← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 36

Sashe 5

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mama ni fa ban yadda har yanzu da yarinyar nan ba, babu wani kamshin gaskiya a kalamanta." Mahaifiyar Abba zuba ma Abba ido ta yi tana mamakin furucinsa, ta ce "Abbana, babu abinda ka rage a halin mahaifinka, tabbas na yadda barewa Bata gudu danta ya yi rarrafe, haka mahaifinka yake shima bashi da yadda, Amma in ba haka ba meye na karyata, ko yana yin halin da yarinyar kadai take na furgici da razana ai ya ci ya sa ka yadda da maganarta. Ni yanzu abin da nake so da kai ka yi hakuri mu barta ta zauna tare damu har zuwa wani lokaci, alabashi idan ta aikata wani abu Wanda ba mu gamsu da shi ba sai mu koreta."
"Tom ba damuwa mama, Allah ya sa mu dace." Abba ya fadi haka yana tashi ya nufi bangaransa.

Haka rayuwar Mansura ta ci gaba da wakana a gidan. Sosai Amina ke bakin ƙoƙarin ta wajan ganin ta jawo Mansura a jikinta ganin ta kauda Mata damuwarta, Amma Ina abin ya ci tura. Amina ko fira ta kawo ma Mansura da ido kawai take binta har ta gama. Amina ganin haka ya sa ta watsar da Mansura. Mansura Kuma ganin Amina ta watsar da ita sai ta dawo tunaninta, duk Kuma sai ta damuwa, dan tasan sosai Amina ke bakin ƙoƙarinta ganin ta sata farin ciki.

Mansura kallan Amina ta yi da ta yi banza da ita, yau tun da suka tashi bata tanka Mata ba, hakan ya sa Mansura ta ce "Amina yau tare za mu shiga kitchen kinsan ban iya girki ba Ina so ki koya min."
Amina da murmushi ta amsa ma Mansura dan tun da ta zo gidan magana mai tsayi ba ta taba shiga tsakaninsu ba sai yau. Hakan ya sa Amina da murnarta ta ce "Tom zo mu je mu yi girkin, dama yanzu nake shirin shiga kitchen din."

Koda suka shiga kitchen din, Mansura da kallo kawai take bin Amina inda ba iya girki ta yi ba, ko in zata dauki wani abun ta mika mata, a haka suka gama girkin. Tare suka ci duk da Mansura ba wani abun kirki ta ci ba.

Da daddare suna zaune babu mai cema kowa koma. Amina datse shirun nasu ta yi ta ce "Mansura gobe zan koma makaranta, hutun mu ya kare, da yake Ina koyarwa.
Yanzu idan na koma ya za ki yi Kinga mama Islamiya take zuwa, ke kadai za a rika bari a gida, ko in yi ma Yaya Abba magana ya sa ki a islamiyarsu mama zata debe miki kawar kadaici, ya fi mu tafi mu barki a nan ke kadai." A'a, ni dai bana so." Cewar Mansura.
"A'a Mansura ba zai yuwu ba a barki ke kadai, kadaici damuwa zai Kara Miki. Ina kika tsaya a school?." Diploma certificate garan.
"Yauwa, tom ko in ma Yaya Abba magana ke ma ko teaching ne ya Samar maki, inga kin huta zaman kekadai"
Mansura turo baki ta yi ta ce "Ni dai bana so."
Amina hakuri ta yi ta rabu da Mansura, haka Amina tai ta jan Mansura da hira, har ta ji Mansurar ta yi banza da ita alamun ta yi barci, dama Kuma daga, Eh, sai a'a, Mansura take yi a firar. Amina jin ta yi shiru alamun ta yi barci ya sa itama ta kwanta.

Washegari, Amina da wuri ta tashi ta yi masu abin breakfast. Bayan ta shirya, tada Mansura ta yi ta mika mata wayar ta ce "Dear ga wayata nan ta debe miki kewa." Tana Bata ta tafi.

Mansura ba ita ta tashi ba sai da ta ji yunwa na naiman takura mata kafin ta tashi ta yi breakfast, ta koma ta kwanta. Zaman kadaici sai ya je fa Mansura a duniyar tunani, inda gaba daya tunanin mahaifinta ya fado Mata rai. Mansura kuka ta fara, tun tana yi kadan-kadan har ta fara yi da karfi. tana cewa"Wayyo Abbana, Allah ka jikanka Abbana, Allah ya fe maka. Allah ba dan halina ba ina rokanka Allah ka samin nazuwa a rayuwata. Allah ka cire min damuwa da furgicin da ke damuna. Allah ka dandana min farin ciki koya yake kafin ruhina jikina ya yi ban kwana da gangar jikina nima. Wayyo Abbana." Mansura kuka take sosai da majina tana turje-turje tana Kiran Abbanta.

Abba da shigowarshi gidan kenan, tun kafin ya karaso yake Kiran layin Amina. Amma Mansura da yake kukanta take sha ko ringing wayar ma bata ji ba. Abba jin yadda Mansura ke kuka tana Kiran Abbana, da sauri ya yi bedroom din Amina, dan shi ya za ci ma Amina ce ke kuka. Abba cikin gigita ha hau kan bed din da Mansura take tana bubbuga kadon tun karfin tana Kuma Kiran Abbanta. Gashi Kuma ta kudindi ne kanta cikin blanket din. Abba da gaba daya ya manta da wata Mansura dan tun ranar da ya dawo da ita bai sake ganinta ba, hakan ya sa gaba daya ya dauka Amina ce. Abba da sauri ya kamo Mansura yana cikin tashin hankalin halin da ya ganta ci, ya ce "Amina, lafiya? Me ya same ki? Wa ya taba ki kike kuka haka?."

