← Book details Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 36

Sashe 7

Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar ruwan da aka yi hakan ya sa suka samu tsaikon abin haka. Har Magriba ba suna tsaye babu mota. Da yake gidan Aunty Zainab ya na a bakin titi ne, Amina kallan get din gidan Aunty Zainab ta yi ta ce " Anya ko dear ba gidan Aunty Zainab za mu koma mu kwana b..."
Amina bata rufe baki ba wata tsaleliyar mota ta saya kusa da su. Matashin saurayin tambayarsu ya yi Ina za su. "Cikin gari zamu shiga." Ku shigo mu tafi nima can na yi."
Shiga suka yi ya ja suka tafi. Koda suka shiga cikin garin Katsina tambayar sunan layin su Amina ya yi, nesa da gidan su Amina ya yi parking ya saukesu, inda Amina ta bukata. Suna sauka yana son yi masu magana amma Amina bata bashi damar yi masu magana ba ta ja hannun Mansura da sauri suka wuce.

A baya ya bisu ya ga gidan da suka shiga kafin ya dawo.

Abba a kan idonsa aka sauke su Amina a mota zai shiga sallar isha'i kenan.

Amina Kuma bayan sun shiga gida, kallan Mansura ta yi ta ce "Dear Yaya Abba zai tambaye mu dalilin da ya sa muka Kai dare, idan muka ce mai mun fito za mu tafi kenan, aka fara ruwa zai yi fadan me ya sa muka Kai la'asar, dan haka ce mai za mu yi tun da mu je ake ruwa." Da "to". Mansura ta amsa ma Amina suka shiga gidan.

Koda suka shiga kan dadduma suka iske Mahaifiyar Amina, bisa ga alama sallar issha'i ta idar.
Mahaifiyar Amina dago kanta ta yi ta kalli Amina ba ta ce mata komai ba ta maida kanta kasa.

Amina zama ta yi tana fuskantar mahaifiyarta, cikin sanyi kamar za ta yi kuka ta ce "Mama Wallahi ki Kira Aunty Zainab ki ji muna fitowa aka tsuge da ruwa, kin ji dalilin da ya sa muka Kai dare."
"Amina, ba tun yau ba kinsani bana son kai dare, nikam babu ruwana tsakaninki da yayanki, ko kafin ku fita sai da ya jaddada miki karku Kai dar..."

Sallamar Abba ya sa Mahaifiyar Amina yin shiru.

Mansura ko da ke tsoran Abba, hakan ya sa ta tashi zata shige bangaransu, jin sallamarshi. Har ta tafi Abba ya dakatar da ita ya ce "Ke."

Mahaifiyar Abba kallan Abba ta yi ta ce "A'a Abbana, laifin Amina ne ita bata da laifi in da ba ta san dokar gidan nan ba. Mansura tafi abinki."

Mansura saida ta sauke ajiyar zuciya tsabar jin dadi.

Abba cikin fushi irin Wanda Amina ta sanshi da shi ya ce "Amina waya kawoku a mota?."
Amina kallan mahaifiyarta ta yi tana langabar da kai ta ce "Mama Wallahi tun da muke je ake ruwa, shi ya sa muka rasa mota, shine dalilin da ya sa ma Koda ya yi Mana ta yi ma muka shiga motarsa ganin dare ya yi."

Marin da Abba ya kaima Amina ne ya sa ta yi shiru ba tare da tasan ta yi shiru ba. Hannu Abba ya daga da sunan Kuma Kai Mata wani Marin mahaifiyar Amina ta rike hannunsa ta ce "Abbana inda ta ce ruwa akayi akwai uziri."
Abba Kai ya girgiza ya ce "Wallahi mama karya take acan na yi sallar ajahar sai 3::00PM Na bar garin, Kuma lokacin haɗarin ba wani sosai bane bama. Kin ga sai yamma kila ma aka fara ruwan."

Abba shako wuyan Amina ya yi ya ce"Su waye suka saukeku a mota?." Amina ihu take tana ba Abba hakuri. Wanda ko jinya baya yi, dan shi babu abin da ya tsana Kamar yaga yarinya na yawo a motar saurayi, atunaninsa haka yana taka mahimmiyar rawa wajan lalacewar tarbiya. Hakan ya sa Abba ya shake Amina Yana cewa "Ba zaki fada min ba su uban waye suka daukeku a mota?."

Amina ko zare ido kawai take ta kasa magana yadda ya shaketa.

Allah sarki uwa, mahaifiyar Amina kasa jurewa ta yi,ta kamo hannun Abba dake wuyan Amina ta yi ta ce, "Abbana, aika shaketa ba zata iya magana ba, ka saketa sai mu ji Wanda ya daukesu a motar."

Abba sakin Amina ya yi wadda yana sakinta ta samu damar fashewa da kuka. Mahaifiyar Amina Kuma, tsawa ta yi ma Amina ta ce "Dan ubanki ba za ki fada Mana uban waye ya daukeku a motar ba?."
Cikin kuka Amina ta yi masu bayani ta hada da cewa "Wallahi yana kawo mu yana tambayarmu Number waya, Amma ko sauraransa ba mu yi ba muka tafi."

Abba Kai ya jinjina ya ce "Daga nan har ki bar gidan nan Allah ya sa wani dan isa ya Kara kawoki a mota, Wallahi tallahi ranar ba za a gane kamanninki ba." Yana fadin haka ya fita ya bar falon baki daya.

Mahaifiyar Amina Kuma fada ta Kara yi ma Amina.

Amina da kuka sosai ta shiga bangaransu, inda ta iske Mansura sai zare ido take, kallo daya za ka yi Mata kafahimci a tsorace take.

