← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi, ta ce "Abbana, nikam sai inga yarinyar nan kamar tana da wata boyayyar damuwa da ta aje a ranta. Lokuta da dama zaka ga idonta ya yi jajir alamun ta ci kuka, Koda yaushe ina tambayar Amina kodai ta fada mata wani abu, amma sai ta ce min bata fada mata komai ba."
Shiru Abba ya yi kafin ya ce "Mama, tun farko ba na fada miki yarinyar nan ba gaskiya ta fada mana labarinta ba."
Kai mahaifiyar Abba ta jinjina alamun hakane ta ce "Gaskiya yanzu na fara yadda, saboda idan mutuwar iyayanta ce ya kamata ce ta dangana haka nan, hakika mutuwa na da radadi da Kuma magagi, tom Amma Allah na sa ma mutum juriya aransa, musamman idan aka arba'an, sannan in dai bawa ya yi imanun kowa zai mutu radadin mutuwa da magaginta na watannaine, Allah na sama bawa salama a rai, sai dai ranar da ya tuna ya yi kuka, amma ba irin Wanda nake ganin yarinyar nan na yi ba, kukanta baya kama da na rashi, ya fi yanayi da furgici da gigita. Tom, amma dai inda har yanzu bata nuna mana wani aibunta ba sai mu yi hakuri murungumi kaddarar kasancewa data."
Abba kallan mahaifiyarshi ya yi kafin ya ce "Shagwaba ta yi ma yarinyar yawa da sangarta, bare a fahimceta da kyau, shi ya sa nake ganin ko tsabar shagwaba ne ya sa take hakan?." Tom, kila, zai iya yuwuwa shagwabarce. Yauwa Abba mu bar wannan maganar ma, na ce yau she zaka je ganin jaririn Zainab? Ka ga dai yau kwana biyu da haihuwar."
Abba ido ya zaro da sai yanzu ya tuna da maganar haihuwar, ya ce "Gobe in sha Allah zani."
Mahaifiyar Abba, hararar Abba ta yi ta ce "Kamanta goban mu ka yi da Kai za ka je ganin Aisha, yarinyar da muka yi magana."
Abba shafa kan shi ya yi bisa ga alama ya manta, ya ce "Wallahi na shafa'a, in sha Allah goban sai inje, amma Mama ita ta san da zuwan nawa?." Ta sani Mana, mahaifiyarta ta sanar Mata, ka ga idan kuka daidaita ba sai a hada a yi da na Amina ba."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Allah ya kaimu goban sai in je in ganta✍🏻

Fadila Sani Bakori ce

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Daga Marubuciyar

*Fadeela
*Meenalyn Daddy
*Oga Habib
*Abdurrahim
*In da rai
*So ne sila
*Daga Allah ko dora ma Kai
*Rayuwar Haidar
*Bakin kishi

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

Litafin Abbana na kudi 400 my number 08063830828

P 15-16

Washegari ya kama juma'a, Abba 4 ya dawo aiki, Yana dawowa ya yi shirin zuwa wajan Aisha kamar yadda suka yi da mahaifiyarsa. Abba bayan ya fito da shirin zuwa gidansu Aisha, Kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama, zan tafi gidansu Aishar."
Mahaifiyar Abba zaro idanunta ta yi ta ce "Abbana, a haka zaka gidan surikan naka? Haba Abbana wayace maka ana zuwa gidan surikai da k'ananan kaya, ka sa manyan kaya mana."
Abba bata rai ya yi ya ce "Haba mama, kayan nan me suka yi." Ni dai dan Allah ka je ka canza."
Abba ba tare ya kara cewa komai ba ya tafi ya canza kayan daga can ya wuce gidansu Aisha, da yake yasan gidan yana kai mahaifiyarsa in abin Allah ya sa alkairi ya samu ko alakyauta.

Kasan cewar ansan da zuwan Abban ya sa duk wani abu na tarbar bako an tanadar masa shi. Yana zuwa gidan ya Kira Aisha a waya. Aisha na zaune cikin jillimin bakon da mahaifiyarta ta sanar da ita zai zo wajanta yanzu, ta ji ringing din wayarta. Aisha cikin siririyar muryarta ta daga wayar tare da yin sallama.
"Gani a kofar gidanku." Abba ya ce yana mai kashe wayarsa.
Aisha tashi ta yi tana sanye da hijab dinkin bare kyada.

Abba na nan tsaye hankalinsa gaba daya ya tafi a wayar hannunsa, Aisha ta yi masa sallama ta yi.
Abba dago kansa ya yi yana mai zuba mata idanunsa. Aisha kanta kasa ta gaida Abba.
Abba amsa mata ya yi babu yabo babu fallasa. Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Mu shiga falon Daddyna kamar zai fi safe."
Kai Abba ya girgiza ya ce "A'a nanma ya isa." Shiru ya yi kafin ya dora da cewa "Nasan gida an gabatar miki da koni waye tun kafin in zo."
Aisha Kai ta jinjina ma Abba, ta ce "Eh, haka ne,Malama ta fada min komai."
Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ma Sha Allah na ganki mai sunan mommyna, kamar yadda mahaifiyata ta umarce ni. Ya kiba ganni na yi Miki?." Abba ya tambayi Aisha.
Aisha jin tambayar ta yi wani iri, kasa cewa komai ta yi kanta kasa.
Abba, Kiran sunanta ya yi ya ce "Malama baki ban amsa ba kin sidda Kai kasa, dalilin da ya sa na yi miki tambayarne bansan ko kina da Wanda zaki aura ba ake son hadaki dani, kamar ni Kinga ban shirya aure ba, zan ne bisa umarnin mahaifiyata ba bisa son raina ba."
Aisha shiru ta yi tana jin maganganun nasa wasu iri, hakan ya sa ta ce "Ayyah, yayana nima hakane a bangarena, zan yi biyayya da umarnin mahaifiyata ne."
Murmushi Abba ya yi ya ce " Ni a ganina bai kamata mu yi abin da zamu cutar da kanmu ba ki yi tunani, na barki lafiya."
Abba na fadin haka ya ja motarsa ya tafi ya abar Aisha da tunani, dan idan zata fada makanta gaskiya Abba ya yi Mata, dan haka ba ta jin zata iya mujirema bukatar zuciyarta, sanan uwa uba mahaifiyarsa na sonta.

