← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 36

Sashe 21

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansura bayan ta tafito wanka ta dauki daya daga cikin kayan Amina za ta sa inda dama kayan Aminar take sawa. Amina dake zaune kusa da Mansura hararta ta yi kafin ta wurga Mata wata farar lifaya wadda adonsu ne kawai ya banbanta da tata, ta ce "Ga wadda za ki sa nan."
Mansura da mamaki ta kalli Amina tana son yin magana Amina ta yi Mata nunu da mutane cikin dakin, hakan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Wadda ta yi ma Amina kwalliya ita ta yi ma Mansura ta nada Mata lifayar. Wayyo mutane rasa Wanda ya fi kyau suka yi tsakanin Mansura da Amina, idan ka gansu zaka dauka su duka amaran ne. Amina ko da bata taba ganin Mansura da kwalliya ba sosai ta rude ganin yadda Mansura ta yi Mata kyau kamar ka saceta ka gudu. Wasu da dama kance Mansura ta fi masu kyau, wasu Kuma suce Ina ma za a hada Amarya ai dabance.

Nan fa aka yi ta yi masu hotuna. Aisha ta tasha adonta cikin wani green hijab, duk sai ta sha jinin jikinta ganin yadda Mansura ta sha kyau kamar ita ce amaryar.

Hutuna akaita daukarsu Amina, Wanda duk abin da ake Mansura na yake ne kawai, amma bi ainihi jitake kamar ta fasa ihu, amma ta daure ta cije dan karta sama kawarta damuwa.

Hassana da itama tasha adonta da Hajiya babba sosai ta yi kyau, jawo hannun Aisha ta yi suka bar falon Abba da yake acan suke shirin nasu.
Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha in fada miki gaskiya kin yi kyau, amma shegiyar yarinyar nan ta fiki, ke bakya kishin Yaya Abba ya ganta haka, wai ke ko kunshin ma kinkasa yi."
Aisha kallan hannuwanta ta yi ta ce "Ki bari kinsan Mommy ta dauki nauyin walimar nan tom aiki ya yi yawa, saidai gobe zan je a yi min da wuri, inda na ji ance sai lahadi za a kai Amarya ba ranar da aka daura aure ba."
Hassana shiru ta yi ta ce "Shi kenan, Amma dai ki kula kema gobe ki yi wankan kece raini." In sha Allah ." Aisha ta ce tana kama hannun Hassana ta ce zo muje mu yi hoto da Amarya."

Hassana da yake duk kawayansu daya da Amina kusan, hakan ya sa duk sai da ta bisu ta rada masu su yi hankali da Mansura maciyiya Amanace tana naiman kwace ma kawarta Aisha saurayin da zata aura, hakan ya sa duk sai suka rika yi ma Mansura kallan munafuka, sukaita sakar mata habaici. Amina tana so ta yi masu magana amma Kuma bata son Mansura ta ji tana musu magana inda ta ga kamar bata barga da ita suke ba. Mansura ko tasan ta ita suke saidai damuwar da take ciki ya sa bata maida hankali akan habaicin nasu ba, dan bisa ga alama ma ba ta su take ba.

Aunty Zainab ta shigo bangaran Yaya Abba inda kawayan Amarya da Amarya suke. Aunty Zainab kallan Mansura ta yi cikin fada-fada ta ce "Mansura me kuke yi ne tun dazu gashi can har an fara gabatar da Malamai bakwanan."
Mansura cikin sanyi ta ce "Afuwa Aunty Zainab, bamu san amfara ba."
Mansura kama hannun Amina ta yi kawayan duk suka rufa masu baya suka fita.

Suna zuwa aka gwada masu inda zasu zauna.

Take Malama Safiya ta fara wa'azi akan falalar dake tattare da aure, menene aure, waya ce ai yi shi, da Kuma darajar da yake tattare da ita. Bayan ta gama dogan bayani, ta kuma koma magana akan hakin dake rataye akan mace akan mijinta. Take jikin mutane ya yi sanyi. Bayan ta gama taba Malama Farisatu wadda ta fara bada kisa akan yadda Nana Khadija ta zauna da ma'aiki S.A.W. jikin Amina sanyi ya yi da yake babu wuyar kuka take ta fara kuka wadda ita kanta bata san me ya sa ta kukan ba.

Mansura da dama kiris take jira, take itama ta ji kukan na niyyar kwace Mata, hakan ya sa da wayau Mansura ta bar gun kamar tana sosa ido kamar wani abu ya fada mata a ido.

Mansura can bayan window Abba ta je inda tasan babu wanda zai ganta ta duka a wajan ta fashewa da kuka. Mansura kuka take sosai har tana jan ajiyar zuciya irin na wanda ya gaji kuka ya yi yinsa.

Mansura sai ji ta yi an dago kanta. Dago fuskarta ta yi wadda ta dame gaba daya saboda kuka. Abba bai cema Mansura komai ba handkerchief dinsa ya ciro yana goggo ma Mansura hawayanta. Sai dai ya gama kafin ya kama hannunta ta tashi daga duken da take.
Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Kalli yadda kika bata kwalliyarki, Haba Mansura ba za ki iya hakuri ki adana duk damuwarki ba har Amina ta bar gidan nan ba kamar yadda na ce maki ko? Kuma ahaka ne kike cewa ke bakya son komai kin fi so a barki ki ci gaba da zama gida, ai dole ma in sama maki abin yi idan aka gama hidimar bikin nan." Abba shiru ya yi yana kallan Mansura dake sauke ajiyar zuciya akai-akai, kafin zuwa can ya ce "Kin ga kin bata kwalliyarki, zo muje ki wanke fuskarki ki koma wajan walimar Kinga Amina yanzu zata kasa natsuwa idan ta fahimci baka wajan.

