← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Mansura da Amina suka ba mutane tausayi, dan da yawansu sun san babu dadi irin rabuwar nan.
Abba cikin lallashin Mansura ya ce "Ki yi hakuri ba za a jima ba zan kawo ki wajanta.". Abba na rike da Mansura dake rusa kuka a haka har suka karasa wajan motasa ya bude Mata ta shiga kafin ya zagaya ya shiga suka tafi. Sun yi nisa da tafiya har lokacin Mansura bata bar kuka ba.

Su Aunty Zainab ne sukaita bata baki a haka suka samu ta hakura ta yi shiru.

Da yake Basu fito garin da wuri ba hakan ya sa gaf La'asar suka shiga garin Katsina.

Suna zuwa Mansura da tun a hanya kantake Mata ciwo na kukan da ta yi suna shiga ta ruga bangaransu da sauri tana kuka, mahaifiyar Mansura Kai ta girgiza ta ce "Dama ni nasan ai za a yi haka." Uhmm, mama danma baki ga yadda aka rabasu da Amina ba, Kinga yadda suka rike juna da kyar aka rabasu, Aminar ma can muka barota tana aikin kukan." Cewar Aunty Zainab.
Kai Mahaifiyar Amina ta jinjina ta ce "Ni dama nasan za a yi haka." Haka dai Aunty Zainab taita ba mahaifiyar Amina labarin tarbar arziki da dangin Ahmad din suka yi masu, Aunty Zainab ta ce "Gaskiya mama Amina ta yi sa'ar dangi miji idan har zasu dore da abinda muka gani, sai dai mu yi mata fatan zaman lafiya Kuma."

Mahaifiyar Amina sosai ta ji dadin maganar da Aunty Zainab ta yi hakan ya sa ta ce "Tom Allah ya daurar da kauna a tsakaninta da su da Kuma Ahmad din baki daya. Allah dai ya sa kun Kara jamata kunne da zaku taho duk da Amina bata da matsala." Ai mama Amina ko fada suka yi da Ahmad ni zan iya cewa laifinsa ne, yarinyar da batasan fushi ba, ba ta dauki rayuwar duniya komai ba ai Kar ki ji komai mama indai akan Amina ne."
Lumshe ido Mahaifiyar Amina ta yi, tsabar jin dadin yabar Aminarta da Aunty Zainab ta yi ta ce "Tom Zainab ina rokan Allah Allah ya sa Amina ta ci gaba da tafiya kamar yadda muka Santa karta canza". Ameen mama."

Aunty Zainab sun dade suna hira da mahaifiyarta.

Bangaran Mansura ko Aunty Zainab ganin har an yi magariba Mansura bata fito ba hakan ya sa Aunty Zainab ta shiga wajan Mansurar da tea a hannunta,. Zaune ta iske Mansurar kan abin Sallah da alama bata jima da idar da Sallah ba, ta yi shiru ta yi ta gumi daga ganinta ta yi nisa a duniyar tunani. Aunty Zainab zama ta yi tasa hannunta daya ta cire tagumin da Mansura ta yi. Sai yanzu Mansura ta dago tana kallan Aunty Zainab. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi ta ce "Dauki tea din kisha ga biscuits naga alama kema Amina ta koya miki shan tea da biscuit."
Mansura yake ta yi ma Aunty Zainab kafin ta dauki tea din tana sha kadan-kadan a haka ta shanye.
Aunty Zainab kallanta ta yi ta ce "In kawo miki tuwo Kinga tun safe rabonki da abinci." Mansura Kai ta girgiza ta ce "Na koshi."
Jinjina Kai Aunty Zainab ta yi ta yi shiru tana kallan Mansura kafin ta ce "Mansura dan Allah karki sama ranki damuwar rashin Amina, haka dama ita rayuwar 'yamace ta gada, kema watarana haka zamu kaiki mu baroki Kuma dole zamu yi hakuri, daga kin yi hakuri a hankali za ki Saba, zan yima Yaya Abba magana kema ya Samar maki ko teaching dinne ya rage miki zaman kadaici."

Aunty Zainab ta dade tana ma Mansura nasiha kafin ta fita ta barta.

Aunty Zainab na fita Kiran Amina Amarya ya shigo wayar da tabar ma Mansura. Mansura bin wayar ta yi da kallo ganin sunan dake jikin layin my bea, Mansura daga Kiran ta yi ta ce "Lafiya Lau muka iso, ya muka barki?." Shiru Mansura ta yi da alamar Amina take saurare kafin ta ce "Tom ma Sha Allah ki gaida min Yaya Ahmad din."

Bayan Amina ta kashe wayar Mansura tashi ta yi ta tada sallar issha'i, tana idarwa ta kwanta, tana kwantawa ko barci ya kwasheta.

Bangaran Abba kasan cewar yasan wayar Amina na hannun Mansura ta bar Mata, hakan ya sa bayan ya yi shirin kwanciya ya Kira layin Amina dan yasan in ba sa'a ba Mansura nacan na kuka, saidai ya yi Kira harta katse ba a daga ba, sake Kira ya yi nanma haka, sai da ya yi ma Mansura Kira 5 Bata daga ba, kafin ya hakura ya kwanta yana tunanin kila ta yi barci ne.

Washagari da wuri yan biki aka fara watsewa, zuwa a zahar ya zamana gidan babu kowa duk sungama tafiya sai Aunty Zainab kadai, itama mijinta anayin magariba ya zo ya dauketa suka tafi ya zamana sai Mama da Mansura kadai a gidan.

