Sashe 31
Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Aikuwa wani shegen kallo ta sake watsa mata tana riƙe hannun dayay niyar shaƙota hankali kwance babu alamar tsoro kona sisi a idanunta. Cikin zafin rai disgin da yau ne ta taɓa riska kaff cikin rayuwarta ta shiga nuna Meesherh da yatsa cike da tafasan zuciya take furta. "Ke har kin Isa ki raɓe inda Mijina yake har kiyi tunanin tsaiwa dashi!? Wato anga an gama yawon tsaface tsafacen duk babu riba shi ne kike son ɓata masa suna ta wannan hanyar ko? To wllh kinyi kaɗan da ɓata sunan Mijina to ki sani niba takalmi bace ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda kikaga dama dani da Mijina munfi ƙarfin karamar ƴar duniya irin ki wllh" ta faɗi tana wani huci tare da ƙoƙarin son kwace hannunta a cikin na Meesherh ɗin data gasa amsa. Da wani shegen kallon sama da ƙasa Meesherh tabi yarinyan da aƙalla zata girme mata da kamar shekaru biyar zuwa hudu haka. Kafin ta janye kanta wata dariya nason kwace mata don wllh ita sema a yanzu ne ta gane fuskan wato Samha ce wacce ta sani tun basu kai haka ba. "Ohhhh Ashe fa kene wacce aka ce ana daurama pa'apahh Naaaaa Aure dashi buhh congratulations Amma kafin nan Respect your self ok? Don bar ganin kina a matsayin wacce pa'apahh Naaaaa zai aure tsaf idan kika min ba daidai ba zan wulaƙanta ki. Tana cilli da hannun tare da surarn hand bag nata tare da furta. "Hi my enemy friends ku muje ko?" Tayi maganan tana yin gaba cikin takun izza... Ita kuwa Samha tamkar gunkin da aka dasa haka ta kasance tsaye tana bin Meesherh'n da kallo, dan da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata, ganin tana shirin ɓacema ganin tane ya sanya ta furta. "Ke karamar ƙaruwa idan har kin haifu yau a cikin ubanki SAMEER JEDAANS ki tsaya a idd...... Ai bata ƙara sa ba Meesherh tayo wani kalan zaburowa da nufin tafiyar ruwa da Samha ɗin. Domin ita ba mutum bace sakarya da zata ji ana zagar mata iyaye ta iya jumrewa. Se dai kuma chark ta tsaya sakamakon riƙe tsintsiyar hannunta da taji anyi. Hakan ya sanya ido rufe ta buɗe baki tana antaya bala'in koma waye ita ya sake ta, duk da cewan zuciyan ta ya rigada ya gama sanar mata cewan ko waye ɗin kuwa, amma haka ta shiga shure shure tana furta ya sake ta ya barta ta tafi. Be sake ɗin ba sema sake damƙar hannunta. Bakinta dake maganar yake kalla yana ɗan lumshe idanuwansa yayi tare da buɗe su ahankali yana zuba mata su cikin wani kalan sanyi.. Itama idanuwantan masu shegen kaifi a gareshi da yanke haƙuri da duk wani kamewansa akanta ta zuba mishi uwa uba kuma ga numfashinta dake daf da nashi me gauraye da ƙamshin turarenta na tafiya kai tsaye i zuwa cikinsa, Ita kanta ajiyan zuciyan take sauƙewa mara sauti tana rufe idanuwanta ahankali batareda ta motsa ba, domin wannan wani abu ne da tunda ta mallaka hankalin kanta bai taɓa faruwa da ita ba. Saida suka kusan yin mintina biyu a hakan kafin ya juyo da ita ahankali zuwa gabansa chak yana tsaidata kan ƙafafunta tare da zubawa fuskanta nasa Idon yanajin abinda baima San meye yake ji ba, Kansa gaba ɗaya kuncewa yaji yana naiman hakan ya sanya shi ja baya yana raɓata a hankali da nutsuwansa yana barin wurin. Kafe bayansa da idonta da suka kusan tara ruwan hawaye tayi tana kallonsa a hankali cikin yanayin daya sanya numfashinta neman yankewa Amma tana danne hakan a natsen ta kuma ta janye. Tuni Samha kuwa cikin wani irin uban tashin hankalin abinda ya faru da maganar da Sheikh juraij ɗin ya yanka mata akan taɓa koda da farcen karen gidan daya kasance ahalinsa ne ta sake yin ƙurinyi to kuwa tabbas anan ne kaɗai zata gane cewan me aka nufi da hasalin ƙure haƙurin me haƙuri da kaishi bango. Ta bangaren Meesherh kuwa kota kan banzar bata sake biba sema su Aysha da tama magana tare da basu wata farar envelope tace su hau machine. Tunda suka ɗauki hanya suke maida zancen yadda abin ya faru. "Wai kinsan wllh a loƙacin nan har wani zazzaɓi naji na neman