Sashe 30
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba bayan sun fita motarsa ya bude ma Aisha front seat ya ce "Shiga muje babu musu Aisha ta shiga. Bayan Aisha ta shiga Abba kallanta ya yi ya ce "Mommyna meye damuwarki da auran Mansura da zanyi? Idan ma baki so ku zauna gida daya sai ki zabi inda kikeso in ajeki ko nan gidan ko Kuma gidan da na gina."
Aisha kallan Abba ta yi da idanunta dake zubba da hawaye ta ce "Yaya Abba dan Allah ka fahimceni ba zan iya kishi da Mansura bane, saboda nasan kana sonta fiye Dani, impart ita kake so bani ba, taya zan hada kishi da ita, bannaima ma kaina kwanciyar hankali bama idanna yi haka. Tursasani Kuma da kake so ka yi in amince maka kana yi ne Yaya Abba kawai dan ka guje ma fadan mama bawai dan kana Sona ba, Yaya Abba dan Allah mu fahimci juna Wallahi da gaske nake na kura dakai zan yi ma Mama bayani nice bana sonka Ina da Wanda nake so."
Abba ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan indai haka ta faru baya tunanin zai Kara ganin hakorin mahaifiyarsa, hakan ya sa Abba ya kalli Aisha ya ce "Idan na fasa auran Mansura shi kenan kin hakura zaki auran?."
Aisha da mamaki ta kalli Abba jin abinda ya ce. Abba Kai ya daga ma Aisha ya ce "Da gaske nake zan fasa auran Mansura idan har zaki janye kudirinki."
Aisha runtse ido ta yi jin abinda Abba ya ce, ko a mafarki Aisha bata taba tunanin Abba zai iya haka ba akanta, tunani ta fara anya ko ba gudin bacin ran mahaifiyarsa ya sa shi in yi haka ba, wata zuciyar ta ce Mata in ma yakasance haka ne zai kula dake kenan ko bayan aure saboda gudin bacin ran mahaifiyar tasa kenan.
Aisha kallan Abba ta yi ta ce "Yaya Abba nasan baka sona karka yaudari zuciyata dan Allah, ka fadamin me ya sa ka zabeni akan Mansura? Bacin nasan Mansurace zabinka?."
Abba shiru ya yi yana kallan Aisha, azuciyarsa ya ce tabbasa Mansura ce zabina. Afili Kuma ya ce "Mommyna, auran Mansura ni kadai nake maganarsa Amma mama taki aminta in aureta, Kinga idan na bari kika sukubuce min na yi biyu babukenan."
Aisha sosai ta gamsu da hujjar Abba, hakan ya sa ta ce "Shi kenan Yaya Abba na fasa dama zan tursasa zuciyatane rabuwa da Kai ba wai danna daina sonka ba."
Abba murmushin jin dadin nasara ya yi ya ce "Yauwa my love har hankalina ya kwanta."
Abba na fadin haka ya tada motar suka tafi, suna tafiya suna hira har suka kai gidansu Aisha. Abba hira suka yi yau sosai da Aisha wadda basu taba irinta ba, Aisha bata taba jin ta gamsu da auran Abba ba sai yau, ji take kamar an cire mata wani nauyi a kanta.
Abba bayan sun zo kofar gidansu Aisha kallan Aisha ya yi ya ce "Gamu a kofar gidanku, shi kenan in wuce?." Aisha kai ta girgiza ma Abba ta ce "Ka shiga ka gaida Malama kafin." Aisha ta fadi maganar dan ta ji abinda Abba zaice inda tasan Malama bata gida tana makaranta.
Abba kayan jikansa ya duba ya ce "Kalli fa kayan dake jikina, gaskiya ba zan iya zuwa da k'ananan kaya ba." Aisha bata rai ta yi ta ce shi ya sa Wallahi na ce zan fasa auran baka sona gashi nan ko mamana baka taba gaidawa ba."
Abba da a halin yanzu babu abinda ke tata mai hankali kamar Aisha ta ce zata fasa auransu, dan yasan mahaifiyarsa ko bata tsinenemai ba tom kadanne, inda ta ce ko bayan ranta in bai auri Aisha ba bata yafe ba.
Abba cikin sanyi da son nuna ma Aisha ba haka bane ya ce "Mommyna so nawa Ina fada maki bani da lokaci in ba rana irinta yau ba, yanzu ki bari da daddre Zan zo sai in gaidata ya yi Miki?"
Aisha damamaki ta ce "Da gaske zaka zo da daddre ka gaidata?." In sha Allah, ki kirani ki tuna min."
Aisha yau cikin farin ciki suka rabu da Abba, soyayar Abba ko ta Kara nunkuwa a zuciyarta.
Abba lokacin da ya shiga gida ya iske mahaifiyarsa harta dawo, saidai ita kadaice a falon babu Mansura.
Abba fita ya yi ya Kira wayar Mansura, har ta katse bata daga ba saida ya sake Kira. Mansura daga wayar ta yi tana kangata a kunnanta. Abba cikin sanyi ya ce "Man's, gani na dawo ki fito falon Mama plz."
Mansura kamar zata fasa kuka ta ce "Yaya Abba dan Allah ka rabu dani ka kyaleni." Abba shiru ya yi jin Abinda Mansura ta ce, Abba cikin damuwa ya ce "Man's ki yi hakuri nasan akan Aisha ne, idan ban yi haka ba Mama zata yi fushi dani kito fito dan Allah yanzu kin ji."
Abba na fadin haka ya kashe wayarsa ya koma falon mahaifiyarsa, amma har ya gama zamansa Mansura bata fito ba, dole ya hakura ya fita gidan baki daya.
