Sashe 15
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A falon Mahaifiyar Abba Abba ya zauna, kafin ya ce ma Mansura "Me ya sa ke kika dawo?."
Mansura zata yi magana sai kuka, babu irin tambayar da Abba bai yima Mansura ba amma taki Magana sai kuka take. Abba Kiran Amina ya yi a waya tana dagawa ya ce "Amina me aka yi ma yarinyar nan?." Amina na jin haka ta san Mansura yake nufi, cikin jin haushin Mansurar ta ce "Yaya Abba babu fa abinda aka yi mata, ita kawai komai kuka take Mai, matar da za ka aurace fa daga ta yi...." Tsawar da Abba ya yi ma Amina ce ya sa ta yi shiru. Dan yasan wa take nufi an fada mishi tare da Aisha suka tafi.
Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abin da zan mik.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za su je naimamaka auranta✍🏻
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828
P 17-18
Abba cikin bacin rai ya ce "Wallahi Koda wasa kika kara hadani da yarinyar nan zaki ga abinda zan Miki.." ai ko hadaka da ita yanzu ma ta fara, dan gobe iyayanka za suje naimamaka auranta."
Abba shiru ya yi bai tanka, ba daga ƙarshe ya tashi ya koma sight dinsa.
Washegari kamar yadda mahaifiyar Abba ta ce iyayan Abba suka je naiman auran Aisha. Kasan cewar iyayan Aisha manya mutane ne, mahaifinta babban malami ne kusan ansa shi kaf cikin garin Katsina, hakan ya sa aka yi komai kamar yadda addinin musulunci ya tsara.Inda aka sa ranar auran daidai dana Amina sati 11 kenan.
Bayan an kammala komai baba karami ya taho da cingam da biscuit da sweet ya nufi gidansu Abba.
Kasan cewar weekend ne ya sa Abba yana gida, yana falon mahaifiyarsa zaune baba karami ya yi sallama ya shigo rike da kwalayan biscuits a hannunsa, diresu ya yi kafin ya dora da cewa "Aisha ga abin sa ranar nan, munje anyi komai an gama an tsaida lokacin aure daya da na Amina. Amma gaskiya duk mun yi murna ganin inda Abba yaje ya naimi aure, dan gidan shaikh Sani babban gudane, juri'ar gidan duk malamai ne, fatan dai Allah ya nuna Mana ranar lafiya."
Mahaifiyar Abba sun dade suna tataunawa da Baba karami akan auran kafin ya yi mata sallama, ya kalli Abba da bacin gaisawa da suka yi uffan baice ba. Baba karami ya ce "Abba muje sauran kayan na motata ka dakko."
Abba tashi ya yi ya bi Baba karami, suna fita Abba ya kalli baba karami cikin alamun damuwa ya ce "Baba karami, Wallahi ko kadan bana son yarinyar nan da mama ke shirin hadani da ita, tom amma inda aikin gama ya riga ya gama ya zanyi, inda har kun riga kunje, Amma baba dan Allah Ina naiman alfarmar a daga auran nan da wata 5 lokacin na kammala duk wani shiri da zanyi, ka ga shi kanshi wanda zai auri Amina bashi da amini sama dani, dukanmu ba za mu ji dadin hudimarmu ta kasance rana daya ba."
Shiru Baba karami ya yi kafin ya dafa Abba ya ce "Abba ka kwantar da hankalinki ka ji, hakika mahaifiyarka ta zabar maka aure gidan ya ya dace, gidan mutunci, in sha Allah za ka yi alfaharin zama da ita nan gaba, maganar aure Kuma da kake so adaga inda kaine me yi ba za a shiga hakinka ba za a d'aga kamar yadda kanaima, gobe zan je in samu iyayan yarinyar mu yi magana."
Godiya sosai Abba ya yi ma baba karami kafin ya dauki kwalayan ya shiga da su falon mahaifiyar tashi.
Aisha ko lokacin da mahaifiyarta tasanadarmata da sa ranarta da Abba tayi murnar amma fargaba tafi yawa atare da ita, dan tun ranar da Abba ya zo wajanta har yau bai sake dawowa ba, bare Kuma ya kirata. Amina wayarta ta dakko ta tura ma Abba da Sako kamar haka "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zabin zuciyata. jiya na zo gidanku cike da dokin ganin kyakkyawar fuskarka, sai dai kash lokaci ya rike min Kai baibani damar ganawa da Kai ba, amma banyi fushi ba inda na ga fuskar da ta yi sanadin zuwan taka fuskar duniya. cikim hikimar Allah Kuma a yanzun nan na ji wani daddadan albishir din rayuwa tare da kai na har abadan abidina in sha Allah.
Abba Koda ya gama karanta sakon Aisha tsaki ya yi ya goge text message din.
Mahaifiyar Abba ko sosai ta yi mamaki lokacin da sakon daga ranar auran Abba ya isa gareta, ta nan zaune Abba ya shigo da shirinsa na tafiya aiki.
Abba ganin yadda mahaifiyarsa ta daure fuska kamar ba ta taba dariya ba hakan ya sa ya sha jinin jikinsa, dan Koda ya gaidata ba ta amsa gaisuwarsa ba ta ce "Meye nufinka na daga auran nan da kasa aka yi?."
