← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 36

Sashe 25

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin Abbana na kudi ne, wa inda suka biya kafin ingama free pages 400, daga na gama 500 zai koma, my number 08063830828.

Fadila Sani Bakori ce.

⭐ ABBANA ⭐

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*

Domin samun littafin ABBANA daga farko 👇🏻Follow the ABBANA channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaYZGsNEFeXsr1CKQl3r

P 29-30

Abba dakatawa ya yi da abin da wakar ganin Mansura ta yi kasa da kanta tana kuka, gabadaya sai Abba ya ji rauni shima, hakan ya sa yakama hannun Mansura yana rungumarta suka bar cikin hall din da sauri.
Abba inda ya yi parking din motarsa ya nufa da Mansura, cikin motarsa suka shiga, Abba kallan Mansura ya yi da har yanzu hawaye ke zuba a idanunta. Handkerchief dinsa ya ciro ya dago kan Mansura dake kafadarsa ya fara goge ma Mansura hawayanta, ya ce "Kinmanta alkawarin da kika yi min kenan." Abba ya ce yana kallan Mansura da har yanzu hawayanta bai tsayaba.
Mansura hannu tasa tana goge hawayanta.
Shiru Abba ya yi yana kallan Mansura da ta sadda kanta kasa. Abba cikin sanyi ya ce "Mansura, har yanzu baki shirya fadamin damuwari ba,. Meye sa ko cikin farin ciki kike kuka?."
Mansura shiru kanta kasa batace ma Abba komai ba. Hannun Mansura ya kamo ya ce "Fada min yanzu me kike so?." Gida zani."
Abba kallan Mansura ya yi kafin ya ce "Kinga yanzu idan kika tafi gida jama'a zasu dauka ko wani abune, ki yi hauri ki zo mu koma har a tashi." Abba ya fadi maganar yana fita daga motar, Mansura ma fita ta yi tana jingina da motar. Abba ruwa ya ba ma Mansura ta wanke fuskarta kafin suka jera suka koma hall din.

Cancikin hall din ko lokacin da Mutane suka Ankara Mansura kuka take, bayan Abba ya fita da ita ihu aka kama, wasu nacewa shaukin so ne ya dibeta take kuka.

Aisha ko daurewa kawai take, gudin karta fasa kuka cikin Jama'a, hakan ya sa ta lallaba mutane na can suna ma Amarya da ango liki bayan an fitar dasu fili Aisha ta fita daga hall din, daidai zata fito su Mansura kuma zasu shiga ita da Abba. Abba kallan Aisha ya yi da hanzari ganin yadda ta fito hall din, Abba juyawa ya yi yana kiran sunan Aisha ya ce "Mommyna ina zaki?." Aisha bata tanka ma Abba ba ta tafi da sauri.

Abba juyawa ya yi ya bi Aisha, shan gaban Aisha ya yi ya ce "Mommyna lafiya ina zaki."
Aisha da dama kiris kawai take jira ta fashe da kuka. Abba da mamaki ya bi Aisha da kallo ganin yadda take kuka, Abba cikin sanyi ya ce "Mommyna me ya faru?." Aisha banza ta yi da Abba, ta Kuma juyawa zata tafi, Abba hannun Aisha ya kamo ya ce "idan gida zaki ki tsaya in samu wani ya kaiki a mota."
Abba ya fadi maganar yana Kira a wayarsa, sunanan tsaye saiga Wanda ya Kira ya karaso, Abba nuna mai Aisha ya yi ya ce "Bilya ka Kai Mommyna gida."
Yana fadin haka ya juya ya tafi.

Mansura Kuma tana nan inda Abba ya barta tsaye, Abba na karasowa inda take ya kalleta ya ce "Muje."

Da yake hankalin mutane duk suna kan Amarya da ango dake tsakiyar hall din hakan ya sa mutane basu lura da shigowar Mansura da Abba ba, Abba bindir din dari biyu ya diba ya ba ma Mansura ya ce "Kima Amarya da ango liki." Yana fadin haka ya saki hannun Mansura ya yi wajan Amarya da ango Yana masu liki.

Mansura ma tashi ta yi ta je ta lika masu kudin da Abba ya bata.

An dade ana gudanar da hidimar bikin sai 11 kafin aka tashi suka dibi kawayan Amarya da sauran iyaye da basu tafi ba aka maida kowa gidansu Amarya.

Aisha ko misalin karfe 8 ta koma gida tana zuwa ta nufi dakinta tana kuka. Mahaifiyar Aisha tsaye ta yi kan Aisha tana kallanta, Wanda ita Aishar ma bata lura da mahaifiyarta dake tsaye kanta ba.
Mahaifiyar Aisha cikin daga murya ta ce "Ke Aisha lafiya meke damunki kike kuka haka?." Aisha dago kanta ta yi tana kallan mahaifiyarta ta ce "Malama, dan Allah ku janye maganar aurena da Yaya Abba." Aisha ta idasa maganar tana goge hawayanta.
Malama zama ta yi gefan katifar kusa da Aisha, ta dade tana kallan Aisha kafin ta ce "Saboda me za a janye maganar auranku? Laifin me ya yi Miki?."
Aisha gyara zamanta ta yi ta ce "Malama Yaya Abba zai aureni ne bisa umarnin mahaifiyarsa bawai dan Yana Sona ba, yana da wadda yake so, ki yi hakuri Malama rannan karya na yi Miki da nace miki Yana kirana muna chart na fadi haka ne kawai tunanin ko zai canza, Amma yanzu na gama tantance baya sona ba tani ma yake ba, ko na auresa bakin ciki kawai zan kwasa."
Shiru Malama ta yi dan tuni ta fahimci haka, sannan tunda Aisha ta fito ta furta haka tasan tana da babban dalilinta.
Malama kallan Aisha ta yi ta ce "Aisha, kin riga kin makaro da kika boyemin gaskiya tun farko, kina ganin yanzu zan iya tunkarar mahaifinki da maganar nan ne in ce mai bakya son Abba, ba zaima sauraran ba, dan haka ki yi hakuri kawai kita addu'a."
Malama na gama fadin haka ta tashi ta fita ta ba Aisha waje. Ita ko Aisha abin da ya Kuma ta fasata ta tabbatar Abba baya sonta ganin ta tafi tana kuka Kuma baidamu yasan damuwarta ba, sannan ko ya kirata, abin da ya kamata yadda ya barta tana kuka ace ya kirata.

