← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 37

Sashe 32

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

ꨄ

*༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻*

_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _
♡
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

𝙋a𝙜𝙚

21&22

https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D

✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta.

Ga link nan ga masu buƙatar shiga
👉https://t.me/ammeylaylerh_novel

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Masu iya magana sukace wai Rana bata ƙarya, tabbas wannan karin magana haka take don kuwa a yau ne ranar asabar dubban jama'a suka shaida ɗaurin Sheikh juraij thabit Jedaans tare da amaryarsa Samha Abdulkareem Wada a babban masallacin dake nan cikin anguwarsu. Biki da bidi'a sosai dangin amarya suka shirya wanda suka san ko guguwar me Sheikh ya sha sun san bazai jeba. Haka suka inga gudanar da taron bikinsu Amarya Samha kuwa ba'a cewa komi. Don wani irin zumuɗi take yi na bikin. Wanda kuma a daren ranan ne aka dangan tata da gidan Sheikh ɗin, dake sun san tsarinsa babu bidi'a ko kaɗan ya sanya baffanta da kanta ya kai ta har ɗakin mijin nata. Sedai ya tarar da wasu dangin mahaifiyarta a gidan shidai seda ya tabbatar ya danganata da ɗakin mijinta kana ya mata yar nashiharsa kan tabi mijinta kar kuma ta ɗauka halin mahaifiyarta. Fitowarsa daga wanko kenan ta shigo kamar an jehota room ɗin. Kawai sai sauƙar hannuwanta yaji saman fresh naked skin ɗin sa, farko seda gabansa yaji ya may wani mummunan bugu amma yana jinta bai ko motsa bare  ta saka ran zai tanka ta, cik6 nutsensa ya zame hannuwanta data zagaye shi yana zaunar da ita gefe da bed ɗin. Kai tsaye kayansa na bacci farare ya kwasa yana komawa bethroom ɗin daya fito ya kimtso kansa cikin dogayen lallausan kayan baccinsa na long sleeve pyjamas, seda ya gabatar da nafilfili kana ya dawo kan gadon yana kwanciya don shi shafff ma ya manda da wata ana Samha zaune a dakin. Daga inda take zaune ta miƙa hannunta a bayansa kasancewar rufda ciki ya yi slowry ta fara shafa bayansa she's try to make him feel emotions for her, da wani irin tarin mamaki al'ajabi ya yayi saurin juyowa yana sauƙe kallonsa a kanta.
"YA SHEIKH BACCI" ta furta cikin wata shegiyar murya wai irin zata rinjaye shi ɗin nan tare da sake ɗora hannunta a waist ɗinsa ta zagaye ƙugunsa da duka hannuwantan, duk abinda dake mishi yana jinta sai dai he's not interested bai da feelings ko guda a kanta bare ta yi tunanin zai ji wani abu dangane da abinda take masan, abinda kawai ya sani feelings nashi yana jin sane kawai akan mutum ɗaya wanda a farko ma shi yasa kota kota baida cikakken lafiyane irin na kowanne cikakken ɗa namiji. Se daga baya ya gane ba haka hasalin karatun yake ba shi wannan feelings ɗin akan tane kaɗai yake tasiri domin duk inda cikar mace takai mace to ko ɗan yatsar ƙafarsa bai harbawa bare har aje garin jin feelings a knata. shiru kawai yayi yana jinta yana son mata magana
Amma kuma baison shiga haƙƙinta gudun kar ALLAH ya kamashi da laifin rashin kyautatawa a gareta tunda yanzu mallakinsa ce ta zama matarsa ta sunna. Daɗi da ƙari baison hayaniyar komi saboda yadda yaji gaba daya komi da komi na sire mishi kansa kuma kamar zai fashe ya tsage gida biyu,jin tana ƙoƙarin sanya hannunta cikin bxer ɗinsa ne ya sanya ya yi saurin haɗe ƙafafunsa tare da mirginawa ya ware fararen idanunsa a kanta, ita kuwa samha jin ya dakatar da itane ya sanya ta buɗe idanunta don ta riga da ta gama sakawa ranta cewan yau zata kwashi romonsa. Jikinsa har wata tsuma tsuma yake ya mike tsaye tare da mata nuni ta fita. Ƙi yawa tayi sema sake ƙoƙarin rarumarsa da take sake niyan yi hakan ya sanya shi miƙewa tsaye yana furta "pls Samh kije bana cikin ko wanne kalan mood moment ne" cikin wata maraitacciyar murya ta furta "Please jurh ka saurare ni wllh I love you to the rest of my life,kai kawai nake gani na ji farinciki,I want to stay with you forever! I want to stand by your side Ina sonka wllh na yarda zan kwana anan ba tare da munyi komi ba" Wani irin yunƙuri yaji zuciyansa ta masa wanda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa a kanta amma duk yacce yakai ga hakan hakan seda ya gagara hakan ya sanya shi nufar inda take cikin tafasar zuciya amma a normal nashi yake.haka ya ja hannunta kiiiiiiiiiiiy har nakin doorhandle na room ɗin ya a cillata woje tare da rufe ƙofar yana jingina da jikinta, yana jin tamkar ana gasa kanshi ne a cikin ovan, daga ta cen ƙasan zuciyarsa kuma yana jin tamkar hakan dayay ya saɓa wota lamba ce, yana jin tamkar ya aykata ma abu mafi soyuwa a cikin zuciyarsa wani abu ba daidai ba.
