Sashe 16
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba Kuma 30k ya ciro ya mika ma Aisha ya ce gashi ki yi manage na ankon Amina." A'a Yaya Abba hidima ta yi yawa dan Allah ka barshi Aisha ta fada cikin jin dadin Abba ya fara sonta.
Abba Amina ya mikamawa ya ce "Amina amsa ki Bata." Aisha ganin haka ta dauka ya yi fushi ne dan taki amsa, hakan ya sa ta amsa daga hannun Abban.
Abba kallan Amina ya yi ya ce "Shigo mu tafi."
Amina shiga ta yi tana jin rashin jin dadin yadda Abba ya yi ma Aisha wanda ita Kuma jin dadi take ganin kamar ya fara sonta.
Amina bayan sun taho tana so ta yi ma Abba magana akan abin da ya yi ma Aisha amma Kuma ba ta ga fuska ba, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru dole, amma sai ya ban halin Aisha take, wanda har ta gama Abba bai tanka mata ba.
Bangaran Aisha ko tana rungume da kudin ta je ta nuna ma mahaifiyarta. Mahaifiyar Abba Kai ta jinjina ta ce "Amma kamar yanzu na ga kin fita, Kuma Aisha ina lura yaron nan ko waya bakwayi anya ko mahaifiyarsa ba tursasa mai auranki ta yi ba?."
Aisha Kai ta girgiza ta ce "A'a mama muna chat sosai a WhatsApp, yanayin aikinsa ne ya sa kika ga baizuwa." Mahaifiyar Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Oh ai ban san kuna chat ba."Mahaifiyar Aisha na fadin haka ta juya ta tafi.
Aisha Kuma wayarta ta dakko ta fara rubuta ma Abba sako kamar haka "Habibatina na gode sosai ta kulawarka agareni, zan dade ban manta ba."
Abba Koda ya ga sakon tsaki ya yi ya goge text din.
Yau mahaifiyar Amina ta dakko Mai gyaran jikin da zata fara yi ma Amina gyaran jiki da Mansura kawar Amarya. Mansura kallan Amina ta yi bayan mahaifiyar Amina ta tafi jin ance har da ita ta ce "Amina dan Allah bana so kima Mama magana." Mai gyaran jikin da keta kallan Mansura ta ce ma Amina "Ni ko kamar na San wannan?." Ta fada tana nuna Mansura.
Mansura Kai ta dako a gigice tana kallan mai gyaran jiki, jikinta har ya fara rawa. Amina Kuma da fata lura da halin da Mansura ta shiga ba ta ce "Eh ai haka ne kila maikama da ita kika Sani."
Mai gyaran jikin kallan Mansura ta yi ta ce "Ke ko za a yi biki gidanku ki ce ba kyason gyaran jiki, Koda yake kila dan Kinga kina da kyau ne, amma da za ki yi kyanki zai Kara fita sosai.
Mansura dai mai gyaran jikin gaba daya ta rudata furta kalmar kamar ta Santa da ta yi, hakan ya sa ba tare da ta ce mata komai ba ta tashi ta fita.
Can cikin gidan Mansura ta fi je tana ta kuka, kuka take kamar wadda aka aikoma sakon mutuwar iyayanta. Kuka take tana mai cewa "Allah ka takaita min wannan razanannan rayuwar da nake yi, Allah ka kawo min dauki acikinta, Allah idan har rayuwata ba ta da alkairi cikin jama'a Allah ka dauki rayuwata. Kuka Mansura take yi sosai tana bubbuga kafarta.
Abba da cikin barci yake jiyo kukan mace, Wanda har ya yi nasarar tadashi daga dogon barcin da yake yi. Abba dafe Kai ya yi kafin ya tashi ya zauna yana mamakin wake kuka haka.
Abba tashi ya yi ya saka jallabiyarsa ya ya zo wajan window sa, da mamaki ya bi Mansura da kallo ganin yadda take kuka, daga gani tana cikin tsananin damuwa da tashin hankali. ga uwar rama da ta yi dama tun da bikin Amina ya gabato kulum cikin damuwar yadda za ta ci gaba da zama gidan ita kadai take yi babu Amina.
Abba ya dade yana kallan Mansura da babu alamun zata yi shiru daga kukan da take yi, fita ya yi ya je ya sameta. Abba tsaye ya yi kan Mansura da ko'alamar tsayuwarsa bata ji ba balle ta ji tafiyarsa. Abba tsugunnawa ya yi kusa Mansura yana dago kanta da ta tusa tsakankanin cinyoyinta✍🏻
Fadila Sani Bakori ce.
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar
*Fadeela
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Abdurrahim
*In da rai
*Daga Allah ko d'ora ma Kai
*So ne sila
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
Page 19-20
Mansura dago jajayan idanunta ta yi ta saukesu kan Abba, Abba ya dade yana kallan Mansura kafin ya kamo hannunta, Mansura da kallo ta bi Abba, Abba na rike da hannun Mansura har zuwa madaidaicin falonsa ya yi ma Mansura masauki. Kallan Mansura ya yi da har yanzu ba ta fasa share hawayanta ba. Abba kan lover chair din falonta ya nuna ma Mansura da hannu ya ce "Zauna." Mansura zama ta yi tana mai goge hawayanta. Abba zama ya yi gefan Mansura kamo hannuwan Mansura ya yi guda biyu duka ya rike yana kallanta, Wanda Mansura ta sidda kanta kasa tana mai ci gaba da zubba hawayanta. Abba cikin sanyi ya ce "Idan har kina min kallan da Amina take min kin daukeni dan'uwanki tom ki fada min damuwarki?."
