← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 37

Sashe 9

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙafar benen tay hanzarin kamawa tana sakin wata munafukar ɓoyayyar ijiyar zuciya ta saki acan ƙasan ranta. Juyowar da zatai tay ido biyu da Mammanta wacce ta tsarera da ido, Ɗan faɗuwa taji gabanta yayi ganin yadda Mah ɗin ta wani kalan tsareta da idanunta."Me ki ke yi anan?" kai tsaye Mah ta cilla mata tambayar fuskanta babu alamun wasa don ita mace ce bame son ɗaukan wargi ba ko daga yaran natane kuwa. "Ina shan iska ne maah" Rolex watch ɗin dake daure a tsintsiyar hannun ta Mah ɗin ta kalla tana furta. "Kalla ki gani ƙarfe nawa yanzun da kike nan tsaye har yanzun baki kwanta ba?" Kanta ta ɗan rausayar gefe ba tare data ko sake furta wata magana ba Mah ta kama hannunta tana kaita har bakin ƙofar parlour'n ta.
Ita kuwa Meesherh Koda ta shige room ɗin nata ma bata shige bedroom nata ba kwance kawai tay anan bisa 3 str daga ita sai wata yellow ɗin doguwar rigar baccin dake jikinta irin me santsin nan me kuma bin jikin mutum.Sai wata tattausar hular sanyin dake kanta yellow, yayinda himilin gashinta yayi luf luf yana kwanciya har gadon bayanta se dai ba can ba, don da kaɗan ya zarce kafaɗunta. Sosai tay wani kalan masifar kyau duk da kasancewar kayan bacci ne a jikinta,kasancewar ita ɗin me kyau ce wanda shi wannan kyaun ya haɗu da aji da kuma tsantsar hutu da jin daɗin Rayuwa. Har ta kama doorhandle na ƙofar parlour'n ta seta juyo da baya tana jin kamar ba daidai ba, kodan kasancewar ta auta ne ya sanya duk daren duniya bata taɓa iya bacci ba tare da ita taga baccin babyn nata ba. Kamar yadda take a kwance a parlour'n haka Mah ta tarar da ita kwance hankalin kwance kuma take baccin abinta.Gashin kanta dake ɗaure cikin jan riboms ƙwara ɗaya ya zame yayi nashi wuri, se hakan ya bama gashin damar bajewa akan 3 str ɗin da take kwance akai.Se sheƙi da walainiyar kyau yake gwanin birgewa. Zama tay gefenta farar fuskanta irin ta Mahaifinta Sameer Jedaans sak ta ɗan shafa,sauƙe ajiyar zuciya tay tana zuba mata idanu sosai, A natse kuma ta shiga tashinta ba yadda zata firgita kota tsorata ba. Idanunta ta baccin sosai ya fara cin ƙarfin su ta ware akan mahaifiyar nata. Ɗan Murmushi me laushi ta sakar mata tana kamata ta mikar da ita tsaye.
Kasancewar ta bame nauyin bacci sosai bace ya sanyata miƙewa Mah na taimaka mata wajen soma tafiya da ita. Akan lallausan gadonta ta kwantar da ita haɗi da tattare mata gashin tan wuri guda tana sake ɗaure mata shi da ribboms ɗin cen ƙasan ƙeyarta don karya dameta wajen baccin. Adda'an barci ta mata haɗi da neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta kuwa faɗi take {ya Allah ga baiwar ka nan Meesherh ka kula min da ita cikin amincinka da buwayarka, kaci gaba da tseratar min da ita daga duk wasu masu nufarta da mugun nufi. Na bayyane da na ɓoye, ya Ilahi ya mujibud da'awati karkaci gaba dabe kowa damar sake cutatarmaka da wannan bewar take me raunin zuciya!!! Ya Allah} Se kuma A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai saman ƙirjinta haɗi da ɗan ɗukawa tana manna mata kiss a goshinta.
"Ya Allah kamar yadda ka raba tsakani idan har babu Alkhairi karka kuma jarabtar wannan baiwa taka da wani abu na daban" wannan karon kam a bayyane tay maganar Jiki sanyaye ta juya tana barin bedroom ɗin. Itama jikinta sanye da kayan bacin dogon wando da riga sakake sosai da riga buɗaɗɗiya sosai irin fararen nan masu faɗi dai haka sosai. Kamar yadda ta fita haka ta dawo ta tarar da prof Sameer Jedaans yana nan zaune gaban System nashi sai faman aikin sarrafata yake idanunsa sanye da farin gilashi, bare daya ɗago ba ya furta "Se yanzun kike dawowa? Kin gama lallaɓa Babyn taki kenan har tayi baccin!" Murmushi kawai ta yi ba tare da tace komai ba ta wuce Bathroom don haɗa masa ruwan wanka me ɗumi da ƙamshi. Don al'adansane baya taɓa kwanciya har se yayi wanka. Zama tay kusa dashi tare da ɗan Murmushi ɗauke saman fuskarta. Kanta ta kwantar da kanta saman shoulder nashi, "Papiey'n Meeshel ruwan wankanka is ready"
Kansa kawai Papiey'n ya ɗan girgiza yana lumshe idannuwansa ƙaunar matarshin abin sonshi na sake ratsa shi. Kayan jikinsa ya rage yana faɗawa bayin.
Bayan ya fito É—aure da alwulan da al'adan gidan ne ba'a kwanciya ba tare da alwulan ba, sedai wasu sukan yi wasu kuma basu yi haka nan tsarin yake. Ko kafin ya fito tuni Mah ta sake gyare bed É—in daga nan suka kwanta abinsu se bacci.