Gaf magariba Aisha ta Kira Abba ta tuna mai zuwa gidansu, Abba kamar ya ce ba za shi ba, amma Kuma Yana tsoran ya yi ma Aisha laifi hakan ya sa bayan ya dawo sallar magariba ya shirya cikin wata brown din shadda ya yi kyau sosai ya shigo falon mahaifiyarsa.
Zaune Abba ya iske mahaifiyarsa da Mansura suna hirar Amina da suka gama waya da ita yanzu. Abba cikin sanyi dan yanzu gaba daya mahaifiyar tasa ta canza mai ya ce "Mama zani gidansu mommy zan gaida iyayanta." Tom ka dawo lafiya." Mahaifiyar Abba ta ce.
Abba fita ya yi yana kallan mansura da ta sadda kanta kasa. Abba fita ya yi ya Kai Koda ya juyo suka yi ido hudu da Mansura, murmushi Abba ya sakar mata ya tafi.
Abba na gaf kaiwa gidansu Aisha ya kirata a waya ya sanar da ita zuwansa.
Aisha daketa rawar Kan Abba na ji da ita yanzu, mahaifiyarta ta samu ta shaida Mata Abba na nan zuwa gaidata.
Mahaifiyar Aisha da alamun mamaki a fuskarta ta ce "Abban ne zaizo gaidani?." Kai Aisha ta daga ma mahaifiyarta tana murmushi. Mahaifiyar Aisha kallan Aisha ta yi ta ce "Kin janye maganarki kenan ta fasa auran." Aisha dariya ta yi ta ce "Malama ai yanzu mun fahimci juna." Aisha suna cikin magana da mahaifiyarta Abba ya kirata ya sanar da ita ya karaso. Aisha kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Malama, bari in je in taho da shi." Aisha na fadin haka ta fita.
Abba da ya shigo bayan ya gaida mahaifiyar Aisha har falon mahaifin Aisha aka kaisa ya gaidata kafin ya yi masu sallama ya tafi, bai biyema Aisha sun yi fira ba, Yana fitowa ya kalli agogon hannunsa ya ce "Mommyna dare ya yi bari in tafi." Tom Yaya Abba Allah ya tsaremin Kai cikin tsarewarsa."
Abba bayan ya koma gida da ya shigo mahaifiyarsa bata falo hakan ya sa ya nufi badroom dinta.
Abba sallama ya yi, yadda mahaifiyarsa ta amsa mai ya sanar dashi ta fara sakkowa. Abba zama ya yi Yana Bata labarin karamcin iyayan Aisha da tattakonsu. Mahaifiyar Abba cikin jin dadin hirar ta ce "Haba ai baka ga komai bama sai in Allah ya yi auranka da Aisha, zaka san ka yi aure gidan mutunci."
Abba dai murmushi ya yi. Kafin Abba ya ce "Mama dama akan Mansura ne, baki ganin indan mun yi aure da ita zata sanar da ni ahalinta, saboda mama idan zaki kalli Mansura bata da wata wani mugun hali ko rashin da'a ko dabi'a, daga ganinta duk inda ta fito ta samu tarbiya daidai ta addini musulinci, Kuma Wallahi mama inaji ajikina akwai alkairi sosai a aurena da ita."
Mahaifiyar Abba kallan banza ta yi ma Abba ta ce "Nima bance babu alkairi ba, Amma Abba indai ka ga ka auri Mansura ba tare da ahalinta ba saidai in bana raye, idan tana da gaskiya meye abin tsoro a sanin a halinta, tom Wallahi Koda wasa ka karamin maganar nan sai na bata maka rai, idan yau ka je ka ga a halinta na amince ko a ranar ka aureta."
Abba shiru ya yi baice komai ba ya ja bakinsa ya yi shiru, ƙarshe ya tashi ya fita.
Abba na fita bedroom din mahaifiyarsa ya yi wuf ya tura badroom din Mansura ya shiga.
Lokacin da ya shiga bata dakin, Abba na zama ita Kuma ta fito daga toilet. Mansura karasawo inda Abba yake ta yi ta zauna kan abin sallayar da ta yi Sallah. Abba bakin bed din Mansura ya nuna Mata ya ce "Zo ki zauna magana za mu yi."
Mansura tashi ta yi ta je ta zauna kusa da Abba, Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Mansura, saura wata biyu bikina da Aisha, ina so in aureki kafin Aisha idan kin amince, amma Kuma auran sirri nake so mu yi bana son kowa ya sani har Amina bana so ta sani."
Mansura Kai take girgiza ma Abba ta kasa magana, da yake bata da wuyar kuka goge hawayan da ya fara zubar Mata ta yi ta ce "Aure Kuma Yaya Abba, auran ma na sirri? A'a gaskiya ni ba zan iya haka ba, ba zan taba amincewa ba Yaya Abba."
Abba shiru ya yi Yana kallan Mansura dake furta kalmar haka ba zai taba yuwu bama Ina.
Abba cikin sanyi ya ce "Mansura ke kanki zakifi samun natsuwa, na tabbata auran zai rage miki wannan damuwar da kike cikinta, ki yi tunanin magata akwai alkairi sosai a cikinta."
Mansura Kai ta girgiza ta ce "Yaya Abba dan Allah mu b.." Abba rufe ma Mansura baki ya yi jin Mahaifiyarsa na Kiran Mansurar tana cewa "Mansura badai kin yi barci ba zo ki bude min.. ... ✍🏻
Littafin Abba na kudine, 400 kacal kafin in gama free pages daga na kammala zai koma 500 my number 08063830828.
Fadila Sani Bakori ce
⭐ ABBANA ⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r
P 37-38