← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 36

Sashe 17

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansura tashi ta yi kafin ta mai da kallanta ga Yaya Abba ta ce "Ba zan sake ba."
Mansura na fadin haka ta kama hannun Amina suka tafi, Amina dai da mamaki take kallan Mansura. Cikin sanyi Amina ta ce "Mansura kamar kuka kika yi ko naga idanki da muryarki sun nuna?."
Mansura baki ta murguda ma Amina ta ce "Ai na daina."

"Allah ya sa da na fi kowa murna."

Mansura dai ba ta kula Amina ba.

Amina kalan Mansura ta yi ta ce "Wai yaushe kuka fara magana da Yaya Abba ban Sani ba?."
Mansura kwashe abin da ya faru ta yi kaf ta fada ma Amina.
Mansura zuwa ta yi itama aka shafa mata ragowar hadin dilkar Amarya da ya rage.

Tun daga ranar ya zamana Mansura ta fara sakin ranta a gidan, sosai take ƙoƙarin ganin ta kauta duk wata damuwa dake damunta, dan tana so Amina ta yi hidimar bikinta cikin kwanciyar hankali.

Hatta mahaifiyar Amina sai da ta lura da sauyin Mansura.

Yanzu haka zaune suke an gama yi ma Amina dilka, Amina ta ce "Mansura, na yi shiru na zira miki ido Ina jira in ji kinyi maganar kudin sitin Amma Kuma na ji kin yi shiru."
Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Me ye kudin sitin?." Amina da mamaki ta ce "Wai da gaske baki San meye kudin sitin ba?." Wallahi ban Sani ba."
Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Kila hausarce ta banbanta, ku ya kuke Kiran kudin da ake ba kawayan Amarya na girki ranar daurin aure?."

Murmushi Mansura ta yi ta ce "Tun da nake sau daya na taba zuwa bikin aure, ke nifa duk wani abu da kika san za a yi kawai ki min magana ban San komai ba , ya kamata ki fahimta ma."
Kai Amina ta jinjina ta ce "Gaskiya na ga alama ai, jiya na yi ma Yaya Ahmad maganar kudin sitin ya ce in yi ma Yaya Abba magana, wai duk abin da muke so mutambayi Yaya Abba, sai da na yi mai maganar ma na tuna ashe muna tare da babban abokin anko. Amma Mansura kinsan ni da kunya in ma Yaya Abba maganar kudin sitin, dan haka yau ko gobe ki yi mai, kin ga yau saura kwana hudu gobe uku ya kamata ce mun amsa musan abin da za mu yi."

Mansura ido ta zaro ta ce "Wai ke bakya ganewa ne, Wallahi ban san yadda ake kowata hidima ba ni."
Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Haka fa kawai zakice mai Yaya Abba kudin sitin Kai muka sani abokin anko, idan kika amshi kadan Kuma kin cika sauran."

Mansura ido ta zaro ta ce "Ni dai ki Kira wadda Yaya Abba zai aura mu yi mai magana tare gaskiya, ni Allah ban iya ba."

Amina dungure Mansura ta yi ta ce "Kada Allah ya sa ki iyar babu wata mommy da zan yi ma magana wallahi, wai baki iya ba sai ka ce wani abu ake yi, cemaifa kawai za ki yi kudin sitin shi ai ya san maganar."

Mansura ganin ran Amina kamar ya fara baci ya sa ta yi shiru, ta amsa za ta yi mai magana.

Amina zaune suna hira da Mansura, duk da yawanci hirar Amina take yi, Mansura takan yi ƙoƙarin biye Mata suyi, amma bata taba kawo labari ba ko hira akaran kata, sai dai in an kawo ta yi t comment akai.
Yanzu haka zaune suke suna fira Amina ta ce "Mansura kinsan Allah yanda hidimar nan ta gabato Yaya Abba a busy yake, bari in kirasa mu ji yana ina."

Amina Kiran Abba ta yi a waya, ta ce "Yaya Abba muna ta tsimayinka shiru?." Amina shiru ta yi da alama dai Abba take saurare, kafin ta ce "A'a, Yaya Abba Mansura ke son magana da Kai."

Mansura sai da ta dafe kirji jin Abin da Amina ta ce.

Amina katse Kiran ta yi tana kallan Mansura ta ce "Kin ji ko gara da na kirasa, ya ce ki samai a bangaransa."

Mansura dafe kirji ta yi ta ce "Ni dai Wallahi kin dora min aiki."
Amina hararar Mansura ta yi kafin ta ce "Mansura dan Allah karki amsar Mana kudi kadan."

Mansura turo baki ta yi ta ce ma Amina "Nawa to zance?." 200k zaki ce mai haka aka bamu a auran Maryam."

Mansura shuru ta yi tana zaune sai aikin turo baki take ita kadai. Amina ganin Mansura ba ta da niyyar tashi ta ce "Mansura dan Allah ki je mana Kar ya fita, Kinga kyau gobe a je ayi cefanan komai."

Mansura tashi ta yi tana yafa dankwakin doguwar rigar jikinta ta fita.

Mansura bakinta dauke da sallama ta shiga falon Abba, wanda da ke waya da ango.

Abba jin sallama katse Kiran ya yi bacin ya sanar dashi zai kirasa.

