Sashe 18
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari Aisha da wuri ta tashi, ta samu kankana ta goge fuskarta dashi, sannan ta debo kurkur sokali daya da fulawa itama cokayi daya da Madarar gari itama cokali daya ta fasa danyan kwai tasa kwaiduwar ta hada ta motse kafin ta shafe fuskarta da hannuwanta da hadin. Bayan 30 minute Aisha ta wanke fuskarta da ruwan dimi, kafin ta shiga wanka. Da yake mahaifin Aisha komai yana koya masu hadin gargajiya ne saboda baya so su yi amfani da kwaya ko man bleaching, hakan ya sa yake koya masu hadin islami wajan gyaran jikinsu.
Aisha bayan ta fito wanka man kwakwa ta shafe jikinta da fuskarta da shi.
Kafin ta dakko wata bakar Abaya ta sa ta tanannane kanta da farin jesi. Wayyo Allah ku zo kuka Aisha yadda ta yi kyau, mahaifiyars Aisha kallan Yar tata taita yi ganin yadda take sheki. Aisha za ta fita mahaifiyarta ta kirata ta ce "Ki kula Wallahi idan mahaifinki ya ganki da gyale babu ruwana. Aisha turo baki ta yi ta ce "Mommy duk inda zamu a mota fa zamu ba a kafa ba." Shi kenan Allah ya tsare."
9:45AM Aisha ta shiga gidansu Abba.,...✍🏻
Abbana sai Monday za ku jini in sha Allah bana yin update ranar weekend, wancan week dinma na yi ne saboda a week din na fara littafin.
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 21-22,
Aisha koda ta yi sallama falonsu Amina babu kowa, hakan ya sa ta nufi bedroom dinsu Amina kai tsaye. Amina da tashi ta yi tana murmushin ta rungume Aisha ta ce "Oyoyoo Mommyna." Aisha zama ta yi tana kallan Hassana ta ce "Hassana yahaya dama wai kina garinnan." Wadda Aisha ta Kira da Hassana murmushi ta yi ta ce "Ke dai zan ce kina gari." Take hira ta barke tsakaninsu dan sun dau dogan lokaci basu ga juna ba. Hassana kallan Aisha ta yi da yake Hassana irin masu shegen tambayar nan ne ta ce "Aisha a ina kika san Amina?."
Amina amshe zancan ta yi ta ce "Yaya Abba ya hadamu, Yaya Abba zata aura yanzu haka wata hudu masu zuwa auransu." Hassana Kai ta jinjina ta ce "Ki ce daga yau mu dawo cewa Aunty Aisha mu bar cewa Aisha kaitsaye." Amina kallan Mansura ta yi da har yanzu take kwance bata tashi ba ta ce "Mansura 10:10AM fa dan Allah ki tashi ko wanka fa baki yi ba, yanzu za ki ga Kiran Yaya Abba Wallahi."
Mansura tashi ta yi da sauri ta fada bathroom dinsu. Hassana kallan Amina ta yi ta ce "Amina wannan fa wacece?."
Amina hararar Hassana ta yi ta ce "Wai ke dan Allah yaushe za ki bar wannan halin naki na tambaye-tambaye ne?." Hassana hararar Amina ta yi itama ta ce "Na ji ance tambaya rabin ilimi ce, meye laifin da na yi tambaya akan abin da ban Sani ba."
Cikin jin haushi Amina ta ce ma Hassana "'yar kanwar mama ce."
Amina Kai dubanta ta yi ga wayarta dake ringin tana addu'ar Allah ya sa ba Yaya Abba bane. Amina ido ta zaro ganin Abba ne, gashi tasan babu abin da ya tsana Kamar jira, hakan ya sa Amina na dagawa ta sanar dashi gasu nan fitowa. Amina kallan Aisha ta yi ta ce "Momnyna ku je dan Allah kafin Mansura ta fito idan ba haka ba tafiya zai yi Wallahi."
Aisha kallan Hassana ta yi ta ce "Muje."
Abba na cikin motarsa yana jiran fitowarsu Mansura, su Aisha suka karasa inda ya yi parking.
Aisha gefan Abba ta matsa ta ce "Yaya Abba ina kwana." Abba da farko bai gane Aisha ba sai da ta yi magana dan ta yi mai kyau cikin shigar da ta yi.
Abba babu yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar Aisha da ta Hassana baki daya, yana tsaki tare da dayasanin amsa ma Ahmad da ya yi zai yi jigilar kaisu Mansura duk inda zasu. Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Ku shiga Muje."
