Sashe 35
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba da tsoran yin magana yake ji gudin Kar mahaifiyarsa ta ji hakan ya sa baiba Mansura damar Kara yin magana ba hannunsa na rufe da bakin Mansura ya kwantar da ita ya kwanta bayanta yana Mata magana a hankali a cikin kunne dan duk ya firgita da Kiran mahaifiyarsa da ta yi.
Abba cikin sanyi da lallashi ya ce "Haba Mansura so kike ki tona min asiri kome? Meye na Kiran Mama cikin darannan? Yanzu dai inda duk bayanin da zan Miki kinki saurarata Kuma kin ki yadda da abinda nace zan Kira maki Amina ki ji, Wallahi har yanzu bana jin soyayyar mommy cikin raina zan aureta ne kawai dan in faranta ma Mama rai, maganar da kika ji ina yi awaya mommy ta fahimci ke nake so Kuma na fada Mata zan aureki shine ta ce ta hakura idan har zan aureki ba zata iya kishi dake ba saboda nafi sonki, tom idan har mommy ta furta ma Mama haka zan fuskanci fushin mama, Kuma kinsan fushin iyaye akan yayansu bashi da kyau, kin ji dalilin da ya sa na amsa ma Aisha na fasa auranki dan a wuce maganar."
Abba har ya kari maganarsa ya gama Mansura batace mai komai, ranar dai haka suka yi barci kowa zuciyarsa ba dadi.
Kiran sallar farko Abba ya tada Mansura ya bude kofar falon ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta.
Mahaifiyar Abba bayan ta idar da sallar Asuba tana zaune Mansura ta shigo gaidata, suna cikin gaisawa Abba ya shigo. Mahaifiyar Abba kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura hala jiya mafarki kika yi, kina ta Kiran sunana da karfi abin har ya naimi ya ban tsoro, na je Kuma inata bugun kofarki na ji shiru."
Abba katse maganar ya yi ya ce "Ina kwana mama, kin tashi lafiya, hala mafarki ta yi." Lafiya lau Abba, ina jin Kam mafarkin ta yi baka ji ba Wallahi yadda take kwalamin Kira da na yi Mata magana Kuma shiru."
Mansura tashi ta yi kanta kasa ta gaida Abba, ta tashi ta fita da sauri ta nufi kitchen tana so ta sha tea ta tashi da yunwa. Bayan Mansura ta fita ta jimawa Abba ya tashi ya fita, ya nufi kitchen din inda ya ga Mansura ta yi.
Abba na zuwa ya yi hugging din Mansura ta baya ya ce "Da fatan kin tashi lafiya, ya fushi dani." Lafiya Lau, inanan Ina yi."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Shi kenan, yanzu za ki bar yinsa." Abba na fadin haka ya Kira Amina a waya.
Amina da mamaki ta bi wayarta da kallo ganin kamar Kiran ya yi wuri. Dagawa Amina ta yi tana gaida Abba. Bayan sun gaisa da yake wayar a speaker ya sa Mansura na ji Abba ya ce "Amina Ina naiman taimakonki kisa baki Mana ko Mama zata janye aurena da Mommy." Daga bangaran Amina ido ta zaro ta ce "Yaya Abba har yanzu dai ka kasa hakura da Mommy, ko jiya Wallahi ta kirani tana kuka ta kawo min kararka ta ce baka kiranta sai in ita ta kiraka Kuma in ta kiraka dinma ba lallai ka daga ba. Haba Yaya Abba yau fa saura kwana 28 bikinku kake wannan maganar, Kuma kasan zaka fuskanci fushin mommy indai ka ce zaka fasa auran nan,Koda yake Yaya Ahmad ya ce wai Mansura kake so, tom Yaya Abba in ma Mansurarce zabinka ka hadasu su duka ka aura Mana."
Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura alamun kinji ko. Har yanzu hannunsa daya Yana rike Mansura. Daidai lokacin mahaifiyar Abba ta shigo kitchen din.
Abba da sauri ya saki Mansura ya ce ma Amina "Shi kenan zan kirakk."
Abba na fadin haka ya kashe wayar yana kallan Mahaifiyarsa ya ce "Ruwan zafi na zo samu yau a gida nake son yin breakfast."
Mahaifiyar Abba bata tanka ma Abba, Abba Kuma ruwan zafin hannun Mansura ya amsa ya fita da sauri.
Mahaifiyar Abba Mansura ta bi da kallo, kafin ta ce "Mansura kina so ki bata tarbiyar da nasanki da ita ko? Tom shi kenan babu ruwana idan kin biye ma Abba auransa zai yi kina gani, Kuma kisa a ranki duk yarinyar dake bari Namiji na taba bata wallahi ba auranki zai yi ba, inma Allah ya sa ya aureki ba zai ganki da daraja ba, idan ma tsoro kike dan karya rabu dake kike sake mai jikinki nanma daga ya samu abinda yake so rabuwar zai yi dake."
Mansura dai shiru ta yi kanta kasa bata ce komai ba, mahaifiyar Abba Kuma ta dage sai fada take mata.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, inda yanzu shakuwar Mansura da Abba ta wuce duk yadda kuke tunani, soyayyarsu suke sha sosai abinsu, kullum mahaifiyar Abba daga ta rufe kofa Mansura zata je ta bude ma Abba ya shigo sai asuba zata bude mai ya fita ita Kuma ta rufe kofar falon ta koma ta kwanta.
Sai dai yanzu Mansura cike take da fargaba da tunanin auran Abba da Aisha dan saura sati daya bikin.