Mansura zama ta yi tana mai gaida Abba, kafin ta dora da cewa "Yaya Abba kudin sitin na zo amsa." Nawa ?." Abba ya tambayeta.
"Two hundred thousands." Abba aje wayarshi ya yi yana kallan Mansura ya ce "Dubu dari biyu ku yi me da su?."
Mansura turi baki ta yi ta ce "Girkin abincin biki Mana." Kai Abba ya jinjina kafin ya ce "Ban account number zan muku transfer One hundred thousand." Yaya Abba Wallahi ya yi kadan, Amina ta ce bikin kawarta da aka yi ba a dade ba 200 aka basu." Shi kenan zan baku 150."

Mansura turo baki ta yi ta ce"Tom Yaya Abba ka cike Mana, Wallahi Amina ta ce Idan bakabada da yawa ba ni zan cika."

Abba Kallan Mansura ya yi ya ce "Idan basu isheku ba zan Kara muku, bani account numberki sai in miki transfer din kudin." Ka yi Mana a na Amina bani da account." Okay." Abba ya ce.

Mansura Kuma tashi ta yi ta fita, cikin sanyin jiki ta koma wajan Amina saboda Abba bai cika masu kudin ba sunkai 200 kamar yadda Amina ta so.

Amina shanjinin jikinta ta yi ganin yadda Mansura ta dawo. Amina kamo hannun Mansura ta yi cikin damuwa ta ce "Kadan ya bamu ko?." Kai Mansura ta daga ta ce "Wallahi na yi na yi ya cika ya Kai 200 ya ki, wai idan basu ishemu ba mu yi mai magana zai Kara Mana."

Amina cikin kosawa ta ce "Wai nawa ya bamu." 150, ya ce zai tura a account dinki." Amina rungume Amina ta yi ta ce "Ni Wallahi na sadakar ma, ban sha zai bamu haka ba, yanzu gobe zan Kira Mommy da Hassana ku je ku yi cefanan tare."

Mansura baki ta turo ta ce "Kinsan nifa bana son hayaniya, su je su kadai."

Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Kar ki so hayaniyar Mana Wallahi da ke za a. Kinga nama manta ince miki ki fada ma Yaya Abba gobe shi zai kaiku siyayar, inda mudai shi muka Sani amatsayin abokin anko shi Yaya Ahmad ya nada ya ce duk abinda muke so mu tambayeshi. Kobai nadashi bama dole ya kaimu inda Yaya Ahmad bashi da aboki sama da shi. Nasan halin Yaya Abba idan muka bari sai gobe zai iya cewa ba za shi ba baisan da maganar ba, dan haka bari in kirasa a waya ki fada Mai."

Mansura turo baki ta yi ta ce "Ke ki fada mai Mana."
Amina hararar Mansura ta yi ta ce "Ai kawaye ke yin irin haka ba Amarya ba, Kuma ma ai da kunya kamar banda kawaye ace ni zan Kira, Wallahi ke zaki Kira, tsabar mama ma tasan ke ce gaba da komai ya sa ta hada gyaran jiki harda ke a matsayinki na babbar kawar Amarya, Kinga ko komai kawa za ta yi kece nan za ki yi sa."
Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Anji din."

Amina Mika ma Mansura wayarta ta yi ta ce "Amsa na kira."

Mansura amsa ta yi tana tura baki. Ringing daya Abba ya daga." Yana cewa dama yanzu zan kiraki in ce ki samin account detail naki."

Mansura tura baki ta yi ta ce"Ba fa ita bace."

Abba shiru ya yi dan ya gane mai maganar. Mansura ma shirun ta yi, Abba jin shiru-shiru ba ta yi magana ba ya kashe wayarsa.

Mansura Mika ma Amina wayar ta ta yi ta ce "Ga shi ya kashe wayar."
Amina cikin jin haushi ta ce "Haba Mansura ba dole ya kashe ba, kin yi shiru ki sake kira."

Mansura sake Kira ta yi sai da ta kusa katswa Abba ya daga.

Mansura kamar yadda Amina ta tsara Mata ta ce "Yaya Abba dama zaka kaimu siyayyane gobe." Abba shiru ya yi, dan sun yi maganar da Ahmad tuni akan shi zai yi jigila dasu akan duk abin da ya kama, sannan Abba ya ce "Ke da wa zaku?." Da mommy da Kuma wata friend din Amina." Ya sunanta?." Abba ya tambaya dan idan har da Aisha ba zai kaisu ba wani zaisa ya kaisu, da yake Abba bai San mommy suke cema Aisha ba.

Mansura Kuma ta ba shi amsa da "Hassana."

Ajiyar zuciya Abba ya sauke jin ba su ambaci Aisha ba. Ya ce "Da misalin karfe nawa zaku tafi." Da yake wayar a speaker take Amina duk tana jin abin da suke cewa, da hannu ta nunama Mansura. Mansura ta ce" 10:00 AM." Okay Allah ya kaimu bana son shiririta ku shirya da wuri." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.

Amina Kuma take ta tura ma Aisha da Hassana massage akan gobe su zo da wuri 10 za su tafi shiyayya, Yaya Abba ne zai kaisu baya son jira."

lokacin Aisha da ta ci karo da sakon Amina sosai ta yi murna jin Abba zai kaisu, take Aisha ta fara shirya kalar kwalliyar da za ta yi tare da tanadan kalmomin masu hikima da basira da za ta yi amfani da su ko Allah zai sa ta ci zuciyar Abba da ya ki.
Chapter 17 · 0% Book details