Sashe 2
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ikon Allah, ni ban san kalar zuciyar Amina ba, Kuma Abbana har da laifinka, taya zaka biye mata ku dakko yarinya tun daga garin Kaduna har nan Katsina, haba Abbana, sai ka ce baka san wacece Amina ba. Ni Kam na yarda da hausar nan da ake cewa wai d'an gado ya fi magaji. Haka mahaifinku yake da tsantsar tausayin nan amma Amina har ta fisa. Yanzu Abbana hakuri za ka yi in ka ci abinci ka koma kar yarinyar nan ta jawo Mana wata masifar.
Abba ya San idan ya ce ba za shi ba mahaifiyarsa za ta yi ta yi masa magiya, har sai ya yadda ya tafi, hakan ya sa ya barta a zai je. Yana gama cin abincinsa ya kama hanya ya fita.
Har dare mahaifiyar Amina ta ji shiru-shiru basu dawo ba, ba Abba ba Amina, Kuma ta Kira wayar Abba bai dauka ba, Amina ma haka ta Kira wayarta bata shiga.
Mahaifiyar Amina tana zaune tana zagaye madaidaicin falonsu ganin har 8:30 babu ko mutum daya a cikinsu. Tana a haka Allah ya shigo da Abba. Tun kafin ya karaso ta ce mai, "Ina Amina?." Gaban Abba faɗuwa ya yi dan bai dauka ba har lokacin Amina bata dawo ba.
" Ka je ka zo min da ita yanz..." Shiru mahaifiyarsu Amina ta yi sakamakon sallamar Amina da ta ji. Amina da sallamarta ta shigo falon tare da matashiyar budurwar da suka tsinto ita da yayanta.
Mahaifiyar Amina da kallo ta bi Amina da matashiyar da suke tafe da Amina. Wadda sai zare ido take tana kallan mahaifiyar Amina.
Amina cikin sanyi ta ce "Mama, kin jini shiru, ki yi hakuri tafe muke da bakuwa matsala ta fada Kuma sai da muka biya asibiti aka dubata."
Mahaifiyar Amina dai bata ce komai ba, kallan yarinyar da ke tafe da Amina ta yi, tana mamakin yadda take kallanta ba tare da ta gaidata ba. Mahaifiyar Amina cire mamakinta ta yi ta kalli matashiyar nan ta ce " 'Yan Mata ya sunanki?." Shiru babu amsa, Kuma babu wata alamar da ta nuna bata ji ba, dan kallan Mahaifiyarsu Amina take yi. Amina ganin haka tashi ta yi ta dafa kafadarta ta ce "Kawata bi ki ji ba, Mamana na tambayarki sunanki ba? Ya sunanki?." Ido ta daga tana kallan Amina, sannan a hankali ta ce "Mansura." Amina kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama, kin ji wai sunanta Mansura."
Mahaifiyar Amina shiru ta yi, sannan ta ce "Amina ku shiga ciki ta yi wanka ta ci abinci sai mu ji daga Ina take."
Amina hannun Mansura ta kamo ta ce "Kawata, zo mu je ki watsa ruwa ki ci abinci ki Sha magungunanki." Amina ta fadi maganar tana kamo hannun Mansura, Mansura Kai ta girgiza ma Amina alamun ba za ta ba. Babu yadda Amina bata yi da ita ba, Amma taki yadda ta tashi ta bi Amina, daga karshe ma sai ta yi kwanciyarta kan caution din da take. Daga Amina har Mahaifiyarta da Abba da ke tsaye duk mamaki ya cika su.
Mahaifiyar Amina kallan Mansura ta yi, ta ce a'a, ki tashi ki je ki ci abinci ki Sha maganinki tukun sai ki kwanta din."
Mansura shiru ta yi kanta sama daga gani ma ta yi nisa a duniyar tunani ba jin abin da Mahaifiyar Amina ta ce ta yi ba.
Abba da ransa ya fara baci ganin yarinyar kamar tana naiman raina masu wayau, ya ce "Ke! ba da ke ake magana bane, ba zaki tashi ba ana miki magana dan samun waje kin yi banza da mutane." Ya yi maganar cikin tsawa sosai wanda ba Mansura ba har Amina sai da ta firgita.
Mansura ko da ba jin abin da ya ce ta yi, ita dai ta ji ya yi Mata tsawa, hakan ya sa ta tashi ta rirrike Amina jikinta na rawa. Yadda take rawar jiki kawai zai nuna maka ba Karamar furgita ta yi ba. Tana Kuma zare manyan idanunta.
Amina ganin haka janta tayi suka nufi bedroom dinta da ita. Suna zuwa Amina da kanta ta hada Mata ruwan wanka, Amma babu dabarar da wayan da ba ta yi Mata ba taki yi, dole ta rabu da ita, ta kawo Mata abinci shima ko kallansa ba ta yi ba bare Amina ta sa ran zata ci. Amina ganin taki cin Abincin, Kuma taki shan maganin hakan ya sa ta kalleta ta ce " Ki dauki maganin ki Sha ko in je kin Kira miki yayana in ce kin ki shan magani." Mansura Kai ta girgiza ma Amina tana daukar maganinta ta Sha.