Yana jin idan da ace itace yau a matsayin mallakinsa kuma halaliyara a yau zata kwana a gidansa matsayin matarsa to kuwa da babu abinda ze hana komai faruwa a wannan daren.
Don yana mata wani irin Mahaukacin S0 ne wanda ko a baki aka tambayeshi wanne irin so yake mata bazai taɓa iya furta shi ba abinda kawai ya sani yasan He luv her more & more & more for ever never.
Se dai kashhhh idan ya tuna a yanzu ko wacece ita wani irin zafine ke yankar zuciyarsa da ƙirjinsa na irin yacce take gudanar da rayuwarta yanda take so, Ya so ta taso killace a kamile cikin kamalar rayuwa bawai ta zamo me talla wa jikinta ga wasu mazajen duniya na amma wannan kalma ta ƙaddara ta riga fata, ta riga ta gama yima kanta gurbi daram a cikin babin ƙaddarorinsu da haka ALLAH ya rigada ya gama tsaro musu, wanda sau da dama idan ya tuna yacce take mu'amulantar jama'a yakanji ma kwata kwata tama gama sirewa a kansa, amma dake ance so jarabta ne so masifa ne duk yacce yakai ga munana ta a cikin zuciya dama kwayar idonsa da ruhinsa se abin yaƙi tasirantuwa a cikin brain nashi. Innalillahi ya shiga natata yana jin tamkar yana masa dakan ɗaka ne a cikin taaƙiyar ƙirjinsa.
✯
Washe garin ranar.
Zaune take akan sofar dake parlon hannunta ɗauke da wayarta tana ƙoƙarin saka ƙiran mahaifiyarta kana ganin yanayinta kasan She is not felling Wall,Idonta ya kumbura sosai saboda kukan data kwana ta nayi a daren jiya lips nata har tashi yayi saboda tsaban kukan data kwana da kuma irin yadda mararta ta azabtar da ita. Shi kuma Sheikh ya rufe mata ƙofa tayi bugun duniyar yaƙi buɗe mata kofa tunda ya hankaɗota wojen nan.Jin kamar an zauna kusa da ita ne yasa ta ɗaga rinannu idanunta tare da sauƙewa akan Sheikh wanda ya zuba mata ido tare da furta.
"Are you Okay?" Zuba masa idanun nata tayi jin har yana da bakin da zai iya tambayan abinda ke damunta se kawai ta fashe da kuka wanda ya sanya Sheikh Runtse fararen idanunsa domin ya tsani yaji ana kuka kusa dashi, kukan ma ace na mace, macen ba kuma wacce take matsayin mallakinsa. gyara zaman sa yayi har laps nasu na gogan juna wanda ita hakan ya sanya tsikan jikinta wani kalan zubawa, shi kuwa babu abinda yaji. Yana ƙoƙarin sake mata magana kawai ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙameshi tana sake sakin woni kukan tare da cusa kanta cikin tsaƙiyar ƙirjinsa. Wani irin yankewa yaji gabansa yayi ya faɗi kansa na sarar masa loƙaci guda.ita kuwa Samha jinta cikin jikinsa ya sanya ta ƙara ƙanƙameshi tana jin kamar tayi may faɗe. Se kuma cikin muryan kuka ta furta"Kai ne! Ba kai bane jiya ka rufe ɗakin ka ba nayi ta bugu kaƙi ka buɗe min kuma" wani kalan dafe kansa yay domin shi sammm hakan ya ɗauka ba woni matsala bane. Ƙoƙarin janye ta a jikinsa yake tare da furta "OK shi ne kawai matsalan?" Kanta ta jinjina masa tana sake maƙaleshi. Sadda kansa ƙasa kawai yayi haɗe da lumshe fararen manyan Idonsa haɗi da ɗan taunar gefin lips nashi ba da yawa ba yana jan idanunsa ya lumshe saboda yadda yaji zuciyansa na bada bugu da ƙarfi har yana iya jin yanayin yadda gudun zuciyar san ke ƙaruwa. wani wahalallen numfashi yaja sleep'yn eyes nashi wanda suke koda yaushe lumshe na sake janyewa yana amsan yadda bugun zuciyarsa ke ƙara tsanananta.
♡
A mugun firgice ta farka daga ɗan baccin data samu ya ɗauketa bayan tayi sallarn subhi, wanda kwana tayi bata runtsa ba data rufe idanunta pisc na shi kawai ke mata gizo a tsakar kanta tare da wata macen rungume a jikinsa.wani kalan cukukkuye jikinta wuri guda tayi tare da sakin Shassheƙar kukan da bata san sadda ya zo mata ba har eyes ball ɗin ta na ƙanƙancewa jikinta kuma ya shiga rawa jijiyoyin ƙanta na tashi da ƙyar ta samu cikin wani tear out voice ɗinta dake creating ta furta "I don't love him anymore, My life is nothing for him, ba haka ya kamata kamin ba, ba yadda nai zata na samu ba WHO? why? Why pa'apahh da zaka ma zuciyana irin wannan mummunan horon da kai tsaye ze iya illatar da ita. Sake lafewa tay tana maƙale jikin fuskar gadon tare da rufe idanunta tana jin kamar shi ne ya shigo wai yazo ze rarrasheta. Hakan ya sa cikin cira sauti ta furta "Ahhhhhhhh A ahhhh don't touch me! Don't touch me pls paah ka fita a rayuwana kamar baya bana so bana son duk hakan in ba haka ba wllh zan haukace kowa ma ya huta I hate all off you about.......
Sosai zucyarta ke beating very fass,gefe guda kuma ji take kamar ana buga mata wani abu a tsakiyar kanta,dalilin hakan yasa jijiyoyin kanta sukai raɗa² yayinda jikinta ya shiga rawa take ta fara wata irin jijjaga ta fitar hankali.
Chapter 32 · 0% Book details