Sashe 6
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahmad kallan Abba ya yi ya ce "Usman wa ya yi wannan girkin haka?." Hmmm, Wallahi wata sangartattar yarinya ce, mu je restaurant mu ci abinci."
Restaurant mai tsada Abba ya kaisu suka ci abinci. Kafin suka nufi makarantar da Amina ke koyarwa. Amina da mamaki ta bi Ahmad da kallo dan ko jiya sun yi waya da shi Amma bai fada Mata zai zo ba. Amina ba sarwa ta yi ta ce "laa, Yaya Ahmad, yaushe ka zo?." Ahmad maimakon ya Amina amsa motar Abba ya nuna Mata ya je mu je."
"Ina zuwa bari in zo."
Amina cikin makarantar ta koma ta sanar da headmastern makarantar kafin ta fito suka tafi.
"My Meena , ya hayaniyar yara." Alhamdullh ya Ahmad ya hanya." Lafiya lau."
Amina Koda suka shiga gida, hannu kawai ta daga ma Mansura ta shige bathroom ta watsa ruwa da sauri ta fito. A gaggauce Amina ta Sha fa lotion dinta, ta jira doguwar rigar lass dinta.
Mansura kallan Amina ta yi ta ce "Dear, unguwa za ki kika sha gayu haka."
Amina zama ta yi kusa da Mansura ta ce "Dear Ina Wanda kike ji muna waya da shi kullum, shi ne ya zo abokin Yaya Abba ne."
"Okay, dazu ko Yaya Abba ya sani na yi masa girki Allah ya sa ya yi masa dadi ma." Ameen, tashi mu je ku gaisa."
Mansura shiru ta yi Amma har ga ranta ba ta ji dadin zuwan ba. Amma ba ta iya musa ma Amina hakan ya sa ta tashi suka fita tare suka nufi bangaran Abba, tana sanye da brown abaya a jikinta. Da sallama suka shiga in da suka iske Abba da Ahmad zaune suna hira.
Mansura cikin girmamawa ta gaida Ahmad, sannan ta juya da sauri za ta tafi. Amina rike mata hannu ta yi ya sa ta dakata.
Abba Kuma tashi ya yi ya basu waje.
Amina kallan Ahmad ta yi ta ce "Ga sabuwar sisterna da nake baka labari." Ahmad cikin fara'arsa suka gaisa da Mansura. Mansura Kuma da ta jita duk a takure tashi ta yi zata tafi ta ce "Dear bari in shiga ciki."
Amina plate din taliyar da Mansura ta dafa ta gani, Wanda tana gani ta fahimci girkin da Mansura ta fada Mata Yaya Abba ya sa ta yi ne. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Dear ki tafi da kayan nan."
Mansura dawowa ta yi ta dauki plate din abincin.
Abba Kuma falon mahaifiyarshi ya dawo ya zauna wanda da itama shigowarta kenan. Kallan Abba da ta yi ta ce "Abbana, ya na ganka Kai kadai bayan na ga mota a gidan."
Murmushi Abba ya yi ya ce "Yarki ce ta yi bak'o."
Kai mahaifiyar Amina ta jinjina, ta ce "Aminar ta yi bak'o bani da labari, hala Kai ta fada maka ne?."
Abba gurin zama ya nuna ma mahaifiyarsa ya ce Mama zauna ki ji."
Mama na zama Mansura ta yi sallama ta shigo rike da plate din taliyar da ta dakko.
Mansura kallan Mama ta yi ta ce"Sannu da dawowa Mama." Tana fadin haka ta juya za ta tafi.
Mama kiranta ta yi ta ce "Mansura a binci ne a plate din nan?."Eh Mama taliya ce." Mansura ta bata amsa.
"Yauwa bani in ci."
Mansura mika ma mahaifiyar Amina taliyar za ta yi Abba ya kalli Mansura ya ce "Ke kin ci ne?."
Kai Mansura ta girgiza.
Abba waje ya nuna ma Mansura ya ce "Zauna ki ci."A'a na koshi." Mansura ta idasa maganar tana mika ma Mahaifiyarsu Abba plate din taliyar.
"Diba ki ci." Abba ya umarci Mansura. Mansura ba tare da gaddama ba ta yi 1 spoon. Tun shigar taliyar bakinta tasan an samu matsala, duk yadda ta so ta daure ta hadiye ta bakinta kasawa ta yi, hakan ya sa ta furzar da taliyar a hannunta, tana ya mutsa fuska, ga uban ya ji da har kwakwalwarta sai da ta amsa.
Mansura tagowa ta yi ta kalli Abba Wanda shima ita yake kallo✍🏻
Fadila Sani Bakori ce.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LGosWoHsPkj3rhf9EbKjrK
⭐ABBANA⭐
🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
Daga Marubuciyar 👇🏻
*Oga Habin
*Fadeela
*Meenalyn Daddy
*In da rai
*Abdurrahim
*So ne sila
*Bakin kishi
P 7-8
Abba a natse ya ce ma Mansura "Ke da kika dafa kinkasa ci Ina ga mu." Sannan ya maida kallanshi ga mahaifiyarshi ya ce, "Mama, dazufa na dawo gida dan sa Amina ta yi man girki, na iske bata nan, shi ne fa na sa yarinyar nan, shi ne ta dafa taliyar nan"
Abba kallan Mansura ya yi ya ce "Shi kenan, za ki iya tafiya, dama na sa ki ci ne dan ki ji kalar abin da kika dafa ma mutane"
Mansura da sauri ta tafi tana turo baki.