Abba ba shi ya koma gidan ba sai bayan sallar issha'i. Mahaifiyar Abba da fara'arta ta tarbi Abba tana cewa "Babana fira ta yi dadi, da alama dai tare da na Amina za a hada nan da wata uku musha biki."
Abba zama ya yi yana murmushi.
Amina ko da ta kaku ta ji sauran labarin ido ta zaro ta ce "Laa, Yaya Abba aure zai yi mama?." Amina ta ida maganar cikin jin dadi sosai. tana taba Mansura da yake duk suna falon.
Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "Aiko ki fara shirye-shiryan tarbar Auntynki. Oh namanta she bakya gidan kema lokacin za mu mika ki gidan Ahmad." Amina turo baki ta yi.

Mahaifiyar Abba maida kallanta ga Abba ta yi ta ce "Abbana, ya Aishar?."
Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ganin yadda take ta doki da lamarin, cikin danne abin da ke damunsa ya ce "Na ganta Mama, ita ba kyakkyawa ba ita ba mummuna ba."
Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Abbana, babu mummuni a musulmi, Kuma kyawun zuciya ya fi na fuska, ni dai yanzu fadamin ya kuka yi da ita?."

Abba ji ya yi bakinsa ya kasa furta kalmar a'a, hakan ya sa ya ce "Mama itama fa yarinyar ta sanar dani tana da Wanda take so."
Mahaifiyar Abba bata fuska ta yi ta ce "Idan tana da Wanda take so kenan shi kenan Kai ma kana da wadda kake so baka sonta, Yes or no?."
Abba kallan mahaifiyarshi ya yi wanda daga gani kiris take jira ta ji ya furta abin da ke ransa ta ci ubansa. Abba cikin jarumta ya ce "Mama, dan Allah ki canza min wata, yarinyar ta cika shiru-shiru, tana magana tana tsugunnar da Kai kamar munafuka."

Mahaifiyar Abba ta dade tana kallan Abba kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce " Kamanta abin da ka ce min jiya ko, ka ce ko baka ganta ba in dai ta yi min to zaka aureta, kenan dadin baki ka yi min, dan haka in dai ka ga baka auri Aisha ba to ban da raine, amma Wallahi tun da bakinka ya furta sai ka aureta, inda har sai da na ji ta bakinka kafin in sanar da mahaifiyarta, dan haka baka isa ba kasa in yi karamar magana ba Wallahi, idan kana da shirin da za ka yima ka shirya dan in sha Allah tare za a hada auran da na Aisha, zan samu baban yara mu yi magana gobe."
Mahaifiyar Abba na kaiwa haka ta tashi tabar ma Abba falon, dan bai taba bata mata rai irin yau ba, tun da ta fara ganin Aisha yarinyar ke burgeta, dan da dama itake masu karin karatu idan mahaifiyarta ba zata zo ba. Sai da Allah zai amsa mata rokanta da ta yi ya naimi kawo Mata matsala.

Abba shiru ya yi ganin mahaifiyarsa ta tafi, dafe kai ya yi yama rasa abin cewa. Mansura da gaba daya itama ba cikin hayyacinta take ba tun da ta ji maganar auran Amina. Tashi ta yi da sauri ta bar falon jin kuka zai kubuce Mata.

Amina Kuma zuwa ta yi ta zauna kusa da yayanta ta ce "Yaya Abba Wai meka faruwa ne tsakaninka da mama?."
Abba kallan Amina ya yi cikin damuwa ya ce "Wata yarinya Mama ta lakaba min in aura, Wallahi Amina kafin in ga yarinyar sai na ji na aminta da zabin mama, Amma Kuma da na ganta sai na ji gaba daya bata yi min ba, shine nake sanar da mama akan ta canza min wata, kin ji dalilin fadan."
Amina cikin damuwa itama ta ce "Amma Yaya Abba meye aibunta, gata da ilimin addini sosai, da dama ma fa ita ke koyar da su Mama."Amina Wallahi na rasa dalili, Amma actual abin da na sani bana so in ga mace ta cika sanyi irin nata haka."
Amina kallan Abba ta yi ta ce "Tom Yaya Abba kana da wadda kake so ne?." A yanzu babu."
Shiru Amina ta yi kafin ta ce "Yaya Abba indai haka ne ka yi hakuri da zabin mama, idan ba haka ba da alama zaku iya samun saba ni."
Ajiyar zuciya Abba ya soke ya ce "Zan yi ƙoƙarin ganin na koya ma kaina sonta." Yauwa yayana shi ya sa nake yinka da yawa kana da saurin fahimta."
Abba dungure Amina ya yi Yana murmushi ya tashi ya nufi bangaransa.
Chapter 13 · 0% Book details