Sashe 3
Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina kwana ta yi tunanin yadda za ta kuri Mansura.
Washegari, Amina bayan ta idar da sallar asuba kallan Mansura ta yi dake kwance babu alamar zata tashi. Amina bubbuga kafar Mansura ta yi ta ce "Kawata, ki tashi ki yi Sallah mana, ko kina hutu ne?."
Mansura shiru ta yi bata tanka ma Amina ba, karshe dai Amina gajiya ta yi ta rabu da ita ta nufi bedroom din mahaifiyarta.
Zaune ta isketa kan abin Sallaya tana lazimi, Amina zama ta yi har mahaifiyarta ta kammala laziminta. Amina cikin sanyi ta ce "Ina kwana mama." Lafiya lau Amina, ya bakuwarki ta tashi kuwa?." Cewar mahaifiyar Amina.
Amina cikin damuwa da lamarin bakuwar tata ta ce, "Wallahi mama, nama rasa yadda zan yi bata tashi ba, jiya ma fa ko Sallah ba ta yi ba ta kwanta, yau ma na ga ba ta yi Sallah ba."
Murmushi mahaifiyar Amina ta yi ta ce "A'a rashin sallarta ba damuwa ba ce kila tana hutu ne, ni dai yanzu Amina ya kike ganin za a yi da yarinyar nan? Kin ji dai abin da yayanki ya ce Kuma kin san halinsa."
Amina shiru ta yi dan sosai ta rude da gargadin yayan nata tasan halinsa sosai. Kallan mahaifiyarta ta yi ta ce "Wallahi mama gaba daya tun jiya barci ya kaurace min, Ina tunanin yadda zan yi da ita, dama ban rabota da garinsu ba dada sauki."
"Amina, ni yarinyarce sai inga kamar bata da hankali, anya ba ciwan hauka take ba? Yanayin yarinyar ni dai ya fi min kama da ciwan hauka." Cewar Mahaifiyar Amina.
"Tom kila, Amma dai a asibitin da Yaya Abba ya kaimu sun fi danganta abin da razana, da tsananin damuwa, Kuma nima nafi yadda da haka kamar damuwa ce ta yi Mata yawa. Ni dai mama duk ba wannan ba, ya zan yi da ita kin ji dai abin da Yaya Abba ya ce min?."
Mahaifiyar Amina Kai ta jinjina kafin ta ce, "Amina kin San dai halin yayanki, ba ƙaramin aikin shi bane ya kamaki ya buga akan yarinyar nan, dan haka idan za ki ji tawa ga kudi ina da su ki amsa daga gari ya Kara haske ki je ki sata a motar Kaduna ki dawo."
Amina kamar za ta yi kuka ta ce "Wallahi Mama likitan da ya dubata ya tabbatar min ba cikin hankalinta take ba, ya ce mu bata nan da kwana biyu mu gani kila ta dawo cikin hankalinta. Dan Allah Mama ki yi ma Yaya Abba magana, Allah bashi daga ta dawo hankalinta sai ta tafi garinsu, dan Allah Mama mu tausaya Mata ba mu San halin da take ciki ba, daga ka ganta ka ga wadda razani da tashin hankali ya bayyanar Mata,Wanda daga gani shi ne silar damuwar nan tata."
Mahaifiyar Amina shiru ta yi, sannan ta ce "Amina ba Wai naki bane, rayuwarce me wuya, kina ganin abin da ya faru da gwaggonki kwanakin baya daga taimako yarinyar nan ta yashesu, ga abubuwa nan dai da yawa wa inda muke jin labari sanadin taimako." "Mama ba fa duka aka taru aka zama daya ba, Kuma shi kenan saboda haka sai ka ga mutum cikin ƙunci kaki taimaka masa? Wannan dai daga ganinta Mama munsan tana bukatar taimako, Amma ni ba nace dole sai mun taimaka Mata bane, ina naiman alfarmatar mu bata nan da kwana biyu ta dawo natsuwarta koda za mu koreta, dan yanzu ko mun koreta ba lalle ne ma ta san inda zata ba, inda ba cikin hayyacinta take ba." Amina ta isa maganar tana kallan mahaifiyarta.
Ajiyar zuciya mahaifiyar Amina ta yi ta ce "Shi kenan, amma ya za mu yi da yayanki? Kin ji dai rantsuwar da ya yi in ya dawo ya isketa a gidan nan."
"Mama sai mu hanata fita falo inda dai Yaya Abba ba shigowa bangaremu yake ba." Amina ta idasa maganar tana langwabe kai, alamun mahaifiyarta ta tausaya Mata.
"Shi kenan Amina, idan za ki iya tsareta ba zata fita falo ba, amma fa ki sani babu ruwana idan yayanki ya Kuma ganinta gidan nan?."
"In Allah ya yadda ma ba zai ganta ba." Amina ta fadi maganar tana tashi ta fita. kitchen ta shiga ta soya doya ta dafa ruwan Lipton ta kaima mahaifiyata, ta zauna suka karya tare kafin ta hada na bakuwarta ta Kai Mata nata.
Da mamaki Amina ta bi Mansura da kallo ganin har yanzu bata tashi ba tana nan a yadda ta barta. Amina hannu tasa tana bubbuga Mansura ta ce "Mansura, ki tashi Mana haka nan." Ido Mansura ta daga tana kallan Amina alamun ba barci take ba. Amina murmushi ta sakar Mata ta ce, "Ki tashi Mana ki watsa ruwa ko za ki ji dadin jikinki, ga abin breakfast na kawo Miki."
"Na koshi." Mansura ta ce a hankali.
