Sashe 20
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahaifiyar Abba rasa abin da zata ce ta yi dan ita ko magana banda ranar da Mansura ta zo gidan ba ta taba ganin ta hada Mansura da Abba ba, hasalima in ba yanzu ba Abba ba son zaman Mansura a gidan yake ba. Mahaifiyar Amina mai da kallanta ga Hassana ta yi ta ce "Tom waiku me kuka gani da za ku ce haka? Sannan yanzu meye dalikin kukan nata?."
Hassana da ta rasa abin da zatace dan duk surutun Hassana bata da fiye karya ba hakan ya sa ta ce "Mama ki dai tambayi Aishar da bakinta ta fada miki." Mahaifiyar Amina hannun Aisha ta gama ta ce "Tashi mu je ki fada min in ji." Mahaifiyar Amina na rike da hannun Aisha har bedroom dinta, zaunar da ita ta yi kan one hand char din dake bedroom dinta, itama ta zauna, goge ma Aisha hawayanta ta fara yi kafin cikin taushin murya ta ce "Shi kenan kukan ya Isa haka nan, fada min shi Abban ne ya ce miki yana son Mansura?." Kai Aisha ta girgiza.
Shiru mahaifiyar Amina ta yi kafin ta ce " Aisha ki natsu ki sanar dani kin ji zan yi maganin koma meye, Abba bai isa ba ko bayan raina ya wulakantaki ba bare Kuma da raina, fada min ya aka yi?."
Aisha rasa abin da zata ce ma mahaifiyar Abba ta yi, hakan ya sa ta ce "Mama dan Allah ki tambayi Hassana tasan komai Kuma agabanta komai ya faru." Mahaifiyar Amina wayar Amina ta Kira ta ce ta turo mata Hassana.
Hassana koda ta fito falon ba ta ga Mahaifiyar Amina ba, bedroom din mahaifiyar Amina ta shiga da sallamarta.
Mahaifiyar Amina waje ta nuna ma Hassana ta ce "Zauna." Bayan ta zauna mahaifiyar Amina ta ce "Hassana na tambayi Aisha ta ce in tambayeki agabanki komai ya faru, Ina jinki fadamin meya faru bayan tafiyarku?
Hassana Kara gyara zama ta yi kafin ta ce "Mama Kinga Koda muka tafi muka je zamu kasuwa siyayya Mansura kin fita daga motar Yaya Abba ta yi wai bata jin dadi, amma da muka dawo muka iskesu waje daya da Yaya Abba sai fira suke har tana dariya. Yanzu Kuma bayan mun dawo Yaya Abba ya ce mu shigo da kayan da muka dawo dasu, duk maka dako muka taho ita Kuma har ta taho Yaya Abba ya kirata wai ta dawo ta dauki Abba, Wallahi mama Koda muka juyo abinda Aisha ta gani shi ya sata kuka."
Mahaifiyar Amina cikin sanyi ta ce "Me kuka gani da kuka jiyo din." Gani muka yi Yaya Abba yana rike da hannunta suna magana suna dariya."
Ajiyar azuciya mahaifiyar Amina ta sauke. Shiru ta yi dan ta rasa abinda zata ce, sai zuwa can ta ce "Ki kwantar da hankalinki kin ji yayata, Abba bashi da Mata saike, Mansura Kuma duk abin da kika gani ya faru tsakaninta da Abba ki dauka kamar da Amina kika gani, dan Abba kallan kanwa yake Mata, Kar ki kuma sakanki damuwa indai akan haka ne Abba ba soyayya suke da Mansura ba kamar yadda kuka zarga."
Aisha sosai ta gamsu da kalaman surukartata, hakan ya sa ce "Tom Mommy nagode Kuma in sha Allah ba zan sake sa kaina damuwa akan hakan ba." Yauwa 'yar Albarka Allah ya yi Miki albarka." Ameen Aisha ta ce kafin suka fita suka bar Mahaifiyar Abba dariyarsu, suna fita Abba yana shigowa dan har saida suka matsa mai ma. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama Wana albishir din akai miki ne naga kina dariya." Hmmm Abba dole in yi dariya, Aisha ta zo ta dagamin hankali tana kuka wai soyaya kake da Mansura, Koda na tambayi ba asin maganar tasu duk kame-kame ce, daga ji dai kishi take na magana da Mansura da ka yi."
Abba daure fuska ya yi ya ce "Lallai Kam aiki ya sameta." Mahaifiyar Abba gimtse dariyarta ta yi ta ce "Bana son shirme kamar ya aiki ya sameta? Kenan yanzu ka fara magana da Yan Mata a gabanta? Ko me kake nufi?." Abba kai ya girgiza ya ce "Kodaya ba haka nake nufi ba, Amma mama indai dan taga Ina magana da yarinyar can ne ai abin yaban mamaki, tom wata magana muka yi da har zai sa ta ce Haka." Kai rabu dasu shirmansu ne kawai. Dama Abba ina ta so in maka wata magana sai in mata, ka ga dai anci wata kusan biyu kenan da sa ranarka da Aisha, Kuma ni har yanzu banji wata magana da ka yi ba ta shirin biki da kake yi, ko maganar gininka ma ban ji kana maganar karasashi ba."
Abba Kai ya sosa ya ce "Ko jiya mun yi magana da masu aikin, Ina so sai mun gama hidimar bikin nan ne kafin in dora aikin ba tsayawa." Tom Allah ya taimaka." Ameen." Abba ya ce. Sun dade suna tattaunawa da mahaifiyarsa kafin ya fita.