Amina ko taron mutane da yawa hayaniya ta yi yawa shi ya sa bata lura Aisha ta tafi gida ba.

Bayan su Aisha sun dawo gida daga wajan partyn, Amina kallan Mansura ta yi ta ce "Mansura kinsan Allah dazu a wajan partyn nan da aka ce keda Yaya Abba za ku bude fili har kosawa na yi inga Dj ya sa maku waka, inga yadda za ku yi, abin mamaki wai sai ga yaya Abba yana rawa, abin nikam na rasa yadda za ai ya bar ban mamaki."
Mansura tashi ta yi ta zauna ta ce "Ni Wallahi kunya ma na ji da farko, ke kece fa baki lura ba tun a cikin mota lokacin da za mu tafi wajan fatin yake rawa baya sa wata waka ba, tun a nan ya fara rawarsa." Amina rike baki ta yi ta ce "Shi ya sa Yaya Abba akwai zuwa biki ai, Amma nikam na sha mamaki, Kuma Allah baki ga abin ba Kun bada kala fa, sai kuka yi kamar wasu Masoya."
Mansura hararar Amina ta yi bata ce komai ba. Amina dai gudin karsu yi fada da Mansura cikin daran nan ya sa ta ja bakinta ta yi shiru ba ta Fadi abin da ke ranta ba. A haka barshi ya kwashesu.

Washagari da wuri aka fara Shirin tafiya da amarya, dan abokan angon dama duk suna nan basu tafi ba.

Da wuri mai yima Amarya makeup ta zo ta ta yi mata, aka nada Mata jar lifiya da ta ji adon stone daga wajan kan, sosai Amarya ta fito ta yi kyau.

Mansura ko tun dazu jikinta ya yi sanyin rabuwa da Aminiyarta, hakan ya sa ko wankan ta kasa yi. Aunty Zainab da shigowarta kenan, kallan Mansura ta yi ta ce "Haba Mansura kina jin ance 10 za a tafi da Amarya Amma kallarki ko wanka ba ki yi ba." Mansura kanta kasa bata dago ba, Aunty Zainab hannun Mansura ta kamo ta rakata har bakin bathroom din kafin ta juyo.

Mansura bayan ta fito babu yadda mai makeup din ba ta yi da ita ba ta yi Mata amma Mansura taki, dole ta rabu da ita ta.

Amina 9:30 aka shiga da ita bangaran da iyayanta maza suke, wato kannan babanta su yi Mata nasiha. Sun dade suna Mata nasiha akan zaman aure da ankarar da ita akan mahimmanci dake tattare da hakuri, tun a nan Amina ta fara kuka. Aunty Zainab hannunta ta kama ta shiga da ita bangaran mahaifiyarsu, mahaifiyar Amina ma kukan take, Amina ganin haka sai ta kara azzaza kukanta. Sun dade kowa ya kasa cewa komai iyayan Amina Mata, su Abba ko suna waje kawayan Amarya da wasu daga cikin iyayan Amarya duk sun shiga mota Amarya kawai ake jira a tafi. Abba cikin jin haushi ya shigo gidan har falon mahaifiyar Rashi ya karasa inda sun tasa Amina sun taru kusan sai kuka suke, masu yin maganar kadan ne. Abba kallan Aunty Zainab ya yi yayar Amina wadda Amina ke bimawa ya ce " Zainab wai meye haka ne." Agogon hannunsa ya kalla ya ce "Kalli dan Allah 11:15AM, muda muka so tafiya tun 10. Aunty Zainab iyayanta ta yi ma magana akan su tashi su tafi ana jiransu.

Amina suka dakko wadda ke aikin kuka tana rirrike mahaifiyarta, shi kanshi Abba sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, Amina Kuma ganin Abba da sauri ta rungumesa tana kuka. Abba hannun Amina ya kama tare da sauran iyayanta da zasu tafi suka fita, da yake a motarsa zai dauki Amarya.
Kasan cewar ya bar gidan gaba ne da a matsayin wajan da Mansura zata zauna, gashi Bata, Kuma Yana lure babu ita gaba daya motocin. Abba shiru ya yi dan baisan wa ma zai tambaya ba Ina take. Wayar Amina ya Kira ya ji ringing dinta a jakarta. Abba kallan Aunty Zainab ya yi dake kusa da Amarya ya ce "Zainab Ina Mansura ne, ta fito mu tafi Mana gashi har an fara tafiya."
Sai yanzu Aunty Zainab tatuna da Mansura tashi ta yi ta ce "Laa ka ka ga namanta da antafi an barta."
Chapter 25 · 0% Book details