☆☆☆☆

Ance wai dare mahutar bawa, kamar ko wanne rai me numfashi ke kwance domin samun hutu ga rayuwarsa cikin kwanciyar hankali yana barcinsa, Se dai a dai-dai wannan loƙacin Sheikh juraij thabit ke zaune saman darduma yana rera karatun Al- Qur'ani mai girma,Cikin wani irin amo madaidaiciyar muryarsa mai daɗin sauraro da sanya ma zuciyoyi nutsuwa yake raira karatun. Idanunsa lumshe suke daga can cikin ƙasan ƙasan zuciyarsa karatun ke fitowa.

Wani kalan Nunfashi mai nauyi Abba dake tsaye tun da jimawa a ƙofar shigowa parlour'n yaron nasa yaja. kana ya fesar tare da cike da sanyin jiki ya turo ƙofar ya shigo a natse. Jin motsin ne ya sanya Sheikh juraij buɗe idanunsa da suke a lumshe har zuwa loƙacin. Akan Abbansa ya sauƙe ganinsa kai tsaye, saurin tashi tsaye yay yana me nufo abban.
Sanya hannun sa masu taushi yay yana kama na sheik É—in cikin nashi, bakin bed É—in Sheikh É—in Abba ya zaunar dashi shima yana zama kusa dashi. Se daya É—an ja wasu second haka kafin cike da tsananin tausayin yaron nashi ya furta.
"JURAIJ akwai wata alfarma da nake nema awajenka!" Cike da wani Irin baƙon yanayin da zuciya ke ɗauka a bazata ya ɗago kansa yana kallon Abban cike da girmamawa ya furta.
"Abba kawai kace wani Umarni zaka bani amma ba alfarma zaka nema daga gareni ba. Saboda kafi ƙarfin neman alfarma awajena sai dai ka bani Umarninka kawai, Ni kuma a koda yaushe me biyayya ne ga dukkanin umarninka"

Zama da kyau Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin raunin zuciya da amincin da yakeji akan Sheikh juraij É—in yace.
"Um-um Juraij alfarmar dai kam nake nema" Cikin jin nauyin mahaifin nashi da ganin kimansa ya sake risinar da kansa ƙasa, muryan sa har na shirin karyewan raunin da tay ya furta. "Idan har Abbana ya zaman yana nema alfarma daga gareni to ni a gun waye zan nemi ta wa alfarmar, idan kana faɗin hakan Abba kunya nake ji duk loƙacin da naji kana furta kalmar neman alfarma daga gareni Abbana"
Kai Abban ya ɗan girgiza cikin sauƙe wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya furta. "Sai alfarmar da zan nema daga wurinka inason ya kasance iyaka ni da kaine, a iyaka mu nake son maganar ya tsaya" kansa yake geɗawa Abban tamkar irin wanda bay maganan nan. Kafin cikin wani irin yanayi mai gauraye da damuwa da rauni ya furta. "Insha Allah Abba a koda yaushe ni me bin umarnin kane kamar yadda ni me riƙe maka sirrinka ne"
"Meesherh!!!, Meesherh itane damuwar juraij tare da Mahaifiyar ka na rasa ta yadda zan fuskanci wannan al'amari Juraij....." Daga nan suka juye baki zuwa wani yare na daban wanda Ni AMMEY LAYLERH'NKU banjin duk abinda suke faɗi ɗin kuwa. Sun ɗauki a ƙalla sama da 40 minutes suna magana kuma cikin wannan juyayyen harshen da suka juyemin. Kafin daga bisani Abban ya miƙe cikin yanayi na ƴar damuwa Sheikh ɗin na biye a bayansa. Da sauri Inuwar da tun farkon fara zancen nasu take tsaye ta gilma alamar ta kauce. Kafe wurin da ido Sheikh juraij yay zuciyan sa na beating na ɓacin ran hakan da aka jima ana mai wato laɓe....

*Around 4:20 Am*
Chapter 9 · 0% Book details