rufeni kuwa take?" Caraf Rumaisa ta amshe da cewa "ayke zazzaɓi ma kikace da sauƙi Aysha ni wllh Jima nayi kamar nayi fitsari a wurin ashe haka ta iya wanza almasifatu itama. kai jama'a yaseen ALLAH ka rabamu dayin amai mu lashe abinmu jiday woni faɗan rashin gaskiya a wurin matar cen fa" Rumaisan ta karasa da alamun mamaki tattare da ita. "Wai kam nace ni baki lura da kamar cewa ita ɗayar tamkar tana kishi ne da Aunty Meesherh'n bane? Cewar aysha'n. "Nifa tsaya kiji ma A'isha wllh se da nai tantamar wai wannan itace matar da ze Aura, ke kina ganin ta wllh kinga wankakkiyar ƴar duniya wllh samm basu ma dace ba dan se sukafi ma dacewa da Aunty Meesherh'n" hmmmmm A'isha'n ta kawo ijiyar zuciya tare da furta "Kinga forko dai shi mutum ne wanda ubangijin yayi mishi baiwar ilimin addini dana zamani.kana yana ɗaya daga cikin manyan malam da Afirka kai dama duniyar baki ɗaya ke ji dashi. Sabida a duk ƙiyasin malamai babu yaro matashi mai jini a jika da tarin ilimin addini kamarshi suka gama ratsashi wanda akace tun yana da ƙananun shekaru ya gama haddace al'ƙur'ani mai girma a kansa.kana ga jibgin littatufan dake kansa suma da yake da haddarsu suma a kanshi fiye da zaton me tunani.ga tarin baiwa daraja ɗaukaka amma kuma a ce ya ƙare a wannan abar!?, Ni wllh sammm banma ji ta ko kwanta min a raina ba. Kifa duba kaff girman Kaduna babu malami babba kamarsa daga nan har Lagos kai harda ma sauran garuruwa Kinga nasaba kan nasaba kenan. In kyau ne kuwa na halitta babu ta inda ta isa ta ko kamo tafin ƙafar sane, In kuwa kuɗine ai base an baki labarin ko su waye JEDAANS ba, Shi mutun ne wanda ya gama samun kekykyawan zato a wurin mutanen duniya baki ɗaya, to kuwa kinga tako ta ina ya tserema tsararta kuma bazance wannan aikin asiri bane don wllh ko kaffara bazan yiba duk da ance asiri gaskiyar me shi wanda ko Annabin ALLAH be kauce masa ba amma kuma IN SHA ALLAH wannan asiri bazai taɓa kama shi ba don shi ɗin. SPECIAL ne" Duka a tare suka sauke ajiyan zuciya suna yin shiru kuma suna rasa abin faɗa ma baki ɗaya. ꨄ Sosai aka shiga shirye shiryen yadda ɗaurin Auren Sheykh da Samha zai kasance a duka family biyun,Inda amarya Samha se wani jiji da akai ake za'a auri babban mutum kamar Sheikh juraij Jedaans uwa uba kuma tarin dukiyan dashi kansa bema San adadin tashi ba bare aje kan ta ahalin kuma. Sosai shirye shiryen komai ya gama kankama cikin ƙanƙanin lokacin daya musu saura, iyayen Samha kuwa se aikin banka mata magungunan mata suke. Banda wanda ita kanta Samha'n take banka da ƙawayenta suke kawo mata tsadaddu masu shegiyar tsada. Mayuka kamm na bleaching ai ba'a magana wai duk suma a cikin kaya na gyaran jiki suke. Wanda kuma Ayau ne gidansu su juraij suka kai kayan lefe gidansu Samha, Inda suka sami tarɓa ta girma da girmamawa. Inda babu kunya samha ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su ƴan gidan. Yayinda su papiey ke can suna tattauna yadda ɗaurin auren ze kaya. Wanda cikin masu kai kayan harda Aunty Ummeterh Amma Maah bata je ba. Ita dai Aunty Ummeterh a ranta take ayyana lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa kasancewar itama kamar ƴar gida ce dan sun santa sosai, don wllh ita har cikin ranta take jin tausayin Sheikh ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba'a mafi yawan lokuta. Ita kuwa Samha se wani gani gani take ma Aunty Ummeterh ta dan itama tun kan haka take jin ta tsani duk wani wanda suka haɗa jini da Meesherh haka kawai. Wando da riga ne a jikinta ƙirar ƙasar kuwait inda farin nan ko nace jan nan har wani shuni shuni yake irin me ɗaukan idon nan . ꨄ Ata ɓangaren Meesherh kuwa gaba ɗaya tayi sanyi sosai da zancen Auren ganin dai tabbas gadan gadan kullum maganar da ranakun ƙara kusanto kansu suke se kawai ta ware kanta ta a komawa rayuwarta ita kaɗai babu ruwanta da kowa, sema harkan Film ɗin da take son ta saki a cikin satin da suke ciki shi ya sake dauke hankalinta daga bikin.