Mansura ko washagari kota kan wayarta bata biba dan ta farka da ciwan Kai dan har sai da Aunty Zainab ta sa aka siyo Mata Panadol. Hakan ya sa kusan kwance ta wuni.

Abba Kuma da yake yana wajan aiki hakan ya sa ya shiga busy sai dare ya dawo gidan, kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama taro ya tashi kenan." Bari Abbana, taro ya tashi lafiya ma sha Allah." Abba sun jima suna hira da mahaifiyarsa har ya ci abinci Amma baiga fitowar Mansura ba, hakan ya sa ya ce "Mama na ganki ke ka dai Ina yarinyar nan fa?." Mansura, tana can kila kwance, ni banta ba ganin Wanda baya gajiya da kwanciya ba kamar yarinyar nan." Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Wai mama kina nufin duk yau kwance ta wuni ko falon nan bata fito ba?." A'a, ta fito lokacin da Zainab zata tafi."

Abba shiru ya yi baice komai ba, kafin ya tashi ya fita, yana fita ya Kira number Mansura, harta katse bata daga ba, sake Kira ya yi nan ma shiru ba a ta yi picking ba. Abba tafiya ya yi yana tunanin dalilin kin daga Kiransa da Mansura ta yi. Abin da ko baisani ba Mansura bata kusa ta shiga wanka.

Bangaran Aisha sosai take cikin damuwar rashin ganin Kiran Abba a wayarta, hakan ya Kara tabbatar mata Abba ba ta ita yake ba, dan a ganinta ko yadda ta bar wajan party ya kamata ace ya kirata ya tambayi lafiyarta, haka Kuma Bata je Kai Amarya ba nanma a ganinta ya kamata ya Kira ya ji dalilin rashin zuwan nata, Amma shiru, hakan ya sa ta yanke ma kanta shawarar hakura da Abba, Amma Kuma ta sanar da mahaifiyarta ta ce bata isa ba, hakan ya sa Aisha ta kudiri aniyar sanar da mahaifiyar Abba, dan bata jin zata iya auran Wanda baya sonta. Aisha text ta tura ma mahaifiyar Abba kamar haka. "Assalamu alaikum, mama Ina wuni, ta fatan an tashi taro lafiya. Mama dan Allah kisa baki nasan Malama zata ji maganarki, na fasa auran Yaya Abba, na fada ma Malama taki yadda."

Mahaifiyar Amina ba ita taga sakon Aisha ba sai da ta idata idar da sallar asuba. Sosai sakon furucin Aisha ya data Mata hankali, hakan ya sa ta kira Aisha a waya, mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Aisha yanzu naga sakonki, ko zaki fadamin dalilinki?."
Aisha cikin sanyi ta ce "Mama Wallahi Yaya Abba baya Sona zai aureni ne kawai bisa umarninki."
Shiru mahaifiyar Amina ta yi dan tarasa abin da zatace, hakan ya sa ta yi shiru ta ce "Shi kenan Aisha zan kiraki."

Bangaran Abba ko duk ya kasa sukuni na rashin samun Mansura a waya da ya yi. Kamar yadda ya saba idan ya yi shirin tafiya aiki yana zuwa su gaisa da mahaifiyarsa.

Yau Abba Koda ya shigo ya gaida mahaifiyarsa bata kallesa ba bare ta amsa mai. Abba shiru ya yi yana kallan mahaifiyarsa. Mahaifiyar Abba wayarta dake kusa da ita ta mikama Abba.

Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa ...✍🏻

Littafin ABBANA na kudi ne, 400 kafin in gama free pages daga na gammala zai koma 500 my number 08063830828

Fadila Sani Bakori ce.

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 33-34

Abba amsa ya yi ya karanta sakon Aisha, bayan ya gama karanta text din dagowa ya yi yana kallan mahaifiyarsa.
Mahaifiyar Abba cikin damuwa ta ce "Abba abinda zaka sakamin dashi kenan? Dawana ido kakeso in kalli Malama? Na baka nan da kwana biyu ka yi gaggawar daidaita tsakaninka da Aisha ta yanje kudirinta.

Abba shiru ya yi kafin ya ce "In Sha Allah mama." Yana fadin haka ya tashi ya fita, Yana fita ya Kira number Mansura nanma bata daga ba, abin tsoro ya ba Abba gashi ya kasa tambayar mahaifiyarsa Mansura ganin yadda suke. Abba kallan bedroom din da Mansura da take ciki ya yi, tafiya ya yi ya tura kofar dakin Mansurar, Allah ya taimakesa kofar babu key a jiki ya tura ya shiga. Abba kallan Mansura ya yi da ta lillibe ilahirin jikinta da bargo, Abba tsaye ya yi yana kallanta, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya matsa wajan gadon, bubbuga kafar Mansura ya yi, Mansura cikin barci ta ji ana taba mata kafa, Mansura bude ido ta yi tana kallan Abba dake tsaye akanta.

Mansura tashi ta yi tana mutsika ido, tana kallan Abba.

Abba cikin sanyi ya ce "Kin yi sallah?." Kai Mansura ta girgiza alamun A'a.
"Tashi ki je ki yi Sallah."

Mansura sauka ta yi kan gadon ta shige bathroom da sauri, babu jimawa ta yi alwal ta fito ta zo ta tada Sallah.

Abba zama ya yi bakin bed din yana jiran ta idar da sallar.
Chapter 27 · 0% Book details