta kamar ba babu alamun hauka a tare da ita, tsabar razana ne da tashin hankali ta hanga tare da ita. Ajiyar zuciya Amina ta sauke, ta ce na ji zan taimaka Miki, fada min da me kike so in taimaka Miki?." Matashiyar budurwan nan, babu abin da take cewa ma Amina sai "ki taimaka min." abin da take ce Mata kenan.
Amina hannunta taja suka nufi motar yayanta da ita. Tun kafin su karasa ta fisge hannunta daga na Amina ta ruga ta shige cikin motar da yake a bude Amina ta barta ta dauke umbrella da za ta fita sakamakon ruwan da ake yi.
Daga Amina har yayanta da mamaki su ka bi matashiyar budurwan nan da kallo, wadda kallo daya za ka yi Mata ka fahimci ba cikin hayyacinta take ba.
Abba kallan matashiyar budurwan nan ya yi ya ce, "Lafiya wacece ke?"
Maimakon taba Abba amsar tambayarsa, kallansa ta fara yi, can Kuma ta Fashe da kuka tana huna masu hannunta tana cewa "Na kasheshi! Na kasheshi!! Na kasheshi!!! Kun ga hannuna." Ta idasa maganar tana nuna masu fararan hannunta.
Abba kallan Amina ya yi yana cewa "Amina, kin ga abin da kika jawo Mana ko?." Yanzu sai ki san yadda zaki yi ki fitar min da ita daga mota."
Ajiyar zuciya Amina ta sauke tana mai Kuma kallan matashiyar budurwan nan da har yanzu abin da take furta wa kenan na kashe shi, Kunga hannuna.
Amina handbag dinta ta bude ta ciro kudi tana mika ma matashiyar budurwan nan ta ce "Kawata amshi wannan ki je ki sai wani abu ki ci kin ji ko."
Maimakon ta amshi kudin da Amina ke miko Mata, Kai ta fara girgiza ma Amina tana Kara tsananta kukanta tana cewa "Na kasheshi." Tana mai Kuma nuna masu hannunta da basu fahimci kamai ba a hannun da take nuna masu.
Amina cikin karfin hali ta ce "Wa kika kashe?." Kuka ta Kuma fashewa da shi Maimakon taba Amina amsa, ta Kuma maimaita mata
"Na kasheshi."
Amina Kai ta girgiza tana kallan Yayanta ta ce "Yaya Abba, ya za mu yi da ita? bisa ga alama ma kamar ba cikin hayyacinta take ba."
"Babu yadda za mu yi da ita, Kuma kinsan dai ba zai yuwu mu tafi Katsina da ita ba, kin ji dai furucin da ke fita a bakinta."
"A'a, Yayana Ina ganin kamar furgici ne ya sa ta fadin haka, wannan daga ganinta ko kiyashi ba za ta iya kashewa ba, ka ga har yanzu ruwan bai tsaya ba, Ina ganin mu yi hakuri mu tafi da ita kafin ta dawo hayyacinta, na san ko mama ba za ta yi fada ba, inda ita ke horarmu da yin taimakon."
Shiru Abba ya yi bisa ga alama nazarin maganarta yake yi.
Amina hannun yayanta ta kama ta ce "Dan Allah yayana."
Motar Abba ya ja suka tafi ba tare da ya ce komai ba.
Suna tafiya matashiyar budurwan nan ta kwanta ta kama barci. Amina da yayanta da kallo suka bi ta.
Ba ita ta farka ba sai suna gaf da shiga garin Katsina, ta tashi a gigice tana ƙoƙarin balle murfin motar ta fita. Amina ganin abin da take ƙoƙarin yi ya sa ta ce "Yaya Abba, tsaidar da motar nan tana ƙoƙarin budewa ta fita."
Gefan titi Abbab ya koma ya yi parkin. Matashiyar budurwan nan Kuma bugun glass din motar ta take tun karfinta. Bisa ga alama dai kamar a gigice take.
Wata uwar tsawa Abba ya yi Mata Yana Mai bude mata murfin motar ya ce "Fita! Idan tafiya kike son yi fita na ce." Cikin gigi ta fita tana mai rike Amina da itama ta fito daga cikin motar.
"Wayyo Allah na kashe shi! Na kashe shi!!." Ta fada da karfi tana mai Kuma rirrike Amina tana nuna mata hannunta."
Amina kafin ta yi magana sai ganinta su ka yi ta yanke jiki ta fadi sumammiya.
Abba kuma cikin takaicin wahalar da suka dakko ma kansu da kansu ya kalli Amina ya ce "Kin ga wahalar da kika sa muka dakko ma kanmu ko?, Kiri-kiri Kinga tana naiman tara Mana mutane, yanzu sai ki fada min yadda za mu yi da ita?."
Amina cikin sanyi ta ce "Yaya dan Allah ka kamata mu kaita asibitinku Mana a dubata."
Abba cikin takaici ya ce "Kina da kudin da za a dubata a asibitin mu din ko?."Yaya Abba Ina da su, ka kamamin ita mu maidata mota dan Allah."
Abba kafafunta ya kama a kyamace kamar ya taba kashi suka shimfidar da ita cikin motar. Sannan ya ja motar suka tafi.
Tafiya kadan su ka yi ya danna hancin motarshi cikin wata private Asibiti da ke bakin hanya.
Amina cikin sanyi ta ce "Yaya dan Allah mu kaita asibitinku Mana, ka ga can komai zai zo da sauki, nan fa asibitin kudi ce ni dai dan Allah ka kaita asibitinku."
Abba ko saurarar Amina be yi ba ya danna hancin motarsa cikin Asibitin. Suna zuwa ya kalli Amina ya ce "Na gama iya nawa, saura na ki, fitar min da ita daga motata."
Yadda Abba ya yi magana bai ba Amina damar sake neman wata alfarmarsa ba.
Hakan ya sa itama bata Kuma cewa komai ba ta fita daga cikin motar ta nufi cikin asibitin, babu jimawa suka taho da gadon da aka tana da dan taukar marasa lafiya. Da taimakon malaman Asibitin aka sa baiwar Alllah nan gadon da suka ta nada dan daukar marasa lafiya.
Amina kallan Yayanta ta yi ta ce "Yaya daga an dubata zan taho nima."
Shi dai ko tankama Amina bai yi ba ya ja motarsa ya tafi.
Tafiya kadan ta Kai Abba gida, kasancewar babu nisa sosai tsakaninsu da Asibitin da ya Kai 'yar tsuntuwar tasu.
Ana ta sallar la'asar hakan ya sa Abba bai shiga gida ba sai da ya yi Sallah sannan.
Yaran kanwar Abba na jin parking din motarshi suka ruga da gudu suna mai oyoyooo. Take Kuma suka fara waige-waigen Amina ganinsa shi kadai.
Amira ta ce "Yaya Abba Ina mommy Amina fa?." Abba murmushi ya yi masu ya shafa kan Sadik ya wuce ba tare da ya basu amsa ba.
Mahaifiyarsu Amina da kallo ta bi Abba ganin ransa kamar a bace yake Kuma ba ta ga Amina ba, bacin ko lokacin da za suka taho sun yi waya da Aminar. Bayan ya zauna ta kallai ta ce "Abbana, ya na ganka Kai ka dai, Ina Aminar fa?."
"Mama, ina tsoran Kar tausayin Amina ya jefata a wani halin."
Nan Abba ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da mahaifiyar tasu.