Mansura da gaba daya ta cukuykuye kanta da blanket , hakan ya Kuma batar da Abba itace, gashi dama kusan kirarsu daya da Amina.

Abba cikin jin haushi ya fara fada Yana cewa"Amina kashe kanki kike son yi ne da za ki cukuykuye kanki haka." Yana maganar yana ƙoƙarin fito Mata da kanta.

Mansura take natsuwa ta shigeta ta hadiye kukanta, ta yi tsit kamar an kashe inji.

Abba da mamaki da yake bin Mansura da kallo wadda idonta ya yi jajir tsabar kukan da ta yi. Abba cikin tausasa murya ya ce "Me akai miki?."
Mansura shiru ta yi tana yin kasa da kanta.
Abba dago kan Mansura ya yi ya, ya Kuma maimai ta Mata tambayar, "Me aka yi miki?."
Mansura goge hawayanta ta yi ta ce kamar za ta yi kuka, bakinta na rawa saboda tsoran Abba take. Cikin shashekar kuka ta ce "Abbana."
Shiru Abba ya yi yana kallanta, kafin ya ce " Ina Abban naki yake?."
"Ya mutu ya barni." Mansura ta fada tana Kuma fashewa da kuka. Abba cikin son kwantar mata da hankali dan ya san yadda mutuwar mahaifi take ya ce, "Ki yi hakuri kin ji, ba kuka ya kamata ki zauna kina yi masa ba. Abbanki bai yi gaggawa ba lokacinsa ne ya yi, addu'a ya kamata ki rika yi masa. Daga yau Kar in Kara ganinki kina Mai kuka, Kin ji ko?." Kai Mansura ta daga tana goge hawayanta.
"Yauwa, good girl."
Abba sauka gadon ya yi ya na cewa "ki shiga kitchen ko taliya inda tafi sauri ki dafa min, zan yi bako, dama Amina na yi niyyar sawa tom na zo Kuma ashe ta yi resume school yau, ki yi sauri dan Allah." Abba ya fadi maganar yana fita. Ba tare da ya bata damar cewa komai ba.

Mansura turi baki ta yi ta ce "Ni ai ban iya girki ba." Mansura ta ce tana sakkowa daga kan bed din.

Kitchen ta nufa, tana zuwa ta samu tukunya ta kusa cikata da ruwa, sannan ta zuba mai ya kusa kwalba, ba soyawa ba komai, ta daddaka tarugu da albasa suma ta wasa. Ruwan ko zafin kirki bai yi ba ta zuba taliyar. Magi ko duk magin da ke kitchen din babu Wanda ba ta sa ba, stone fishi din da ta gani shima ta dauka ta maka a ciki. Ta zauna zaman jiran ruwan taliya ya kone ta sauke taliyar.
Taliya sai da ta zama kamar fate kafin Mansura ta sauketa. Ta dakko Plate ta zuba.

Bangaran Abba, abokinsa har ya iso, Abba kayan sanyi ya fara kawo ma abokin nasa, kafin ya nufi bangaransu Amina zuwa dakko girkin Hajiya Mansura.

Abba kitchen din ya je inda suka ci karo da Mansura da ke ta ƙoƙarin fitowa. Abba da kallo ya bita ya ce "Ina abincin fa?."
Mansura plete din taliyar ta dakko ta mika ma Abba tana addu'ar Allah ya sa ya yi masu dadi.

Abba amsa ya yi ya ce "Thanks."

Yana zuwa ya aje ma Ahmad ya ce"Bismillah." Masoyiyarka ce, Taliya.
Ahmad murmushi, kafin ya ce , "Na Kira number Amina Bata daga ba ko za ka Kira min ita." Ahmad ya fadi maganar cikin damuwa.
"Kasan ta fara koyarwa, ba a dade ba na naiman manta koyarwa a wata primary nan kusa damu. Tom yau a gida ta bar wayar nima na kirata bata daga ba sai da na shiga naga wayar tata."

Ahmad shiru ya yi bai ce komai ba. Abba Kuma Abincin ya Kara mika ma Ahmad ya ce "Ka ci abinci mana." Ahmad langabar da Kai ya yi ya ce "Zanci, Amma kafin sai na amayar maka da abin da ke cikina, inda Kai dan iska ne ka kasa fahimtata. Usman, ina son Amina ba tun yau ba, dan na jima da gabatar da kaina a wajanta, yanzu haka nai man aure na zo."
Abba da mamaki ya kalli Ahmad ya ce "Wai da gaske?Kana yawan min maganar Amina Amma Wallahi ban taba kawo haka ba, sai na ga kamar ta yi Karama." Ahmad hararsa ya yi ya ce "Tsohuwa kake so in aura kenan."
"Yanzu dai ba haka ba, ka ci abinci sai mu je makarantarsu Aminar."

Ahmad bude taliyar ya yi, ba tare da tunanin komai ba ya diba tare da yin Bismillah ya afka a bakinsa cike da saukin maganar Amina da ya zo da ita, sai dai Ahmad duk yadda ya so ya daure ya hadiye abincin kasawa ya yi, ga uban yaji ga Magi bau. take ya furzar da abincin. Abba Kuma bai kawo komai ba a tunaninsa Ahmad kwarewa ya yi, hakan ya sa ya diba shima ya Kai bakinsa, ai har gara Ahmad ma Abba da gudu ya ruga toilet dinsa ya zubar da abinci ga uban shakewa da ya yi tsabar tsananin yajin da ke cikin taliyar. Abba da kyar ya samu kansa bayan ya kwankwali ruwa.
Chapter 5 · 0% Book details