Sashe 33
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba bayan ya koma bangaransa wanka ya yi ya sa jallabiyarsa kafin ya Kira wajan aiki ya kawo uzirinsa.
Mahaifiyar Abba bayan ta dawo gidan Kiran Abba ta yi ta sanar mai ta dawo, Abba ma cikin karyar da ya koyo yau dinnan ya ce "Mama gani nima yanzu zan shigo gidan."
Abba bayan ya gama kimtsawa ya nufo falon mahaifiyarsa inda ya isketa zaune da ledar magungunan. Abba zama ya yi ya gaida mahaifiyarsa tare da cewa "Yau Asibiti aka kirani da wuri na yi fitar safe shi ya sa ban samu shigowa ba." Haba, ni dama yau na jika shiru baka shigoba ina jimamin ko lafiya, sai na tuna Mansura ma ban ji duriyarta ba duk yau, shi ne fa na je dakinta ashe kwance take ba lafiya ban sani ba."
Kai Abba ya sosai ya ce "Ayyah, meke damunta?." Muje ka gani." Cewar mahaifiyar Abba tana tashi suka nufi bedroom din Mansurar tare da Abba.
Har yanzu Mansura tana kwance ta rufe baki daya jikinta.
Abba dake tsaye kan Mansurar hannu yasa zai yaye bargon Mansurar, mahaifiyarsa ta rike hannunsa ta ce "Ni fa dadina daku likitoci kamar ba kusan addini ba wasinku, sai ku bage da ai lallurace, yanzu da kake ƙoƙarin yaye mata bargo in fa ba komai jikinta."
Abba Kai ya sosa baice komai ba, kafin ya ce "Tom mama ya zan dubata?."
Mahaifiyar Abba da wayau ta fara duba Mansura ganin akwai kaya complete a jikinta ya sa ta ja bargon Mansurar ta ce "Tom Bismillah."
Abba hannu ya Kai ya taba jikin Mansura, jin babu zafi sosai ya sa ya ce yana kallan Mansura da idanta yake a rufe ya ce "Har yanzu kan na yi miki ciwo?."
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi tana murmushi ta ce "Ka ce Kasan ma bata da lafiya?."
Abba lura da subutar bakin da ya yi kai ya girgiza ya ce "A'a yanayin temperature din ajikinta ne ya nuna ta yi ciwan Kai." Owo, ai fa dadina daku kamar mayu kuke." Cewar mahaifiyar Abba.
Abba dai baice komai ba. Allura ya ciro ya hada yana kallan Mansura ya ce "Ki juyo zan miki allura."
Abin mamaki duk rakin Mansura a allura juyowa ta yi bata yi musu ba Abba ya yi mata allurar.
Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Allurar ma kyau ace ta karya aka yi, Mama ko tea a kawo mata tasha sai tasha maganin."
Mahaifiyar Abba juyawa ta yi ta fita ta je hado ma Mansura tea din.
Bayan ta fita ne Abba ya ce "Am sorry Mansura, ya jikin naki, da fatan dai bayan kan babu abin da yake miki ciwo?."
Mansura kai ta daga ma Abba bata ce komai ba. Abba kuma cikin marairecewa ya ce "Idan Mama ta shigo ki ce Mata ta yi tafiyarta islamiyarya kin ji sauki, sai in yi jinyarki da kaina."
Kai Mansura ta daga ma Abba.
Mahaifiyar Abba babu jimawa ta hado ma Mansura tea tare da soyayyar doya ta kawo Mata, tea dinma da kyar Abba ya samu tasha ya bata magungunan duk ta sha babu musu. Abba jin Mansura ba ta yi ma mahaifiyarsa maganar tafiya Islamiya ba da ya ce ta yi ya sa shi ya ce "Mama karfa ki ce ba zaki je Islamiya ba saboda ciwan, inda anyi mata allura Kuma ta sha magani yanzu zaki ga ta ji sauki."
Kai mahaifiyar Abba ta girgiza ta ce "A'a gaskiya koma na tafi hankalina ba zai kwanta ba, gara dai in naga tabbacin saukin nata zuwa gobe sai in je."
Abba baice komai ba ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Allah ya bata lafiya na tafi aiki." Yana fadin haka ya tafi baiso ba yaso ace shi ya yi jinyar Mansurar.
Abba yana gaf dawowa gida ya Kira Mansura ya ji ya jikinta da yake lokacin suna tare da mahaifiyar Abba ya sa bata daga Kiran ba.
Abba 6:00PM ya shigo gidan rike da ledoji biyu a hannunta, zaune ya iske mahaifiyarsa tana yanka alayyahu. Abba zama ya yi yana mata sannu da aiki, kafin ya ce "Ya mai jikin mama?." Ta ji sauki, amma dai duk yau bata shigo falon nan ba."
Abba ledar hannunsa ya mika ma mahaifiyarsa daya ya ce yana tashi "Bari in duba jikin nata mu gani ko tana da bukatar wani maganin."
Abba na fadin haka bai saurari cewar mahaifiyarsa ba ya shige bedroom din Mansurar.
Kwance Abba ya dadda Mansura ta rufe duka jikinta da bargo. Abba zama gefan bed din ya yi yana kai hannunsa akan Mansurar ya ji jikin nata.
"Alhamdulillah, na ji jikin naki babu zafi, ko sanyin damuna ne?." Mansura dai bata ce komai ba. Abba ya Kuma cewa "Ya jikin naki ? Meke miki ciwo yanzu?." Kai Mansura ta girgiza ma Abba ta ce "Babu komai, sanyi nake ji na rufe jikina."