Can bangaran su Amina ko bayan Mahaifiyar Amina ta Kira Hassana, ya rake daga Amina sai Mansura a dakin. Amina kallan Mansura ta yi cikin sanyi ta ce "Mansura wai meke faruwa ne?." Mansura fara goge hawayan da ya zibo Mata ta yi ta ce "Wallahi nima ban Sani ba, da na shigo ne na iske Mommy tana kuka, har zan tambayi lafiya na ji friend dinki na cewa wai na yi ma Mommy snatching din saurayi, wai Ina soyayya da Yaya Abba."
Amina shiru ta yi ta rasa abin cewa, kafin ta ce "Tom yanzu Kuma meye abin kuka anan, ni abinda nake so in Sani me ya faru a tafiyar takune."
Mansura kwashe duk abin da ya faru ta yi ta fada ma Amina. Amina shiru ta yi ta ce "Ki yi hakuri Mansura dan Allah karki dauki aka a matsayin wani abu nasan watarana zaki fahimci halin da Aisha ta shiga dazu, son Yaya Abba take sosai tattare da tsananin kishi akansa, shi yasa ta ji haushin barinku tare gani take Kun yi wata maganar ne, kinsan masoyi yana da zargi." Amina dai har ta gama maganarta Mansura bata ce komai ba. Suna ana haka Hassana da Aisha suka shigo. Shiru babu Wanda ya ce ma kowa komai, Amina ce ta katse shirun da cewa "Hassana Kun gama shigo da kayan ne?." Kai Hassana ta girgiza "Shi kenan ku bari na samu wani yaran ya shigo dasu."
Aisha tashi ta yi tana kallan Amina ta ce "Amina zan tafi sai Kuma ranar daurin aure." Amina marairaice fuska ta yi ta ce "Na zaci kullum zaku rika zuwa nan mu wuni tare dan Allah."
Aisha dai bata ce komai ba murmushi ta yi ta tafi. Hassana ma tashi ta yi ta ce "Nima ai tafiya zan yi jirani." Hassana tashi ta yi suka tafi tare da Aisha. Amina tashi ta yi ta rakasu har wajan get dinsu, bayan sun fitone Amina ta kalli Aisha ta ce "Mommy dan Allah ki yi hakuri abinda ya faru, amma a ainihin sanina Yaya Abba ko magana ba hadasu da Mansura, dan Allah ki yi hakuri zan mata magana." Aisha murmushi ta yi ma Mansura ta ce "Ayyah babu komai ya wuce ai."
Bayan sun Hassana sun tafi Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha kinsan Allah ki ci gaba da sa ido akan yarinyar nan, dan ni ban yadda basa soyayya da Yaya Abba, na fi tunanin dai ko su ne Basu son suna soyayyar ba."
Aisha dai ba ta ce komai, ta yi ma Hassana sallama ta tari Napep ta hau. Aisha ta tafi babu jimawa mahaifiyarta ta zo gidansu Amina.
Mahaifiyar Amina da fara'arta ta tari malamarta, bayan sun gaggaisa Mahaifiyar Amina take sanar da mahaifiyar Aisha, Aisha ma yanzu suka tafi babu jimawa.
Malama kallan mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Tun jiya nake cewa zanzo Allah bai yi ba, dama na zo in sanar dake ne na shirya Walima da za mu yi ta bikin Amina a gidan nan, shi ne na ce yaushe za a yi gobe ko sai ana gobe darin aure?."
Mahaifiyar Amina da murnarta ta ce "Kai Malama, wannan babar hidima haka, tom angode Allah ya saka da alkairi, a bari a yi jibi ana gobe biki kenan." Shi kenan Allah ya kaimu.
Malama sun dade suna fira da mahaifiyar Amina kafin ta yi mata sallama ta tafi.
Mansura ranar gaba daya haka ta wuni babu dadi dan tashiga damuwar abin da su Aisha suka yi Mata, ta dauki hakan kamar cikin mutunci ne.
Washagari Abokan Ahmad suka kawo lefan Amina.
'Yan'uwansu Amina da dama duk sun zo, hakan ya sa gidan yanzu ya fara cika, dole ya sa Abba ya bar masu bangaransa ya koma dakin abokinsa da kwana.
Bangaran mahaifiyar Aisha Kuma tana ta shirin shirya masu walimar da za ta yi ta a bikin Amina a matsayin gudummuwarta.
Mansura sosai take cikin damuwar rabuwa da Amina Amma ta daure dan karta rusa farincikin da Amina take ciki.
Koda mai lalle ta zo yi masu Mansura kamar ta ce bata so amma tana tsoran maganar mutane hakan ya sa ta zauna aka ranga da Mata kunshinta. Ana yin kunshin Amina ta ce ma maikunshin "Ki yi Mata mai kyau fa kamar nawa itace babbar kawar Amarya." Hakan ya sa mai kunshin da zana ma Mansura filawa mai kyau. Da yake duk sun sha dilka hakan ya sa kyan kunshin ya Kara fita sosai.
Washagari aka kafa manyan rumfuna a harabar gidansu Amina. Mahaifiyar Amina da Amina duk sunyi gayyatar walimar, haka mahaifiyar Aisha ma ta gayyaci duk dalibanta walimar, hakan ya sa walimar ta samu halartar mutane da yawa.
Amarya Amina wanka ta yi ta cakare cikin wata farar lifaya, sosai ta yi kyau daga kaganta babu tambaya ka ga Amarya, duk wanda ya zo gidan sai ya yaba kyan da Amina ta yi.