Aisha zagayawa ta yi ta zauna a front seat. Abba jan motar ya yi zai tafi Aisha ta ce "Yaya Abba akwai sauran mutun daya." Abba dakatawa ya yi dan dama ya yi mamakin ganin baiga Mansura ba. Shiru-shiru babu Mansura babu alamarta, bunubunu Abba na duba agogon hannunsa, Abba wayarsa ya dauka ya Kira Amina ransa bace tana dauka ya ce "Uban waye drivernku da zaku shanyani ina jiranku?."
Amina hakuri taita ba Abba, Abba ya kashe wayarsa.
Amina Kuma can kallan Mansura ta yi da tasa wata green abaya. Amina cikin jin haushi ta ce "Mansura kina ji fa Yaya Abba ya Kira sai fada yake, amma killi yadda kike shiryawa kamar ba jiranki aike ba."
Mansura kallan Amina ta yi da ta dage sai fada take mata, Mansura turo baki ta yi ta ce "Tom ban ATM cart din naki da pin din."
Mansura da sauri ta fita. Mansura na zuwa Abba ya ja motar gaba daya ransa a bace yake, shi kansa baisan me ya bata mai raiba kawai haka nan ya tsinci kansa cikin bacin rai.
Bayan sun yi dan yi nisa da tafiya kadan, Aisha ta katse shirun da cewa "Hassana Kun ko gaisa da Yaya Abba?." Eh mun gaisa." Aisha cikin son yin magana da Abba ta ce "Ban yadda ba, Yaya Abba wai kun gaisa da Hassana?." Biki ji abin da ta ce bane, ko karya za ta yi miki." Cewar Abba.
Hassana Kuma carab ta amshe ta ce rabu da ita Yaya Abba dan ta tsokaneni ne." Na ga alama." Abba ya ce.
Aisha Kuma turo baki ta yi ta ce "Babu maganar tsokana sanin halinki da na yi ne." Kut, Yaya Abba ka ji wai sanin halina da ta yi ne dan Allah idan a gaban bare ta fadi maganar nan Yaya Abba ba sai a dauka mugun hali garan ba." Abba murmushi ya yi ya ce "A'a babu wanda zai dauke ki haka, ai tunaninka kamanninka." Hassana cikin jin dadi ta ce ma Aisha "Muguwa kinji dai ko."
Aisha murmushi ta yi ta ce "Yaya Abba meye Kuma tunaninka kamanninka, wata irin Hausa ce wannan." Ki tambayi kawarki."
Aisha juyawa ta yi tana kalan Hassana ta ce "Fassara min Hausar Yaya Abba."
Hassana harar Aisha ta yi ta ce sai kin biya." Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba agabanka ake min wulakanci, kana jinta fa wai sai na biya, tom ki rike kalamanki nasan kema ba sani ki kaiba, Yaya Abba zai sanar da ni daga ni sai shi ba za ki ji bama."
Daidai nan Abba ya yi parking ya ce "Mun zo sai ku yi sauri ku sayi abun da za ku siya ko ba a nan zaku yi siyayyar ba?." A'a Yaya Abba a nan ne." Cewar Aisha.
Bude motar suka yi duk suka sauka, Mansura Kuma Mika ma Hassana ATM card din Amina ta yi tare da fata Mata pin din. Hassana da mamaki ta kalli Mansura ta ce "Sister bangane ba kin mikamin ATM card kinki fitowa?." Mansura ya mutsa fuska ta yi ta ce "Sister bana jin dadi kuje dan Allah."
Hassana Kai ta girgiza ta ce "Haba sister kinsan mu mata da kishi Aisha ai ba zata ji dadi ba ta tafi ta barki da wanda zata aura tare." Abba juyowa ya yi yana kallan Hassana ya ce "Inda ta kawo muku uzirinta ku yi hakuri ku tafi Mana."
Shuru duk suka yi sannan Aisha ta kamo hannun Hassana tana murmushi ta ce "Mu je kawata dole mu yi mata uziri inda bata da lafiya."
Suna tafiya Hassana ta kalli Aisha ta ce "Caf dijam, Aisha ki ce kina nan da halin sakarcinki, wannance ta yi kama da mara lafiya, tana sone kawai ta tusa kanta a wajan Yaya Abba ta kwace miki shi, ke baki san yanzu yadda ake tashan kwacan saurayi bane. Baki ji yadda ta yi maganar ba ita aladole ga shagwababba, wai bana jin dadi ne ku je dan Allah. Ke daga jin yadda take magana kinsan makirci ne cike da cikinta."
Aisha shiru ta yi kafin ta ce "A'a inaganin ita fa kamar haka take, yadda na lura da ita kamar bata son shiga hayaniya ne, saboda ranar da muka je gidan suna ma haka tayi, ƙarshe ta tafi ta barmu."Hmmm, ni dai hankalina bai kwanta da yarinyar nan ba." Cewar Hassana.
Hassana duk yadda ta so su yi sauri a cefa nan abun gagara ya yi.