Yau Mansura suna kwance da Abba suna babarci ta tashi cikin gigita tana dafe Kai, saboda mafarkin da ta yi.
Abba kallan Mansura ya yi yadda ta yi zufa kamar wadda ta yi gudu, Mansura Kuma fashewa da kuka ta yi tana cewa cikin kuka "Yaya Abba na sake maimai mafarkin rannan, na yi mafarkin ansa min handcuff a hannu gani a gidan yari Kuma Wai ga jariri a hannuna sai kuka yake." Mansura ta idasa maganar cikin kuka tana cewa "Na fara tsoran mafarkin nan na fara razana da abinda nake gani ina tsoro." Mansura ta idasa maganar cikin kuka sosai.
Abba bubbuga bayan Mansura ya yi ya ce "In sha Allah babu abinda zai sameki sai alkairi, ki yi ta addu'a, yaron da kika gani Kuma yaron za ki haifa Mana ne in sha Allah." Kai Mansura ta girgiza ta ce "Ina yawan faduwar gaba Yaya Abba yan kwanan nan a firgice nake, Ina ji kamar wani mugun abu zaisam.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi ya ce "Babu abin da zai sameki in sha Allah."
Mansura bata Kuma cewa komai ba, kanta ta dukar tana kuka kadan-kadan.
Abba cikin damuwa ya kalli Mansura ya ce "Mafarki fa ba gaskiya bane."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ko ba haka ba Yaya Abba mun kusa rabuwa za ka yi min nisa zaka koma gidan matarka da kwana, bacin kasa ba min barci tare da kai."
Abba kan Mansura ya shafa ya ce "Shi ya sa na tsaida aikin gidana, ba ayi komai ba, yau dinnan nake shirin sanar da Mama Mommy anan gidan Aisha zata zauna a bangarena kafin na gara gidana, kin ga sai in raba maku kwana, duk ranar kwananki zaki bude min kofar in shigo nan in kwanta haka ya yi miki ai?."
Mansura kamar za ta yi kuka ta ce "Ita Aishar ya za ka ce Mata duk ranar da ba zaka kwana dakinta ba?."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Zan fada mata a Asibiti aka maidani haka idan na yi kwana biyu gida kwana biyu a Asibiti."
Mansura dai batace komai ba, Abba Kuma ganin an fara kiraye-kirayan Sallah ya kalli Mansura ya ce "Mu je ki bude min."
Mansura bude ma Abba kofar falon ta yi ya fita ita Kuma ta rufe ta koma ta kwanta.
Yau Abba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa ya kalleta ya ce "Mama gobe zansa an yi fenti sabo a bangarena, saboda a nan Mommy zata fara zama, har yanzu aikin gidana ya kasa karasuwa, Wanda na ba kudin aikin gidan ya cinye kudin baiyi koma ba sai jiya da naje na gani."
Shiru mahaifiyar Abba ta yi kafin ta ce "Shi kenan, sai ka yi kokari ka gyara karta jima a nan din." Abba sun jima suna magana akan bikin da mahaifiyarsa kafin ya tafi wajan aiki.
Yau saura kwana uku bikin Abba da Aisha, yau Kuma Amina ta iso garin, zoka ga murna wajan Mansura da Amina kamar za su cinye juna tsabar murna. Mansura na rike da Amina ta saketa ta ruga da gudu zuwa bathroom tana amai.
Amina bin bayan Mansura ta yi tana mata sannu, Mansura daga ma Amina hannu ta yi ta ce "Karki karaso kusa Dani, bana son kamshin turaran da kika sa shi ya sa ni amai."
Amina da ido ta zaro ta ce "Ka ji wani ciwo mai kama da na masu ciki."
Mansura hararar Amina ta yi batace komai ta dauraye bakinta ta fita.
Abba ko bayan ya dawo aiki ya iske Amina ta zo bai yi wani dokin zuwan Amina ba saboda ta toshe duk hanyar zai samu su kebe da Mansurar, Abba akwatin da ya shigo da shi ya Mika ma Mansura ya ce "Gashi kayan da zaki sa na biki akwai angon da su mommy suka yi duka aciki."
Mansura magana take son yi ma Abba amma ganin Amina ya sa ta waske ta ce "Na goge Yaya Abba Allah ya Kara budi." Ameen Abba ya ce ya tashi ya fita.
Bayan Abba ya fita Amina ta bude akwatin amfofi ne da lass a ciki sai bra da panties. Amina ido ta zaro ta ce "Ki ce soyayyarku da Yaya Abba ta yi nisa haka ban Sani ba, Amma soyayar taku Kamar ta yan bariki har da bra da panties, kin San Allah ki dauke bra din nan da panties dinnan ki boye Kar mama ta gansu."
Mansura daukewa ta yi ta bar kayan sawar kawai da handbag da kayan makeup ciki. Koda mahaifiyar Abba ta zo ta gani dadi ta ji sosai ganin yadda Abba ya gwangwaje Mansurar bata kawo komai a ranta ba.
Haka aka ci gaba da shirye-shiryan bikin Aisha da Abba, gidan su Abba ko ya cika da baki, ana gobe bakin da baki Yan nesa duk sun iso.
Ana gobe biki gidansu Aisha suka shirya Walima inda babu yadda Amina bata yi da Mansura dan suje walimar ba Amma taki zuwa, Amina ma lura da kamar Mansurar bata jin dadi ya sa ta rabu da ita.
Washagari aka Daura auran Abba da Aisha, daga ka ga Abba zaka lura da rashin kuzarin da yake ciki.