Sashe 28
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mansura bayan ta idar da sallar, juyowa ta yi tana kallan Abba, kafin cikin sanyi kanta kasa tana wasa da hannunta ta ce "Ina kwana yaya Abba."
Abba kallan Mansura ya yi ba tare da ya amsa gaisuwarta ba ya ce "Me ya sa kika ki daga kirana?."
Mansura waige-waige ta fara nanaiman wayarta ta ce "Namanta da wayarne ban gants bama." Tashi ki duba wayar." Abba ya fadi maganar babu annuri a fuskarsa.
Mansura tashi ta yi tanaimi wayar, Mika ma Abba wayar ta yi, Kai Abba ya girgiza ya ce "Duba ki gani Kira nawa na yi miki."
Mansura dubawa ta yi kafin ta juyo da kallanta ga Abba ta ce "Yi hakuri Yaya Abba Banga Kiran bane."
Abba tashi ya yi ya ce "Okay, ki ajeta kusa." Yana fadin haka ya tashi ya fita. Mansura da kallo ta bi Abba har ya fita, ganin yau yadawo mata ainihin Abban da ta sani.
Abba ko yau Koda ya je aiki ya kasa komai saboda damuwar nauyin da mahaifiyarsa ta daura mai.
Abba zaune yake a office dinsa ya kasa komai, so yake ya Kira Number Aisha amma ya kasa, dan gaba daya sai ya ji ta Kara fita ransa, Abba number Mansura ya Kira Kira daya ta daga. Abba cikin muryarsa mai bayyana yanayin damuwa ya ce "Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata ga zuciyar da ta hana zuciyar Abba sukuni." Ya fadi maganar cikin rashin walwala.
Mansura shiru ta yi, kafin ta ce "Tare da Kai Yaya Abba." Abba kuma ya ci gaba da cewa "Man's Ina cikin damuwa." Abba ya fada cikin damuwa.
Mansura cikin alamun tausaya masa ta ce "Ayyah Yaya Abba me ya saka a damuwa?." Mama ce ta sani a damuwa Mansura." Mansura da alamun mamaki ta ce "Mama Kuma? Yaya Abba yadda mama ke ji dakai nasan ba za ta sa ka a damuwa ba, saidai in baka fahimci mama bane."
Shiru Abba ya yi jin Abin da Mansura ta ce, ya ji ma baice komai ba, kafin ya ce "Man's kinsan ansamin ranar aure da mommy? To ta tura ma mama text cewa ta fasa aurena, amma mahaifiyarta taki yadda tana so mama ta je ta sa Mata baki mahaifiyarta ta amince tasan maganarta kadai zata ji, tom shine mama take ganin laifinane ya sa tace ta fasa auran, taban nan da kwana biyu in daidaita tsakanina da ita, na rasa yadda zan yi man's"
Mansura shiru ta yi dan bata san me za ta ce ma Abba ba. Abba jin ta yi shiru ya ce "Man's ke fa nake saurare." Mansura cikin rashin sanin abinda zata ce ta ce "Yaya Abba ka yi abinda mama tace Mana." Tom ni ai bana sonta, akwai wadda nake so."
Daga can bangaran Mansura ta ce "Yaya Abba, ita wadda kake son tana sonka?." Abba shiru ya yi, kafin ya ce "Ban Sani ba, amma dai na yi ma kaina alƙawarin dolanta ma ta soni."
Ido Mansura tazaro ta ce "Yaya Abba ana soyayya dole ne? Idan takika fa?." Sai in makata kudi kawai."
Mansura dariya ta yi bata ce komai ba.
Abba jin Mansura ta yi shiru ya ce "Ya wakar nan da na tura Miki kin jita kuwa?."
Mansura tana so ta cema ma Abba a'a amma Kuma ba ta iya garya ba, hakan ya sa ta ce "Na ji."
Ido Abba ya lumshe kafin ya ce "Ina so ki Kara jinta, anjima idan na dawo za mu yi magana akan wakar." Kai Mansura ta daga kamar Abba na kusa da ita.
Abba bayan ya gama waya da Mansura ji ya yi kamar anwanke mai duk wata damuwa dake damunsa, hakan sai ya bashi kwarin gwiwar Kiran Aisha. Aisha ba ta daga ba sai da ya sake Kira, kafin ta daga tare da sallama cikin sanyinta.
Abba cikin salon yaudara dan Aisha ta janye kudirinta kamar yadda mahaifiyarsa ta umarcesa da ya sasanta tsakaninta da ita nan da kwana biyu ya sa Abba ya ce "Mommyna, laifin me na yi kika fasa aurena?."
Aisha shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba naga kamar baka sona ne shi ya sa." Kamar bana sonki, Mommyna da bana sonki da ba zan aminta da auranki ba, wayace miki anayima Namiji auran dole Mommyna haba, Yama za ai in ki son mommyna sai ka ce danbanza."
Aisha dariya ta yi da yake zuciyar da ta kamu da so bata da wuyar yafiya ga masoyinta hakan ya sa Aisha gaba daya ta manta da furucinta da ta yi ta fara ganin gangancinta da wautarta ta ce "Shi kenan Yaya Abba, Ina tuba na janye kalamaina masu cike da tarin wauta."
Abba cikin jin dadin furucin Aisha batare da yasha wuya ba ya ce "Yauwa Mommyna, yanzu yaushe za ki zo yi ma mama bangajiyar biki danni da ita mu shaida da kin janye maganarki?."
Aisha murmushi ta yi ta ce "Umarninka kawai nake jira, ko yanzu ka ce min in je ashirye nake."
Abba tabe baki ya yi ya ce "Ki bari sai weekend Kinga Ina gida lokacin."
