← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 36

Sashe 23

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansura turo baki ta yi kafin ta ce "Assalamu alaikum." Ameen Wa'alaikumussalam. Yauwa ko kefa, bari inga da gaske ne baki yi kukan ba." Abba na fadin haka ya kunna flashlight din wayarsa ya haske Mansura. Mansura hannu ta sa tana kare fuskarta saboda haskan na kashe mata ido.
Abba kashe hasken ya yi ya ce "Da gaske dai baki yi kuka ba, tom daga yau har a tashi taron baki idan har baki sake yin kuka ba ki fadi duk abin da kike so ni Kuma zan miki shi."
Mansura dai murmushi ta yi ma Abba ba batace komai ba. Abba Kuma kallanta ya yi ya ce "Muje in rakaki."

Abba sai da ya ga shigar Mansura kafin ya juya ya tafi.

lokacin da Mansura ta koma Amina ta gama waya da Ahmad kenan.
Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Ina mamaki waiku salon soyayyartaku ta sirrce ce, yanzu na gama waya da Yaya Ahmad na tambayeshi dan nasan Yaya Abba na fada masa komai nasa, amma ya ce min bai sanar da shi soyayyarku ba. Mansura me ya sa kike boyemin soyayyarku da Yaya Abba? Ko shi ya ce ku boye ne?."
Mansura hararar Amina ta yi ta ce "Wai ku anan Katsina haka ake yi ne babu damar a ga mace da Namiji suna magana sai ace soyayya suke, har yaya Ahmad dinma kenan baki yadda da abin da ya ce ba, Allah raina sosai yake baci idan Kuna irin wannan maganar sai inga kamar Kuna banbanta tsakanina dake ne dan da kin daukeni kamar yadda kike fada ba zaki rika hadani da Yaya Abba ba dan kinganmu kawai Muna magana."

Amina shiru ta yi dan abinda Mansura ta fada hakane, ya za ai daga sun yi magana ace soyayya suke. Amina ganin ran Mansura ya bace hannunta ta kama ta ce "Yi hakuri Mansura, na yadda Allah tunda Yaya Ahmad ya fada min, nasan da ace Yaya Abba na sonki da ke kanki kafin ya fada miki zai fadama Yaya Ahmad ne, na gamsu Allah."

Mansura da Amina sun yi fira kadan kafin duk barci ya kwacesu.

Washagari da wuri mai dilkar Amarya ta zo ta yi ma Amarya da kawar Amarya, wadda ta ragu kawayan Amarya da dama suka shafa a fuskokinsu.

Bayan Amarya da kawar Amarya sun wanke jikinsu daga nan suka dunguma suka tafi gidan Aunty Zainab da yake acan zasu yi sitin.

Suna zuwa wasu daga cikin kawayan suka fara daura girki.

Kawayan Amina kusan kaf sun hade ma Mansura Kai duk inda ta yi habaci kusan suke sakar mata. Mansura bata wani fahimci da ita suke ba, hakan ya sa hidimarta take ba ruwanta da kowa sai wata kawar Amina da ta nuna tana sonta.

Hakan ya sa Mansura itama ita kadai take kulawa. Ana cikin hakane Amina ta shira cikin wani blue din lass, inda me makeup din ta yi Mata simple makeup.

Amina sosai ta yi kyau, haka Yan matan Amaryar suka fara shiryawa daya bayan daya mai makeup na aikinta na gyara duk wadda ta shirya.

A haka duk suka shirya, inda Mansura ma ta shirya cikin wata green atamfar anko da suka yi, sosai ta haskata ta yi kyau.

Haka kawan Amarya ma duk suka gama shiryawa cikin wannan a tamfa ta anko.

2:30PM dubban jama'a suka shida daurin auran Amina da Ahmad....✍🏻

Littafin ABBANA na kudi ne, free pages ya kusa karewa idan kin shirya 400 ne daga zarar na gama zai koma 500 my number 08063830828

Fadila Sani Bakori ce.

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 27-28

Amina na zaune kawayanta sun sata tsakiya sai guda suke mata tare da shaigantaka irin ta kwayan Amarya, Allah ya kaimu shekara mai zuwa kamar haka mu sha suna. Amina dai ta yi banza dasu bata tanka ba, sai Aisha ce ke tare Mata.
Mansura Mika ma Amina wayarta ta yi da aka Kira ta ce "Gashi, Yaya Ahmad ke Kira." Khadija rangada guda ta yi jin Wanda akace yana Kiran wayan, Amina Koda ta daga hayaniyarsu hanawa ta yi ta ji, hakan ya sa ya Ahmad tura Mata text kamar haka "Assalamu akaimu, zuwa ga zabin zuciyata a maryata, Ina fatan tana cikin farin ciki irin Wanda nima nake ci, na gode ma Allah da ya kaini wannan lokaci ya nuna min auran gimbiyata Amina, Ina rokan Allah ya bani tsawan randa zan rayu tare da ita, ya Kuma bani zuciyar kautata Mata Koda ace ta yi min badai ba, in sha Allah babu ranar da zanga abinda gimbiyata Amina ta yi min a matsayin laifi. Na kirane in jin muryar Mata, in kuma sanar da ita ta sanar da kawayanta 5:00PM zamu zo mu daukeku keda kawayanki zuwa wajan party da Abba ya hada Mana."