Bayan ta tafi, Mahaifiyar Abba, kallan Abba ta yi ta ce, "Haba, Abbana haka ai gwalisa ne, ina laifin Wanda kaba aiki ya tashi ya yi maka."
Abba dai bace kala ba, ya canza firar da cewa" Mama, Ahmad fa naiman aure ya zo, wai Amina yake so, so na aure."
Murmushi mahaifiyar Abba ta yi ta ce "Abba akwai son da ba na aure bane, ni dama ba tun yau ba na fahimci yaron nan yana son Amina. Amma gaskiya na ji dadin jin labarin nan, dan Ahmad yana da hankali sosai. Don haka, babu abin da zance sai dai fatan alkairi in da itama Aminar na fahimci tana sonsa, dan na dade da fahimtar suna waya."
Abba Kam mamaki ya yi dan bai taba dauka haka ba. Abba sun dade suna fira da mahaifiyarsa kafin Kiran Ahmad ya shigo wayarsa. Abba na dagawa Ahmad ya ce "Mama nake so ka zo ka yi min iso in ingaida, ka ga yanzu ta zama sirikata kunga nake ji." Malam, bana son kinibibi, Ina ita Aminar take ? Ta rakoka Mana." Abba na fadin haka ya kashe wayarsa.
Amina ita ta yi ma Ahmad iso ya zo ya gaida mahaifiyrata har falonta. Ahmad dai ya kasa sakin jikinsa kamar yadda ya saba da.
Mahaifiyar Abba kallan Amina ta yi ta ca"Tom lokacin Sallah ya yi maza ki je ki yi."
Bayan Amina ta bar falon ne, mahaifiyar Amina, ta kalli Ahmad ta ce "Ahmad, na ji wani sako wajan Abba, Kuma ya yi min dadi sosai, Ina muku fatan alkairi."
Ahmad cikin jin kunya ya amsa da "Ameen."
Kafin ya yi ma Mata sallama dan yau zai koma. 10k ya ciro a ajjihunsa ya aje ma mahaifiyar Amina. Bayan sun fita Abba ya kallai Ahmad ya ce "Yanzu sai k.d, kenan?." Bari kawai, kasan na dade ban je gida ba wannan Karan......."
Su Abba sun jima suna tattaunawa kafin Ahmad ya Kira Amina suka yi sallama. 10k itama ya faba ya tafi.
Haka rayuwar Mansura ta ci gaba da wakana a gidan har ta fara sakin jikinta, amma duk da haka dai da wuya ka yi doguwar hira da ita.
Yau ya kama weekend, mutanan gidan duk suna gida. Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Dear ki shirya ki rakani Mama zata aike mu Mani wajan Aunty Zainab, za mu Kai Mata magani, da yake tun da kika zo ba ta zo ba, ita ke bima Yaya Abba, da yake tsohon ciki gareta Kuma tana shan wahala shi ya sa mama ta hanata zuwa sai ta haihu. Mansura shiryawa ta yi cikin daya daga cikin kayan Amina suka fito za su tafi. Inda suka iske Abba zaune a falon.
Mahaifiyar Amina kallan Amina ta yi ta ce "Har Kun shirya?." Maganin ta dauka ta mika ma Amina ta ce "ku bata ,na yi Mata bayanin yadda za ta yi amfani da shi a waya."
Amina har sun juya za su tafi, Abba ya ce "Karku Kai dare."
Misalin karfe 10 su Amina suka shiga gidan Aunty Zainab. Amira murna ta yi sosai ganin Amina. Kallan Aunty Zainab ta yi tana nuna Mansura ta ce "Mommy kinga Mommy mai kuka da nake baki labari."
Aunty Zainab da ke zaune da katoton cikinta, kallan Mansura ta yi ta na murmushi ta ce "Sanninku da zuwa Mansura, sai yau Allah ya yi za mu hadu."
Mansura murmushi ta yi ta ce"Yauwa Aunty Zainab ya karfin jikin." Alhamdulillahi."
Amina kallan Aunty Zainab ta yi tana turo baki ta ce "shi kenan, in da ni baki ganni ba."
Dariya Aunty Zainab ta yi ta ce"Na isa ince ban ga autar mama ba. Haushi kika ban, Amina tun ranar fa da za ku Kaduna rabona da gida sati na 7 muke kenan. Amma shine ko kilekoni, yanzu ma nasan da mama ba ta Aiko ki ba da ba ganinki zan yi ba. "Aunty Zainab, sai ka ce kin manta waye Yaya Abba." "Ba wani Yaya Abba, ki ce dai kin samu k'awa kin rabu dani, idan kina son zuwa bani kike sawa ba in yi ma Abban magana ba." Tom Auntyna Afuwa, ba zan sake ba." Yanzu dai bani da wani abu na ci, ke Kuma Amina na San ba son abinci mai aiki kike ba, ni Kuma lallura tasa na Bilki nake ci, idan ba za ku ci nata ba ku shiga kitchen ku girka Mana baki daya."
Su Amina sun jima suna fira da Aunty Zainab da yake mai firace, kafin Amina ta tashi ta shiga kitchen ta yi masu jallop din cous-cous.
Amina ba suka fito gidan Aunty Zainab ba sai da aka yi sallar la'asar. Suna fitowa suka ga garin ya yi bakikkirin na hadari, tsananin hadarin da Aunty Zainab ta gani ya sa ta hanasu Amina tafiya. Ruwa aka yi sosai, sai 5 ruwan ya tsaya. Aunty Zainab babu yadda ba ta yi da su Amina su tsaya su kwana ba Amma Amina taki.