← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyar Amina kallan baki da hankali ta yi ma Amina kafin ta ce"Amina ke ma lokacin da ta zo gidan ai ba sabawa ta yi da ke ba, sai a hankali-a hankali kuka saba, muma a hankali-a hankali za ta saba da mu daga taga baki." Ni dai gaskiya mama bana son in tafi in barta."

Amina ta fada tana share hawayanta, ita dai duk dan mahaifiyarta ta tausaya Mata ta barta ganin bata son kukanta.

Mahaifiyar Amina ido ta tsura ma Amina ganin tana share waye. Hannu tasa ta goge hawayanta ta ce "A'a abun ai Bai Kai haka ba Amina, kin ga Abba shi ne abokin Ahmad, Kuma lokacin da aka sa auran ba daga kowa ba ne daga Ahmad ne, shi ya bukaci haka, dan haka ki je ki samu Abba ki yi masa magana ya yi ma Ahmad magana a d'aga lokacin auran har zuwa lokacin da Mansura ta samu muji itama✍🏻

Fadila Sani Bakori ce.

https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK

⭐ABBANA⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Daga Marubuciyar 👇🏻

*Fadeela
*Oga Habib
*Meenalyn Daddy
*In da rai
*Abdurrahim
*Daga Allah ko d'ora ma Kai
*So ne sila
*Rayuwar Haidar
*So ne sila

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 9-10

Amina da zummarta ta tashi ta nufi bangaran Abba, zata shiga Abba Kuma zai fito ya yi shirin aiki. Amina cikin girmama yayan nata ta gaidashi ba Kuma kamar yau ba da take naiman alfarma agunsa. Abba amsawa ya yi yana kallan Amina, wadda yanayinta ya nuna tafe take da magana.
Amina kallan Abba ta yi da shima ita yake kallo ta ce"Yaya Abba, dan Allah ka koma ciki za mu yi magana." Abba agogon hannunsa ya kalla ya ce "Amina, lokaci ya ja zan makara aiki, ki bari in nadawo sai mu yi maganar."Tom yayana Allah ya dawo da kai lafiya."

Amina na fadin haka ta juya, da Sauri-sauri itama ta yi breakfast ta tafi aiki.
Ya zamana gidan zai Mansura kadai, wadda duk lokacin da aka barta ita kadai kadaici sosai yake bankado mata rayuwartar. Ba kamar yau ba da gaba daya ta hana kanta sukuni tun da ta ji maganar auran Amina, gani take ba zata iya zama babu Amina ba, dan a iya tunaninta darajar Amina ma ya sa aka barta ta zauna gidan, tom ta ya Kuma za ta cigaba da zama babu Amina.
"Wayyoo Allah na, ya zan yi? Ina zan koma da zama. Ya Allah ka kawo min daukin wannan tsillatsillar rayuwar da nake shirin fadawa. Allah ka iyakamce min haka nan, ba dan halina ba ko abin da na aikata, Allah ka dubeni da idon rahama."

Mansura kuka take sosai na rayuwarta. Mansura tun da ta zo gidan ba ta yi kukan da ta yi yau ba, uwa uba ga damuwar da ta sa ma ranta na auran Amina. Hakan sai ya taru ya yi Mata yawa, Wanda take ya saukar mata da zazzabi.
Kwance take duk ilahirin jikinta rawa yake tsabar zazzabin da take ji, ga gidan babu kowa sai ita kadai. Amina ma da ke banmata wayarta ta bar banmata, saboda ko ta bar Mata ba amfani take da ita ba, hakan ya sa ta bar barmata. Inda dama tana banmata ne dan ta debe mata kewa.

Mahaifiyar Amina Koda ta dawo daga Islamiyar da take zuwa ba ta yi tunanin zuwa duba Mansura ba, in da dama ita ba ma'abociyar zaman falon bace. Hakan ya sa zazzabin ya ci gaba da rukurkusar Mansura, ga amai da take ta famar yi, Wanda hakan ya hadu ya Kara galabartar
da ita.

Amina ba ita ta dawo gidan ba sai 1:30PM kamar yadda ta saba dawowa kusan kullum.

Amina Koda ta dawo da yake hankalinta na kan ta watsa ruwa ta yi Sallah, shi ya sa hankalinta bai kai kan Mansura ba dake kwance tana rawar sanyi.
Amina ba ita ta lura da halin da Mansura take ciki ba har sai da taga Mansurar ta tashi ta ruga bathroom dinsu tana kwara amai.

Amina da idar da sallar ta kenan, tashi ta yi tana kallan Mansura, Wanda Amina sosai ta rude ganin yadda Mansura ta fita hayyacinta. Amina cikin tsoro da yadda ta ga Mansura ta koma ta matsa da sauri tana kamo hannunta ta ce "Mansura, baki da lafiya ne dama ban Sani ba? Kin ga ko yadda kika rame lokaci daya haka."

Mansura dai zame hannunta ta yi daga na Amina ta kwanta ta lillibe saboda sanyi da take ji.
Sosai Mansura ke rawar sanyi.

Amina mahaifiyarta ta je ta samu dake zaune tana tulawar karatun da suka yi, ba yan idar da sallar azahar da ta yi.
Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ta ce Kamar za ta fasa kuka, "Mama, Mansura ba ta da lafiya sosai, bi ki ga yadda ta koma ba."
Mahaifiyar Amina rufe littafin hannunta ta yi tana kallan Amina ta ce "Subahallah, da yake na saba ba fitowa take ba shi ya sa Koda ban ganta ba ban yi tunanin komai ba. Mu je in ganta."