Amina fadawa ta yi kan gadon tana kuka.
Mansura dai bubbuga bayan Amina taita yi tana Kuma bata hakuri. Amina ta dade tana kuka kafin ta tashi tana nuna ma Mansura wuyanta ta ce "Dear duba min wuyana ki ga bai ji min ciwo ba?."

Mansura duba mata ta yi, cikin tausaya Mata ganin yanda wajan ya yi ja na rikewar da ya yi Mata ta ce "Sorry dear."

Ranar nan dai haka suka yi barci babu wata hirar kirki, uwa uba Kuma ga sanyi damuna, ga Kuma bacin ran dukan Amina hakan ya sa da wuri suka yi barci.

Washegari, misalin karfe 7:00AM, mahaifiyar Amina ta samu Amina har dakinsu, bayan sun Kuma gaidata ta kalli Amina ta ce "Amina, Ina fatan Ahmad ya sanar da ke yau danginsa za su je wayan 'yan uwan mahaifinki naiman auranki?."
Amina zaro ido ta yi tana mamaki dan ko yau shi ya tadata sallar asuba Amma bai fada Mata ba.

Mahaifiyar Amina Kuma jin Amina bata ce komai ba, ta ce "Amina, ba da ke nake magana ba?."
Amina cikin sanyi ta ce "A'a Mama bai sanar min ba."
Shiru mahaifiyar Amina ta yi kafin ta ce "Tom Ina fatan babu wata matsala?." Eh, mama Babu." Cewar Amina.

Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta sauke ta ce "Tom ma Sha Allah." Sannan ta tashi ta fita.

Mansura gaba daya jikinta sai ta ji yayi sanyi, tana tunanin yadda zata ci gaba da zama gidan idan Amina ta yi aure. Amina lura da tunanin da Mansura ta fada ne ya sa ta dafa Mansurar.
Mansura kallan Amina ta yi, ta yi murmushi ta ce "Amarya, Allah ya kaimu lokacin." Ameen, dear kema Allah ya fito miki da naki ayi tare, bana son in tafi in barki a gidan nan ke kadai, Ina nan ma kullum cikin ƙoƙarin sama kanki damuwa kike Ina ga bana nan."

Mansura sosai jin maganar Amina za ta yi aure ta daga Mata hakankali, dan tana tunanin yadda za ta rayu gidan babu Amina, Ina bata jin ma zata iya ci gaba da zama babu Amina.
Take Mansura ta fara waye wani kan wani.

Amina jin kamar shashshekar kuka da sauri ta dago tana kallan Mansura. Bata fuska Amina ta yi ta ce, "Haba, Mansura yanzu Kuma anan meye abin kuka, auran da ko sashi ma ba a yi ba, yau ne za a sashi, Kuma ke baki fatan Allah ya kawo mik naki kafin mawa a hada a yi."

Ai Amina kamar ta ziga Mansura fashe Mata da kuka ta yi.
Amina baki ta saki tana kallan Mansura, ganin abin da gaske take ya sa Amina ta fara lallashinta ta ce "Ki yi hakuri dear, nima bana son in tafi in barki ke kadai ne, in sha Allah ni Kuma na yi miki alkawari har sai kin samu miji ko zan yi aure, zanma Yaya Ahmad magana a sa lokacin da tsayi har lokacin da Allah zai fito miki da naki kema."
Amina ta dade tana baansura baki kafin ta yi shiru.

Misalin 5:00PM kanin mahaifinsu Amina ya yi sallama ya shigo falon mahaifiyar Amina. Bayan sun yi gaisuwa mai tsayi cikin mutuntawa da mahaifiyar Amina, ya dora da cewa "Tom Alhamdulillahi, baki sun iso kamar yadda suka ce. Duk wani Abu da ake bukata na sa ranar aure kudi suka bata gasu a hannuna. Mun sa ranar aure wata uku cif-cif, ya kika gani?."
"Haba baban yara, ai duk yadda kuka yi Wallahi ya yi, sai dai mu yi fatan Allah ya kaimu lokacin. Kayan aure Kuma kar kice tsaki takura ma kanki, ki bar Komai a hannuna da Abba za mu yi."

Godiya sosai mahaifiyar su Abba ta yi mashi, kafin suka yi sallama ya tafi.

Bangaran Amina da daddare suna waya Ahmad ya ke sanar da ita lokacin bikinsu da aka sa musu. Amina zaro ido ta yi jin ya ce Mata wata uku. Tom Amma Kuma tana tsoran ta yi wata magana Mansura ta ji hakan ya sa ta yi shiru ta bari ta yi ma mahaifiyarta magana, inda akwai fahimta sosai tsakaninta da mahaifiyarta.

Washegari, Amina ta samu mahaifiyarta da maganar. Amina kanta a kafadar mahaifiyar tata kamar za ta yi kuka ta ce "Mama ni dai lokacin auran nan da aka sa gaskiya ya yi kadan, dan Allah mama ki yi ma Yaya Abba magana ya yi ma Baban yara magana a Kara."

Mahaifiyar Amina dago da kan Amina ta yi tana kallanta, dan ta gasgata abin da Amina ta ce.
Shiru mahaifiyar Amina ta yi, kafin ta ce "Kamar ya wata uku ya yi kadan?."
Amina kamar za ta yi kuka, ita dai duk dan mahaifiyarta ta sausaya Mata ta yadda da kudirinta ta ce "Mama kin ga idan na tafi na bar Mansura ba za ta ji dadi ba, da ni kadai ta saba a gidan nan. Amma kin ga yanzu idan aka Mai da shekara kafin itama Allah ya bata nata sai a hada a yi."
Chapter 7 · 0% Book details