Mansura kasa ta yi da kanta har yanzu hawayan dake zuba idanunta basu tsaya ba.
Abba hannu ya sa ya dako kan Mansura ya ce "Ina jinki fada min me kike yi ma kuka?."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Ina kukan rabuwa da Amina ne, inatunanin yadda zan yi rayuwa ni kadai a gidannan babu ita."
Kai Abba ya girgiza ya ce "Karki yi min karya, kukanki bashi da alaka da auran Amina, amma zan iya yadda idan kikace auran Amina ya fama miki raunin dake zuciyarki, dan kukanki ya fi kama da na wanda aka fama ma wani rauni, zuwa yanzu ya kamata ace kin bar mana boye-boye, kin fada Mana gaskiyar abin da ke damunki, ni Kuma na yi miki alkawarin taimakonki akan duk halin da kikeci."
Mansura shuru ta yi bata ce komai ba, Kuma ta tsaya da kukan da take yi. Abba jin ta yi shiru tana kallansa, ya ce "Ina jinki, meye damuwarki? Meke yawan saki kukan nan da kike yi?."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce "Yaya Abba da Ina da wata damuwa da nasar da Amina tuni, saboda bacin Fatima kawata ban taba shaguwa da wani ba adduniya kamar Amina, Yaya Abba da ina da wata damuwa da na sanar da ita."
Abba shiru ya yi yana nazarin kalaman Mansura da babu kamshi gaskiya kodaya a cikinsu, amma sai ya shareta ya ce "Ina ita Fatimar take?." Bakaramin tashin hankali Mansura ta shiga ba dalilin wannan tambaya da Abba ya yi Mata, hatta Abba ya fahimci halin da Mansura ta shiga sanadiyar wannan tambaya tashi.
Abba ganin ta yi shiru sai hawaye dake ta gudana a fuskarta kamar an bude famfo.
Abba cikin sanyi ya Kuma cewa "Ko itama Fatimar ta mutu n..."
Abba bai karasa sanadiyar kukan da Mansura ta fashe dashi tana cewa "Wayyo Abbana Fatima, Wayyoo Fatima, ina kike Ina jin kunyarki bana iya hada ido dake wayyo Abbana me ya sa? Me ya sa..?."
Abba dai ya zira mata ido yana kallanta yana Kuma jin furucin dake fita daga bakinta.
Mansura Kuma zumbur ta yi ta tashi kamar wata zautatta har yanzu tana kiran sunan Fatima.
Abba hannun Mansura ya kamo ganin kamar bama cikin hayyacinta take ba, ga uban kuka da take famar rushawa tana Kiran Fatima.
Abba hannun Mansura ya rika murzawa yana cewa "Shi kenan ki yi hakuri ya isa haka." Handkerchief dinsa ya ciro ya mika ma Mansura, wadda ta ci kuka harda majina.
Mansura kallan handkerchief din ta yi taki amsa. Abba cikin sanyi ya ce "Ki amsa ki goge hawayanki."
Mansura amsa ta yi ta gode hawayanta tana jan ajiyar zuciya na irin wanda ya sha kuka sosai.
Ana cikin haka ne wayar Abba ta hau ringing. Abba dagawa ya yi yana kanga wayar a kunnansa.
Cancikin gidansu Amina, Amina hankalinta tashi ya yi sosai ganin ta duba ko Ina babu Mansura babu alamarta, hakan ya sa Amina ta fara kuka gashi ita kadaice a gidan sai mai yi mata gyaran jiki, Amina ganin kukan ba zai yi mata bane ya sa ta kira Abba ta fada mai bata ga Mansura ba cikin kuka.
Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu bata bar share hawayanta ba ya ce "Gata a bangarena ki zo ku tafi tare." Abba na fadin haka ya kashe wayar.
Amina Kuma sosai mamaki ya kamata me ya Kai Mansura bangaran Yaya Abba.
Abba Kuma bayan ya kashe wayar kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura."
Mansura da mamaki ta dako tana kallan Abba, dan ganin ba shiga safgarta yake ba ta yi tunanin ma yasan sunanta ba.
Mansura cikin sanyi irin muryar Wanda ya gaji da kuka ta ce "Na'am." Kina son Amina?." Abba ya tambayi Mansura yana kallanta.
Mansura turo baki ta yi ba ta ba Abba amsa ba.
Abba murmushi ya yi kafin ya ce "Yau saura sati daya auran Amina, me za ki bata gudunmuwa?."
Mansura kuma turo bakinta ta yi, can ciki ta ce "Ni ai banda kudi."
Kai Abba ya jinjina dama amsar da yake so kenan daga bakinta ya ce "Inda baki da kudi yanzu abin da ya kamata ki bata wanda ba zata manta dake ba shine farinciki, farincikin nan ko zaki ba Amina shine ta hanyar kauda duk wata damuwa da ta dameki ki ajeta gefa har ayi baki a gama, saboda Amina tana dariya ne da dariyarki, idan kikace zaki ci gaba da kunci ko kuka Amina ba zata yi hidimar auranta cikin walwala ba, amma idan ta ga kin saki ranki kina mu'amularki kamar yadda kowa yake yi, itama zata gudanar da hidimar auranta ranta sake. Ina fatan zaki min haka? Daga nan har a daura auran Amina ba zaki Kara kuka ba ko wani damuwa d...." Daidai nan Amina ta yi sallama ta shigo cike da mamakin yaushe Yaya Abba da Amina suka Saba haka.