Abba cikin son mahaifiyar tasa ta fahimce shi ya ce "Mama nifa kadai ne maiyin hidimar nan, duk da baba karami ya ce zai yi ma Aisha kayan daki ba barmai zan yi ba inda hidima yanzu shima ta yi mai yawa, Ina ganin kamar in aka daga din zan fi jin dadin yin tawa hidimar cikin kwanciyar hankali idan ba a hada ba."
Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Hmmmm, Idan ma da wata manufar ka yi ya rage naka, dan ko bayan raina ka fasa auran Aisha ban yafe maka ba."
Abba da mamaki ya dago kansa ya kalli mahaifiyarsa jin murucinta, amma baice komai ba ya yi mata sallama ya tafi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya babu ranar da Aisha ba za ta tura ma Abba sakon gaisuwa ba, daga ya ga itace ko karantawa ba ya yi yake gogewa.
Mahaifiyar Amina ganin biki sai gabatowa yake har yanzu ba ta ji sun yi maganar anko ba ya sa ta samisu Aminar ta ce "Mansura Wai ba za ku fidda anko bane? Wata daya biki ya rage amma har yanzu ban ji Kuna maganar anko ba? Ko ba za ku yi bane, ga kudin gyaran jiki har na biya mai gyan jikin zata fara zuwa duk abin da za ku yi ku yi kafin a fara gyaran jiki dan daga an fara babu fita."
Mansura duk da take ba ma'abociyar zuwa biki ba tasan ana anko, hakan ya sa ta kalli mahaifiyar Amina ta ce "Mama gobe sai mu je musiyo."
Amina dai ba ta ce komai ba,dan tuni take so ta yi ma Mansura maganar ankon amma Kuma tana tsoran Mansura ta shiga damuwa dan daga anyi maganar bikin take shiga damuwa tunanin zata fara rayuwa babu Amina.
Amina Kuma wayarta ta dakko ta Kira Aisha ta shaida Mata ta zo gobe za su je siyo anko."
Aisha sosai ta yi murnar hakan, dan tana jin dadi duk lokacin da ta ga sun nuna kalawarsu akanta, hakan na rage mata fargabar zama da Abba inda Allah ya bata soyayyar danginsa.
Washegari su Amina suka shirya suka je suka siyo ankon, inda suka zabi lass dinsu me kyau da atamfa. Suna hanyar dawowa ne Aisha ta kalli Amina ta ce "Amina za ku yi walima ne?." Tom Wallahi ban sani ba amma kila mama ta yi." Cewar Amina.
Haka suka ci gaba da hirarsu har aka zo kofar gidansu Aisha ta sauka aka wuce da su Mansura gida.
Tun daga wannan ranar walwalar Mansura ta rage ya zamana kullum cikin damuwa take. Haka nan take jin kamar ba za ta iya rayuwa a gidan babu Amina. Hakan sai ya Kara c maida Mansura shiru-shiru a gidan.
Yau mahaifiyar Abba suna zaune kallan Abba ta yi ta ce "Wata daya kenan da kwanakai da sa ranar auranka da Aisha, tun da aka sa ranar ka je wajanta?."
Abba Kai ya fara sosawa alamun rashin gaskiya.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi kafin ta ce "Ka shirya ka je yau, idan ka je ka tambayeta nawa ne kudin ankon Amina kabata, Kuma ka kirata ka sanar Mata zuwanka."
Abba shiru ya yi baice komai ba ya tashi ya fita. Amina ya Kira ya ce ta zo ta rakashi gidansu Aisha. Amina da dokinta ta bishi suka tafi bayan ta sanar da Mansura zata raka Abba.
Abba suna tafiya ya kalli Amina ya ce nawa ne lass din da kuka fidda da atamfa?." Duka 45 thousands."
Kai Abba ya jinjina.
Suna zuwa kofar gidansu Aisha Abba ya tura ma Amina text message kamar haka "ki fito ga ni a kofar gidanku."
Kasan cewar wayar Aisha ba ta kusa da ita hakan ya sa bataga sakon Abba ba.
Abba jin shiru-shiru Aisha bata fito ba key ya sa ma motarsa ya juya zai tafi. Amina rike hannun Abba ta yi tana marairaicewa ta ce "Yaya Abba baka kirata Mana."
Abba daure fuska ya yi ya ce na tura Mata text tun dazu wayau zata raina ma mutane."
Amina Kai ta girgiza tana tunin in ita ce Aisha gara ta fasa auran nan, dan kadan daga cikin rashin son namiji kenan ba zai yi maka uziri ba ko daya, gashi nan ita tun kafin a yi auran ya kasa jurewa akan abin da baikai ya kawo ba.
Amina wayarta ta dakko ta Kira Aisha, ba ta daga ba sai da ta sake Kira kafin ta dauka. Amina cikin tausaya ma Aisha ta ce "Mommyna gamu a kofar ginku ni da Yaya Abba."
Aisha sai yanzu ta lura da sakon da Abba ya tura Mata. Hijab dinta ta zura har kasa ta fito.
Amina kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba dan Allah ka so Mommyna Mana kodan sunan mama da take da shi, Kuma Wallahi tana sonka sosai." Abba daure fuska ya yi, hakan ya sa Amina ta ja bakinta ta yi shiru. Suna a haka Aisha ta fito.
Amina rungume Aisha ta yi tana cewa "Mommyna." Dan Amina sosai take jin son Aisha a ranta.