Ajiyar zuciya Abba ya sauke, ya kama hannun Mansurar ya ce "Ki tashi ki zauna to." Mansura tashi ta yi ta zauna. Abba Kuma ledar ya shigo da ita ya dakko ya ciro yoghurt dinda ya siyo ma Mansura ya zuba Mata a cup ya mika Mata, da yake Mansura yunwa take ji duk ta kasa cin shinkafar da mahaifiyar Abba ta kawo mata da rana, hakan ya sa ta shanye yoghurt din.
Abba ganin ta shanye wanda ya zuba Mata Kuma cika Mata cup din ya yi shima ta shanye, Kara Mata Abba zai yi ta girgiza kai ta ce "Ya isan."
Abba ledar ya nuna mata ya ce "Akwai farfesu ciki sai ki ci anjima." Ya fadi maganar yana dakko biscuit ya fasa ya kai daya bakin Mansurar, Kai Mansura ta girgiza ta ce "Na fa koshi." A'a, ki ci biscuit din ki ji yana da dadi."
Mansura bude bakinta ta yi tana cin biscuit din.
Daidai Abba ya Kai biscuit din bakin Mansura yana Bata gashi sun zauna gaf-da gaf rabin jikin Mansurar kusan duk a jikin Abba take, dan duk ya manmatseta.
Abba ganin mahaifiyarsa da ya yi ya sa ya rika Matsawa a hankali da wayau. Ita kanta Mansura batasan lokacin da ta amshi biscuit din daga hannun Abba, gashi dukansu sai su ka yi kamar marasa gaskiya.
Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Ta sha maganin ko?."
Kai Abba ya sosa ya ce "Eh da yake maganin na da karfi yana dakyau ta ci abinci kafin shine ya sa namatsa mata ta ci abincin."
Mahaifiyar Abba bata ce komai ba, hannu ta mika ma Abba ta ce "Ban maganin in Bata?."
Abba kai ya sosa dan babu magani ma tare da shi, take da bara ta fado mai ya ce "Mama baki ji ba, na ce da yake maganin na da karfi shi ne natsaya ina bata abinci in ba haka ba zai wahalar da ita maganin." Abba ya fadi maganar yana tashi ya ce "Akwai alllurar da zan mata anjima."
Abba na fadin haka ya fita.
Mahaifiyar Abba bin Abba ta yi yana ta sauri zai fita, mahaifiyar Abba Kiran Abba ta yi, karasawa cikin falon ya yi ya zauna yana cewa "Mama gani."
Mahaifiyar Abba daure fuska ta yi ta ce "Abba anya ko kana aiki da ilimin islamiyarka?." Abba dago kai ya yi ya ce "Mama me ya faru?."
Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Kai kanka ai kasan abinda ka yi baikamata ba inda kana ganina ka fara Matsawa, da da iliminka Abba zaka zauna kana nanike ma mace wadda ba murramarka ba, to daga yau ban amince ba ban yadda ba karka Kara shiga dakin Mansurar Kai kadai dan Wallahi ka fara bani tsoro."
Abba dai baice komai ba kansa kasa, mahaifiyarsa ta gama fadanta ta tafi ta barsa a wajan.
Abba tashi ya yi ya fita yana dariyar fadan mahaifiyar tasa dake cemai "Duk inda kake Wallahi ka tuna Allah na kallanka."
Abba wanka ya yi da sauri kafin ya nufi masallaci, bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar issha'i. Abba ya san ko ya yi ma mahaifiyarsa karyar zai yi ma Mansura allura tare za su shiga bedroom din Mansurar hakan ya sa ya share maganar. Koda ya zo ya ci tuwa ya zauna suka yi fira da ya tashi zai tafi Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "Hala ka manta da allurar da ka ce za ka yi ma Mansura?." Ban manta ba na bari sai da safe ne, ganin bata dade da shan maganin ba." Shi kenan sai da safen."
Mahaifiyar Abba ta ce, fita suka yi tare da Abba yana fita ita Kuma ta sama kofar falon key ta rufe ta koma bedroomta ta kwanta.
Misalin karfe goma Abba ya tabbatar yanzu mahaifiyarsa ta yi barci ya Kira Mansura a waya akan ta zo ta bude masa kofar falon, Amma Mansura Bata daga ba, Abba sai da ya yi ma Mansura Kira 5 bata daga ba dole ya rabu da ita.
Ya koma bangaransa yana jin zafin kin daga wayarsa da Mansura ta yi .
Mansura ko tana ganin Kiran Abba haka nan taki dagawa.
Washagari da safe Abba da ya shigo gaida mahaifiyarsa, bayan sun gaisa ya ce "Mama bari in duba jikin Mnasura in ga jikin nata zan tafi aiki Kar sai na je a kirani irin na jiya."
Mahaifiyar Abba tashi ta yi ta rufe alQur'anin hannunta ta ce "Muje nima inga jikin nata."
Mahaifiyar Abba ta sa Abba ta yi har bedroom din Mansura, zaune suka iske Mansura daga ita sai towel ta fito wanka. Mansura hijab dinta ta dakko tasa tana rufe jikinta, cikin ladabi ta gaida mahaifiyar Abba da Abba. Mahaifiyar Abba ta amsa Amma Abba da kallo ya bita yana tsaye, mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi da yaja ya tsaya baice komai ba ta ce "Abba ka duba jikin nata Mana."
Abba Matsawa ya yi inda Mansurar take ya juyo yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mama tasa hijab ta rufe jiki taya zan ji yanayin dumin jikin nata, inda dai ba zan gane da ido ba."