← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 36

Sashe 36

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bangaran Mansura ko duk hidimar bikin nan da ake Mansura tana yake ne kawai saboda bata jin dadin jikinta kusan kullum da zazzabi take kwana.

Da magariba aka kawo Amarya gidan, inda gidan ya cika da mutane, Wanda duk budirin da ake yi Mansura na kwance ta lillibe kanta hidimar biki ya sa ba Wanda ya lura da halin da Mansura take ciki.

Abba Kuma ya Kira wayarta ya fi a kirga ba ta daga ba dole ya sa ya rabu da ita.

Washagarin kawo Amarya yan uwansu Abba duk suka watse ya zamana daga Amina sai Aunty Zainab, itama ana yin magariba mijinta ya zo ya dauketa ta tafi.

Tun da aka fira hidimar bikin Abba baisa Mansura ba a idansa, gashi ko ya Kira wayarta bata dagawa.
Abba shigowarsa gidan kenan ya iske mahaifiyarsa da Amina sun rako Aunty Zainab. Abba da sauri ya nufi bangaran mahaifiyar tasa har bedroom din Mansura, Kwance ya samu Mansura can karshen gadon bedroom dinta ta gudindine da bargo, Abba cikin damuwa da yadda ya ga Mansurar dan bisa ga alama bata da lafiya ya ce "Mansura." Ya Kira sunanta a hankali yana janye bargonta. Mansura cikin muryar irinta ciwo ta ce "Ni ka rabu dani ka tafi wajan Amaryarka, tun da aka fara bikin nan ka manta dani baka ma san halin da nake ciki ba."
Abba cikin damuwa da yadda ya ji jikin Mansura rau da zazzabi ya ce "Haba baby kulllum sai na kiraki a waya baki dagawa ga gidan cike yake da mutane na rasa yadda zan yi in shigo, dama baki da lafiya baki fada min ba."

Abba ya dago Mansura yana kallanta ta yi mai rama sosai kamar wadda ta dade tana ciwo. Abba cikin mamaki da ganin yadda Mansura ta rame mai ya ce "Subhannallahi, meke damunki kika rame haka?."
Mansura fashe ma Abba da kuka ta yi.
Abba kwantar kan Mansura ya yi kan kafadar yana bata hakuri ya ce "Ki yi hakuri bari in kawo miki magani ki sha." mahaifiyar Abba da Amina jin kukan Mansura suka shigo bedroom din.

Daga mahaifiyar Abba har Amina da kallo suka bi Mansura da Abba, ganin yadda Mansura kusan gaba daya take kwance ajikin Abba tana kuka.

Abba rudewar halin da ya ga Mansura tasa ya bai lura da yadda suke da Mansurar ba ya ce "Amina dama tun da aka fara hidimar bikin nan yarinyar nan bata da lafiya Amma dan iskan ciki baki fadamin ba kika ci gaba da hidimarki bacin ke ke tare da ita, kalli yadda ta rame kwana biyu kawai."

Mansura ko har yanzu tana jikin Abba tana kukanta.
Daga mahaifiyar Abba har Amina sun kasa cewa komai tsabar mamakin yadda suka ga Mansura jikin Abba kwance dukansu ko ajikinsu.....✍🏻

Littafin Abbbana na kudi ne na gama free pages daga yau na gama posting dinsa Mai bukata my number 08063830828

Littafin ABBANA cike yake da cakwakiya, karku manta Abba auran sirri ya yi da Mansura koya zamansu zai kaya.....?

Wacece Mansura.... ?

Shin bakwa ganin mafarkin Mansura zai iya zama gaskiya kuwa ?

Koya zaman Mansura da Aisha zai kaya acikin gidansu Abba a matsayin kishiya da Kishaya.....

Ko waye Wanda Mansura take yawan Kiran Abbana da shi a mafarkinta.....

Duk mai bukatar cikigaban littafin Abbana my number 08063830828

Idan ba siya zaki ba karmu bata ma juna lokaci dan Allah 08063830828
Chapter 36 · 0% Book details