Amina dora wayar ta yi a kirjinta bayan ta gama karanta sakon Ahmad tana rintse ido, da alama sakon Ahmad sun yi tasiri sosai a cikin zuciyarta. Khadija dafa Amina ta yi ta ce "Amarya an shiga sauki ne." Tana dariya ta idasa maganar.
Amina bude ido ta yi tana hararar Khadija ta ce "Yar sa ido, yaya Ahmad ya ce ku shirya 5 za a zo daukarmu za a yi party wai."
Khadija kallan Amina ta yi ta ce "Wato ma wai baki san da maganar bane?." Kai Amina ta jinjina ta ce "Allah ban Sani ba sai yanzu da yake fada min da alama shima bai Sani ba."

Amarya da kawayanta haka suka ci gaba da hidimarsu, inda sukaita daukar hotuna, da videos tare da Amarya. Mansura ko kamar yadda ta yi ma Abba alƙawarin haka ta kasance ta aje duk wata damuwatata gefe hidimarta kawai take sha, daga ka ganta ka ga kirjin biki.
Bangaran su Hassana ko tun suna habaicinsu har sun gaji sun yi shiru, dan sunga alamar Mansura batatasu take ba.

Ana cikin hakane aka sanar dasu ga abokan ango nan zuwa, masu gyara daurin dankwaki na yi masu fesa turare da masu kara powder a fuska duka.

Ahmad tare da abokansa a harabar gidan Aunty Zainab suka tsaya, sukasa aka Kira masu Amarya da kawayan Amarya a yi hoto.

Wasu daga cikin kawayan amaryar ne suka fara fitowa da Amarya.
Abba babban abokin ango ansha babbar riga wadda ta Kara fito da baiwar kyawunsa da Allah ya yi masa, sun yi shiga iri daya da ango ko mai nasu hatta agogonsu iri daya.

A hankali-ahankali kawayan amaryar duk suka fito, Abba da wayau ya gama kallace kawayan amaryar kaf bai ga Mansura ba. Yana cikin naimanta da idanusansa Aisha ta zo da iyayinta ta ce "Assalamu alaikum, abokin ango mai kama da ango." Abba juyowa ya yi yana kallan Aisha, kafin ta kakaro, murmushi Abba ya yi mata ya ce "Mommyna, ya kuke ya hidima." Aisha cikin jin dadin yadda Abba ya amsheta ta ce "Alhamdullah, Yaya Abba ya taku." Alhamdullah." Abba da wayau ya Kara dubawa ganin bai ga Mansura ba ya ce "Kice mu kama karamin hole naga kamar baku da yawa." Aisha murmushi ta yi ta ce "Kuma ka ganmu Ina jin mutum uku ne basu anan suke je su dawo." Abba cikin son sanin su waye saboda yana saran ko akwai Mansura a ciki ya ce "Dawa-dawa ye basa nan?." Aisha da dadin soyayyar Abba ya kasa ankarar da ita Abba Mansura yake nema ta ce "Da Khadija da Rukayya da Jamila." Kai Abba ya jinjina. Zai yi magana Ahmad ango ya yafatoshi da hannu alamun ya zo su yi hoto."

Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Kin ga Ango na kirana ina zuwa." Aisha bin Abba ta yi ta ce "Yaya Abba muje a yi hoton dani."

Abba zuwa ya yi kafin a dauki hoton ya matsa kusa da Amina saitin kunnanta yadda babu wanda zai ji ya ce "Amina, Wai Ina yarinyar nan ne?."
Amina sai yanzu ta farga ba Mansura, waige-waige ta fara yi, ganin ba ta ganta ba ta ce ma Abba "Yaya Abba, tana cikin gidan ka Kira wayata tana hannunta."

Abba kallan Aisha ya yi ya ce "Minti daya ina zuwa zan yi waya."
Abba Matsawa ya yi ya Kira Mansura a waya. Mansura dake kwance tana danna wayar Amina tashi ta yi ganin Yaya Abba is calling. Amina picking call din ta yi tana sa wayar a kunnanta. "Kina nan kina aikin kukan naki ko?." Abba ya ce ma Mansura.

Mansura turo baki ta yi kamar Abba Yana kallanta ta ce "Kai Yaya Abba, Allah duk yau ban yi kuka ba." Okay ki fito waje yanzu Ina jiranki."

Mansura jimbur ta tashi ta fita, ita kanta Mansurar tana fita ta fara naiman Abba da idanunta. Can ta hangesa shi gefan ango da Amaya ga Aisha kusa da Abba ta nanike Mai ana hoto, ita ala dole bata son wata macan ta tsaya kusa da Abba.

Mansura karasawa ta yi tana murmushi ta gaida Ahmad, Ahmad da fara'arsa ya amsa ya ce "Babbar kawar Amarya ya hidima."
Mansura murmushi ta yi ta ce "Alhamdullah."

Ahmad nuna ma Mansura ya yi kusa da Amina ya ce "Zo mu yi hoto."

Mansura tsayawa ta yi kusa da Amina akadaukesu hoto su duka, da ita da Mansura da ango da Kuma abokin ango da Aisha.

Abba ya yi mamaki yadda Mansura ta dauke kanta daga shi da ta fito.

Da yake Amina ta rada ma Ahmad cewar ga wadda Abba zai aura wato Aisha ta nuna mai ita, dayake Ahmad ya san komai game da Aisha ita dince kawai baisani ba.

Ahmad kallan Aisha ya yi Yana murmushi ya ce "Aisha zo mu yi hoto." Haka suka yi hoton su hudu da Aisha da ango da Amina da Kuma Abba."
Bayan sun gama Ahmad ya ce ma Mansura itama ta zo su yi.
Babbar kawar Amarya da baban abokin ango da ango da Kuma Amarya su hudu kenan."
Chapter 23 · 0% Book details