Amina da mamaki ta kalleta ta ce "Kin koshi? Jiya ma fa biki ci komai ba kika kwanta, a'a dan Allah, ki tashi ki ci ko babu yawa."
Amina hannun Mansura ta kamo ta ce "Mu je ki yi wanka za ki ji dadin jikinki, sai ki yi breakfast."
Mansura bin Amina ta yi har bathroom din ba tare da ta so ba, Amina hada Mata ruwan wankan ta yi , sannan ta fito ta barta.
Shiru-shiru Mansura bata fito ba, Amina jin shirun ya yi yawa ya sa ta matsa kusa da bathroom din ta ce"Mansura, kin gama wankan ne?."
Mansura da tunda ta shiga tsugunne take tana kuka sai lokacin da ta ji Amina ta kirata kafin ta tashi da sauri ta yi wankan ta fito.
Amina cikin kayan sawarta ta dakko wata goguwar riga ta ba Mansura. Amina da kyar ta samu Mansura ta sha tea din kadan, soyayyar doyar ko ko kallanta ba ta yi ba.
Amina sosai take ƙoƙarin jan Mansura a jiki dan ta ji damuwarta, amma duk abin da za ta ce sai dai Mansura da kalleta da ido. Dole ta hakura ta rabu da ita. A haka Mansura har ta yi kwana uku har yanzu ba su san ko wacece ba, dan jiya mahaifiyar Amina da ta matsata mata da tambaya kuka tasa Mata, hakan ya sa dole suka rabu da ita.
Yau kwanan Mansura uku kenan agidan, Kuma har yau Abba bai san tana gidan ba.
Yanzu haka Abba zaune suke shi da mahaifiyarsa suna fira. Abba kallan mahaifiyarsa ya yi ya ce "Mommy nifa kamar kuka nake ji?" Mahaifiyar Abba da tun dazun take jin kukan, tana sane sharewa kawai take dan kar Abba ya fahimci har yanzu Mansura na gidan, shi ya sa ta yi shiru, dan tasan Mansura ce ke kuka.
Abba jin mahaifiyarsa bata ce komai ba, ya ce "Kai mama, wannan kuka ne." Kallan Amira ya yi ya ce " Amira je ki gani Ina Amina."
"Uncle Abba, ba fa Mommy Amina ba ce ke kuka, bakuwar nan ce wadda mommy Amina ta zo da ita ke kuka, haka take yi kullum sai na ganta tana kuka, mommy Amina da Mama su yi ta bata hakuri amma taki yin shiru.".
Abba da mamaki ya kalli mahaifiyarsa ya ce "Mama, dama yarinyar nan har yanzu tana gidan nan?." Abba Mai da kallanshi ya yi ga Amira ya ce "Amira Kira min Amina."
Amira da gudinta ta je ta kira Amina. Amina ko dama baki daya a tsorace take, jin yadda Mansura ke kuka da karfi ta San yayanta na gida zai iya ji. Yanzu haka hakuri take ba Mansura tana cewa, "Mansura dan Allah ki rufa min asiri ki yi shiru, Yaya Abba ya dawo yanzu kar ya jiki." Suna cikin haka ne Amira ta shigo ta ce, "Mommy Amina, Uncle Abba yana kiranki." Amina zaro ido ta yi tana kallan Amira, sannan ta ce "Amira Yaya Abba na falo ko?" Eh, Yana falo, shi ne ya tambaya wake kuka, na ce mai bakuwarki ce ke kuka, shi ne ya ce in kiraki."
Tun kafin Amira ta gama Kai bayani Amina ta fara goge zufa, dan tasan yau mai kwatarta hannun yayan nata sai Allah. Amina har zata fita ta kalli Amira ta ce "Amira mama na falo?." Kai Amira ta daga Mata.
Amina da addu'a ta idasa falon.
Can falon ko, mahaifiyar Amina ta dage sai ba Abba baki take tana cewa "Abba, ni na ce Amina ta bar yarinyar nan ta wastsake tukun, Kuma ta wastsake, dan tun ranar da ka ce ta koreta ta yi niyyar zuwa ta sata a mota ta tafi, ganin halin da yarinyar take ciki na ce ta barta ta warware."
Abba dai baice komai ba, dan yasan mahaifiyarsa ta fadi haka ne dan Kar ya bugu Amina. Suna a haka ne Amina ta shigo falon a tsorace. Kafin Abba ya yi magana, Amina ta ce "Yaya Abba, dan Allah ka yi hakuri."
Abba be cema Amina komai ba, sai zuwa can ya ce, "Amina kinsan dai baki taba nuna kina son abu ba naki ko?." Kai Amina ta daga Mai. Ya ci gaba da cewa. " Tun da yarinyar nan ta zo gidan nan bayan sunanta kun Kara sanin wani abu akanta?." Nan ma Amina Kai ta girgiza ma Abba, alamun ba su sani ba.
"Amma Kuma shine ke gaki shugabar masu tausayi duk da haka kina tausaya Mata, ba zaki iya barinta ba ko?" Ya ci gaba da cewa "Yanzu Zamani ya lalace Amina fiye da yadda kike tunanin, wama ya Sani kila wani takashe ta gudu, dan da bakinta ta furta Mana haka, Kuma kin ga in ta tabbata haka ne mun boye mai laifi kenan. In dai baki so mu samu sabani Ina so gobe ki sallami yarinyar nan ta bar gidan nan, ni baki daya hankalina bai kwanta da lamarinta ba."
Abba 10k ya dakko ya ba Amina ya ce "Gashi, ki kaita tasha gobe ki sata a motar Kaduna."
Amina cikin jin dadin ganin yayan nata bai mata komai ba ta ce "Na gode yayana Allah ya Kara arziki." Tana fadar haka ta tashi ta tafi.