Abba sun jima suna waya da Aisha kafin ya yi Mata sallama da karyar in ya tashi aiki da wuri zai zo ya ganta.
Abba bayan ya koma gida, falon mahaifiyarsa ya yi direct, sai dai yana magana tana dauke Kai, sallamarsa ma ciki-ciki ta amsa mai. Abba murmushi ya yi ya ce "Mama akan wata kike fushi da Abbanki, mai sunan mahaifinki."
Mahaifiyar Abba hararar Abba ta yi ta ce "Akan Aisha ai Wallahi har falon nan ka kusa bar shigowa, nifa bawai na ce dole ka auri Aisha bane, alokacin da na yi maka maganarta sai ce min ka yi koma baka ganta ba inda ta yi min shikenan, Amma duk da haka ban yadda na yanke hukunci ba sai da ka je ka ganta ka amsa ta yi maka sannan na tura iyayanka, sai yanzu Kuma ka zo ka sani a kunya, tom Wallahi baka isa ba."
Abba dariya ya yi ya ce "Mama inda mommy ce tuni muka shirya, dan ta sanar dani ma zata zo yi miki bangajiyar biki."
Mahaifiyar Abba shiru ta yi tana kallan Abba, kafin ta ce "Abba dan Allah Annabi ka taimakeni ka fiddani a kunyar uwar yarinyar nan, kana ganin hidimar da ta yi abikin Amina, kasan ba dan itaba ba zamu ga malamai da damaba a wajan walimar nan."
Abba kansa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya ya ce "In Sha Allah mama zan auri mommy." Abba, bawai ka aureta kadai bane damuwar, ka sota, ka bata kulawa wadda duk wata 'ya mace take bukata, idan ka yi min haka ka gama min komai Wallahi."
Abba hannun mahaifiyarsa ya kama ya ce "In sha Allah zan yi ƙoƙarin haka mama."
Abba wayarsa ya dauka ya tura ma Mansura text kamar haka "Gani a falon Mama ki fito."
Mansura bayan ta gama karanta sakon murmushi ta yi ta maida mai kamar haka. "Yaya Abba yanzu na bar falon, Kuma na yi ma mama saida safe." Abba bayan ya gama karanta sakon Mansura wani ya tura Mata kamar haka "Bana son musu idan kika dawo yanzu korarki za ta yi ki ce kin je kin kasa barci."
Mansura bayan ta gama karantawa tashi ta yi ta fito.
Abba kamar ba yanzu suka gama chart da Mansura ba dauke Kai ya yi. Mansura zama ta yi tana gaida Abba.
Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama kullum idan na shigo bana samun Mansura a falon nan, na ce tana tayaki girki ma kuwa?."
Mahaifiyar Abba murmushi ta yi ta ce "A'a ai har yanzu kewar kawarta bata saketa ba." A'a, Mama daga yau ta rika fitowa tana tayaki aiki itama ta huta zaman shirun da takeyi , Ina so ma in Samar Mata teaching a school din da Amina ta yi ta huta zama shirun."
Mansura turo baki ta yi jin abinda Abba ya ce ta ce "Yaya Abba ni dai banaso."
Abba da mamaki ya kalli Mansura ya ce "Shi kenan, akwai computer training in kina so?." A'a, Ni dai bana son komai."
Mahaifiyar Abba dariya ta yi ta ce "Shi kenan Abba inda bata so karka takura mata."
Abba daga nan baikuma cewa komai ba ya tashi ya fita.
Bangaran Aisha da safe tana zaune ta turama Abba Sako na barka da safiya.
Abba na wajan aiki ya ci karo da sakon Aisha kamar haka "Barka da Safiya Habibina da'ima. Na farka cikin wallawa, saboda kasancewarka a rayuwata. Ina addu'a Allah ya sa ka soni Koda rabin Wanda nake yi maka ne. Daga Masiyarka mai kaunarka har abadan abidina."
Abba copy din text din Aisha ya yi bayan ya gama karantawa ya gyara ya tura ma Mansura.
Abba replying a yi ma Aisha kamar haka "Na gode da kulawarki amaryata."
Bangaran Mansura ko Koda ta ga sakon Abba maida wayarta ta yi ta aje.
Bangaran Abba Kuma jira yake ya ga replying dinta ga ji shiru, hakan ya sa ya Kira Mansura, Kira daya ko ta daga.
Abba cikin sanyi ya ce "Baki ga sakona bane?." Yaya Abba naka sakonka Amma.." shiru Abba ya yi kafin ya ce "Amma me?."
Mansura cikin sanyi ta ce "Yaya Abba mommy." Shiru Abba ya yi, sannan ya ce "Mansura nasan da mommy ai nace Ina sonki, mommy zabin mahaifiyatace, ke Kuma zabina ce, dan haka daga yau Kar in Kara jin kin min maganar mommy."
Mansura shiru ta yi batace komai ba, Abba jin haka ya ce "Mansura, ina sonki, na so ace mu yi maganar gani gaki, Amma naga kamar kina tsoran mama tasan muna soyayya, bana jin mama zata kiki Mansura, idan har mama kike gudu dan Allah ki saki jikinki dani, yau idan na dawo akwai maganar da nake so mu yi."
Mansura shiru ta yi kafin ta ce "Yaya Abba mu yi ta a waya Mana." A'a zaki fi saurin amincewa idan muka yita a fili." Abba na fadar haka ya kashe wayarsa.
Mansura bin wayarta ta yi da kallo.
Abba bayan ya dawo aiki falon mahaifiyarsa yayo kasan cewar bata falon ya sa Abba ya shiga bedroom din Mansura.