Abincin ko babu wayan da Amina ba ta yi Mata ba Amma taki ci, har cewa ta Kuma yi zata Kira Mata yayanta, sannan ta samu dakyar ta yi 1 spoon. Tana gamawa ta kwanta a wajan Amina dai kasa ce Mata komai ta yi ganin ko Sallah ba ta yi ba. Tana kwanciya Kuma kamar an tsakureta ta tashi ta shiga bathroom din dakin bata jima ba ta fito, ta koma inda ta tashi ta kwanta. Amina na nuna Mata bed dinta amma ko kallanshi ba ta yi ba ta kwanta kasa.
Amina Kuma wanka ta fara yi, kafin ta ci abinci dama kuma Sallah take yi ba.
Amina na gamawa ta fita falon sakamakon kiranta da Mahaifiyarta ta yi. Amina zaune ta iske Mahaifiyarta da yayanta da alama dai suna tattaunawa ne game da bakuwar da su ka yi.
Mahaifiyar Amina kallan Amina ta yi ta ce "Amina me kika fahimta game da yarinyar nan ?."
Ajiyar zuciya Amina ta sauke ta ce "Mama, Wallahi har yanzu ban yi magana da ita ba, ban da sunanta da ta fada mana har yanzu ban San komai game da ita ba. Amma gaskiya kamar yadda likitan da ya dubaya ya yi min bayani har yanzu bata cikin hayyacinta, dan ina da karancin kudi ne ma amma sansamu tana da bukatar kulawar likita a halin da kwakwalwarta take ciki yanzu, kamar yadda likitan ya ce, Amma likitan ya ce mu ci gaba da janta a jiki har a samu ta warware ta dawo Normal Sense dinta."
"A Wana gidan za a ci gaba da lallabata har ta dawo normal sense din nata?." Cewar Abba.
Amina shiru ta yi, kafin ta ce "Yaya Abba dan Allah ka yi hakuri ko kwana uku mu bata mu gani. "Hmmmm, Amina kenan, kina Sara baki duba bakin gatari, yanzu dunuyar ce ta canza mutun mugu ne, Amma koma meye inda kin jajibota ya za mu yi dole mu yi hakuri mu bata nan da kwana biyu mu gani." Shi dai Abba bai ce kamai ba, inda yasan mahaifiyarsa ma halinta daya da Aminar, ba iya korarta za ta yi ba. Sai yanzu ma yake ganin laifinsa da ya biye ma Aminar suka dakkota.
Amina ma sanadiyar gajiya da ta yi hakan ya sa tafiya ta yi ta je ta kwanta.
Cancikin dare ihun da Mansura ke yi ya tada ilahirin mutanan gidan daga dogon barcin da suke yi.
Ihu take tana Kiran "Abbana!, wayyo Abbana!!."
Amina da sauri ta rirriketa tana tambayarta lafiya. Ita ko tun karfinta ta dage ta ture Amina tana Mai Kuma Kiran Abbanta da karfinta. Wanda mahaifiyar Mansura shigowarta kenan ta ci karo da ingizar da Mansura ta kaima Amina da ke ƙoƙarin riketa, ana cikin haka ne Abba m ya shigo dakin a rude yana tambayar lafiya.
Amma ganin wadda ke ihun take ransa ya bace. Bai San sanda ya kamo Mansura ba yana girgizata ya ce "Ke! wacece ke da za ki zo cikin daran nan ki hana mutane barci kina Mana ihu cikin dare haka! Ko so kike ki tara Mana mutane ne?."
Mansura ko bata fasa kukan Kiran Abbanta da take yi ba, sai dai yanzu ta rage sautin Kiran bakamar dazun ba. Abba hannu ya daga zai mareta, mahaifiyarsa ta yi sauri ta rike hannunsa ta ce "Kul, karka mareta, baka ga ba cikin hayyacinta take ba, ina jin ma kamar mafarki ta yi."
Abba zafin mahaifiyarsa ta hanasa Marin Mansura ya sauke hannunsa akan fuskar Amina dake tsaye ba zato ta ji mari. Ya ce "Duk ke kika jawo Mana, Kuma Wallahi kin ji na rantse gobe karki yadda in dawo aiki in iske yarinyar nan a gidan nan, idan ba haka ba Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!, Kin ji na rantse Wallahi sai ranki ya yi munmunan ba ci na dawo na isketa a cikin gidan nan ✍🏻
Fadila Sani Bakori ce 🤗
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK
⭐ ABBANA⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar 👇🏻
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Fadeela
*In da rai
*Abdurrahim
*Daga Allah ko d'ora ma Kai
*So ne sila
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi
Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 3-4