Amina da mahaifiyarta tsaye suka yi kan Mansura da ke tsananin rawar sanyi. Mahaifiyar Amina Koda ta taba jikin Mansura zafi ta ji sosai, hakan ya sa ta Kalli Amina ta ce "Amina, Kira yayanki a waya ki sanar da shi ya zo ya duba jikin nata."

Amina Kiran Abba ta yi, Amma har ta katse bai dauka ba. Amina sai da ta yi ma Abba Kira uku bai dauka ba. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Mama bai dauka b..." Amina bata rufe baki ba Abba ya Kira, yana tambayar Amina lafiya.

Amina cikin damuwa da halin da ta ga Mansura ciki ta ce "Yaya Abba, Mansura ce bata da lafiya tun safe take amai yanzu haka cikin zazzabi take sosai."
Shiru Abba ya yi sannan ya ce "Me ya sa baki fada min ba kafin in fita." Yaya Abba kasan ita Bata magana, tom nima sai yanzu da na dawo na gani, mama, ta ce ka zo ka dubata yanzu."
"Okay." Abba ya ce ya kashe wayarsa.

Mahaifiyar Amina jin shiru-shiru Abba bai zo ba ya sa ta sa Amina ta Kuma Kira Mata Abba. Mahaifiyar Amina da kanta ta yi ma Abba magana akan jikin Mansurar.
Shiru Abba ya yi, kafin ya ce "Mama Wallahi Ina cikin busy, Amma na kusa kammalawa yanzun."

Atakaice Abba, bashi ya zo gidan ba sai 4:00.PM lokacin daga ka ga Mansura kasan ta gama galabaita.

Abba ganin mahaifiyarshi ta daure fuska,alamun ta yi fushi, ya ce "Afuwa Mama, Wallahi ba laifina bane, Ina yarinyar take?"

Amina ita ta yi ma Abba jagora har zuwa bedroom dinsu, dama Abba ya dakko duk abin da ya kamata, ya hado alluransa da drip din da zai sa Mata.

Abba kallan Amina ya yi Wanda duk da bai yi magana ba ta fahimci abin da yake nufi. Hakan ya sa Amina ta hau kan bed din tana bubbuga Mansura ta ce "Dear, ki daure ki tashi ga Yaya Abba nan zai duba ki." Amina ta yi maganar tana yaye rufar da Mansura ta yi.

Jikin Mansura rawa yake tsabar zazzabin dake cinta. Abba zama ya yi bakin gadon yana kallanta ya ce"Bayan zazzabin da kike ji sai me ke miki ciwo?."
"Kaina da cikina." Mansura ta ce a hankali cikin rawar sanyin zazzabi.
"Kina da ulcer ne?." Abba ya tambayeta har yanzu idanshi na a kanta.
Kai Mansura ta daga mai. alamun Eh.

Ruwan Allura Abba ya hada ya mika ma Mansura hannu almaun ta miko mai hannunta, Mansura Kai ta girgiza kamar za ta yi kuka tana kallan Amina, kamar ita ce za ta yi mata allurar, ta ce "Ni dai a ban magani, bana son Allura."
Mansura ta idasa maganar kamar zata fasa kuka. Dan Babu abin da ke daga Mata hankali a ciwo kamar allura, duk da shima maganin ba shanshi take ba. Amma gara Mata magani tana daurewa ta sha.

Amina kallan Abba ta yi cikin sanyi kamar za ta taya kawarta kuka ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka bata magani mana ba sai ka yi Mata allurar ba."
Da yake Amina itama bata son Allura shi ya sa ta fahimci halin da kawarta take ciki.

Abba hanyar fita ya nuna ma Amina da hannunshi alamun ta fita. Hakan ya sa Amina ba tare da ta Kuma cewa uffan ba ta fita.

Abba kuma , mika ma Mansura hannu ya yi alamun ta miko mai hannunta babu alamar wasa.
Mansura yarfe hannunta ta fara kamar za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Allah ka ban magani n..."

Abba jawo hannun Mansura ya yi batare da ya Kara magana ba, da kansa ya nannade hannun rigarta zuwa gwiwar hannunta yana naiman jijiya.

Mansura hannunta gaba daya rawa ya kama gashi tana tsoran musa mai ganin yadda ya daure fuska. Mansura tsabar tsoro hannun rawa ya kama yi sosai, yadda babu yadda za a yi a yi allurar. Abba kallanta ya yi ya ce, "ki natsu ki bar rawa da hannunki, idan ba haka ba aka samu matsala babu ruwana."
Mansura rufe ido ta yi jikinta gaba daya yana rawa, dan wannance ranar farko da wayanta da aka taba yi mata allura, ko za a yi Mata kuka take, mahaifinta Kuma da ya ga haka sai ya ce a rabu da ita a bata magani. Hakan ya sa gaba daya tunanin Mahaifin Mansura sai ya dirar Mata a rai, da ace shi ne da ba zai bari a yi Mata allurar nan ba.

Mansura rufe ido ta yi lokacin da ta ji shigar allurar a jijiyarta.

Abba Kuma ganin yadda take rawa da hannunta ya ce "Wallahi idan kika bari ta kauce sai na sake miki wata garama ki tsaya ruwan ya gama shiga jikinki."

Kusan dai yadda allurar jiji take ruwan na fara shiga zaka ji wani zafi sosai. Mansura na jin zafin nan ta fuske hannunta tana mai fashewa da kuka. Dan gaba daya tunanin mahaifinta sai ya dawo mata a rai ga Kuma zafin allura.

Abba da mamaki yake kallanta, ga ruwan allurar ko rabi bai shiga ba.
Chapter 8 · 0% Book details