Abba shigowarsa kenan ya shiga bangaransa ya dakko kayansa da zaisa gobe ya ci karo da kukan Mansura bayan window shi.

Can bangaran Hassana ko ganin Abba ya shigo Mansura Kuma ta tashi ta yi bangaran nasa, Wanda basu san ita bata san shigowarsa ba, inda ita a saninta kamar yadda mama ta ce sai taro ya watse zai dawo da kwana gidan, hakan ya sa ita ba ta yi tunanin yana gidan bama. Hassana ganin haka radama Aisha ta yi, yarinyar can ina jin wajan Yaya Abba zata, Kinga ta yi bangaran da muka shiga dazu, ba ance nan ne sight dinsa ba, zo muje mugani idan ya tabbata hakane Wallahi mu taru mu taka Mata burki." Hassana dakyar ta samu Aisha ta yadda ta bita, dan ita Aisha bata son ganin abinda zai bata mata rai, Amma kamar yadda Hassana ta ce mata wai zata kafa hujja ne.

Lokacin da Aisha suka iso wajan su Abba sun shiga falonsa kenan shida Mansura yana rike da hannun Mansurar.
Hassana kallan Aisha ta yi ta ce "Kinga abinda nake fada miki ko? Yanzu Kinga ya kama hannunta sun shiga dakinsa, lallai Allah ya sa wannan ma ba wani mugun abin suke aikatawa ba."
Aisha tsabar kishi kasa magana tayi sai hawaye dake zuba daga idanta. Suna nan tsaye sai ji suka yi an daba su. Hassana da sauri ta waigo tana kallan Khadija ta ce "Khadija lafiya?." Nazo wucewa ne na hangoku da fatan dai lafiya na ga Aisha na kuka?." Hmmm Ina fa lafiya ana shirin kwace mata Wanda zata aura." Nan Hassana ta kwashe komai ta fada ma Khadija. Khadija wani uban ashar ta yi ta ce "Yanzu kunsan yadda za yi ke Aisha ki tsaya acan yadda ba zai ganki ba, Hassana mu Kuma zo muje da sunan mun zo daukar Abu inda dai yasan nan muka zauna muka shirya, mu shiga mu gani."

Aisha inda suka ce Mata ta tsaya tana jira, inda Hassana da Khadija suka tusa kansu cikin falon Abba ba tare da sun yi sallama ba.

Abba Kuma daidai ya kama ✍🏻

Fadila Sani Bakori

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 25-26

Abba daidai yana taimaka ma Mansura wajan gaya nadin Lifayarta su Hassana suka shiga. Ganin Abba da Hassana sai suka yi kamar marasa gaskiya, Abba Kuma kota kansu bai bi ba haka Mansura ma ci gaba da tayata ta gyara nadin Lifayarta ya yi.
Kallan Hassana da Khadija ya yi da suka ja suka tsaya sukai kai kuri ya ce "Lafiya?." Khadija cikin wayancewa ta ce "Mansura dan Allah ba ki ga handbag dita ba kamar anan na barta." Ku shigo ku duba Mana. Abba ya ce yana kamo hannun Mansura suka fita. Khadija da Hassana rike baki sukai suna kallan juna. Khadija ta ce "Lallai maganarki gaskiya, wannan ma ai ya wuce soyayya sai dai abarshi layin iskanci, in ba iskanci ba lifaya fa yake tayata nadawa." Hassana dai tsabar al'ajabi ta kasa magana sai zuwa can ta ce "Tab dijam, inko hake ne akwai aiki a gaban Aisha babba ." Khadija Kai ta jinjina ta ce "Wani Anya ko Yana ma wani son Aishar kuwa?." Ke bisa ga alama fa Yana sonta, munafukar yarinyar nan ce ke son yi mai kutse cikin rayuwa, ni yanzu tunani na daya yadda za mu yi mu taimaka ma kawarmu dan idan har muka ce ta bar mata shi ai ta shadamu gara mu nuna Mata ita karamar Yar iska ce."
Hassana koma hannun Khadija ta yi ta ce "Muje Aisha na can tana jiranmu."

Har suka koma Aisha na kuka dan taga fitowar Abba rike da hannun Mansura yana mata magana mai kama da lallashi.
Hassana dafa Aisha ta yi ta ce "Tabbas abin da zafi Wanda kake so ka bashi Amana ka ganshi yana cin amanarka, amma ki yi hakuri sai yarinyar nan ta yi fiye da kukan da kika yi. Yanzu muje ki wanke fuskarki Kar a ganema kin yi kuka."

Aisha zuwa ta yi ta wanke fuskarta kafin suka koma wajan walimar inda suka iske Mansurama zaune kusa da Amarya. Kasan cewar an gayyato malamai mata da yawa hakan ya sa anjima ana walimar kafin aka rarraba abun rabon da mahaifiyar Aisha ta yi kafin aka watse daga walimar.
Chapter 21 · 0% Book details