← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 37

Sashe 34

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Isanta airport ɗin yayi daidai da lokacin da aka far kiran passengers da zasu tashi. Masu gadin wurin ta bama car key na motan ta. Tsakanin airport da Hotel ɗin da suka kama ba wota tafiya bace me zurfi. Tarɓa mai burgewa da aji akayima su Meesherh a Lagos ɗin tare da luxury masauƙin daya kasance Hotel ƴan wasan suka tanadar mu su,kasancewan ba ita kaɗai bace tare da wasu jarumansu ne harda ma ƙarin wasu fitattu guda huɗu daga kano uku maza ɗaya mace Queen beebee. Ita kuma a nata ɓangaren tana tare ne da Sadja se Bishop tare da London boy da ya kasance shi ne kamar babban yaronta kuma babban amininta a harkan kannywood ɗin dan idan Moh Ameern Saif baya ƙasar to kuwa London boy shike maye mata gurbin Moh, to se gashi ma baya ƙasar baki ɗaya kuma se itama hakan ya mata daɗi duba da irin yadda suke samun saɓanin tsakanin su. Duk wannan abin da ake idanunta na a lumshe ne tanajin yadda motocin da suka ɗakko su ke tsuga uban gudu a saman kwaltan.
zubewa a saman lafayayyar kujerarn dake parlour'n ta na danƙareren hotel ɗin da suka kama tayi lumsansun idanunta na'a lumshe wanda suka ɗan canja launi kada, abubuwa da dama sun haɗu sun  mata yawa a kwakwalwarta ga kuma ƙarin tafiyan da yake tattare da gajiya. buɗe idanunta ta yi tana mai furzar da iskan bakinta haɗe da yamusta fuskanta, zuciyarta na son sake dawo mata da wasu emojis cikin kwakwalwanta, lumshe idanu ta yi ta shiga karanto addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciyarta

_"Allahmma inni as'lukas sabbas fil amr, wal azimatu alar rushdi, wa as'aluka shukra ni'matika wa husna ibdatika,wa as'aluka kalban saliman wa lisaanan sadiƙan, wa as'aluka min khairi ma ta'alam wa a'uzubika min sharri ma ta'lam wa astgfruka lima ta'lam innaka anta allumul gayub"_
Sannu a hankali kuwa damuwan dake damun zuciyarta taji suna raguwa cikin kaso mafi rinjayen damuwarta. Daga nan ta miƙe a kasalance tana shigewa bedroom na room hotel ɗin, amma kafin tayi amfani da komai seda ta tabbatar babu damuwan komi irinsu cctv Camera's da wasu Hotel's din ke sanya wa. Daga nan ta faɗa tayi wonko tunda a daren za'a fara shirye shiryen yacce za'a fara gudanar da ayyukan haska Film ɗin.
A daren ranar ne kuma da misalin ƙarfe 8:20pm suka fita zuwa dan shaƙatawa bisa jagoranci mutanen Lagos ɗin tare da rakiyan abokan sana'ar ta. A wani kyakkyawan ~*PLEX INSURANCE*~ suka yada zango, a ƙayatattun wuraren daya kasance na manya ne dama aka musu masauƙi, inda tuni jama'a dama tarin yan mata da ƴan samari suka kewaye inda suke zaunen, kowa cike da murnan ganin manyan jaruman hausa.
bayyanar waɗansu haɗadɗu fitattun manyan motoci guda bakwai A farfajiyar Plex Insurance ɗin suna shigowa a jere ne ya sanya mafi akasarin mutanen meda hankalinsu kan tarin car's ɗin, kowacce motar kuma ɗauke da tint glass a jikinta yadda na waje bai isa ganin na ciki ba. Kafin kiftar idanu duka ƙofofin motocin suka shiga buɗewa ta hagu da dama. Kamar da kusan 5 minute wani bazaraten matashin chocolate ɗin guys ne ya sanyo sawayen sa woje tare da ziro fuskarsa dake sakaye da face mask woje. Daga yanayin suturan jikinsa kaɗai ya isa sanar maka ko shi ɗin wanene bare kuma azo kan yanayin yadda tafiyarsa take to anan ne kaɗai zaka gane shi ɗin wani ne ta fannin aljihu sannan kuma da alamun sun zarce shekarun samartaka. Tunda daga yanayin yadda zaratan soldier's ke kewaye dashi suna sanya shi tsaƙiyarsu.
Haske daya haskake wurin ne ya sake sanadiyyar bayyanuwar irin kyawun da yake da. A jere kamar masu yin layi haka zaratan soldier's ɗin suka rufa masab baya har zuwa cikin ainihin wurin. Kanta sam sam ba'a wurin yake ba domin hankalinta yana ba'a wurin bane, Harya gitta ta gefensu yaji zuciyarsa tayi masa wani irin bugu, hakan yasa yau sanadiyyar tsaiwarsa chakkk a wurin daidai da lokacin da Meesherh ke ɗago kanta a natse da niyar yima Queen beebee magana. Shanyayyun idanunsa da kusan suke a lumshe ya zuba mata zuciyarsa na aiyana masa anya kuwa itace? Da hannu yama tarin soldier's nashi alaman su je. Shi kuma yana komawa da baya tare da tsaiwa daga seti da inda Meesherh ke zaune. Kusan a tare kowa dake wurin ya wani irin zaro ido alaman mamakin ganinsa a wurin. Sallama ya musu tare da ɗan ɗukawa daga inda take kyakykyawar chocolate Innocent face nashi na bayyanuwa ta hanyar janye facemask ɗin da yayi. Tare da furta "ALLAH yasa banyi gaggawa ko ko kutse a cikin daddaɗan yanayin zaiyi kyau wa Masoya, duk da kuwa cewan niba ba sabon masoyi bane a gareki Meesherh, domin kuwa wannan zuciyar dake manne cikin ƙirjin Ahmed xm ta kamu da SO da tsananin ƙaunarki a rana ta farko dana fara ganinki cikin wani Film na *GANSHEƘA* tun daga ranar wannan zuciyar ta kamu da wata kalar azabbiyar SO da ƙaunarki Ms Jedaans!."
Wani É—an iskan kallo ta jefa masa irin na ka kama kan kan nan kafin ta buÉ—i baki cikin muryanta me nutsuwa ba tarin hayaniya ta ce.
"kai É—in wanene? How dare you talk about my life menene haÉ—in ka da rayuwana Ms Jedaans?" Meesherh ta faÉ—i zuciyan ta na wani irin tafarfasa.
tamkar yasan abinda ke kai kawo a cikin zuciyar nata se ya ɗan rage tsahonsa da yake da tare da furta. "Cikin gaggawa haka Cwty?..... Yay maganar kyakykyawan murmushi shimfiɗe a saman lafayayyar fuskansa, wanda hakan ne ya bama Meesherh mamaki tare da ɗan runtse idanunta kaɗan cikin salon da yafi kama da lumshesu tayi kana ta buɗesu kai tsaye tana zubesu saman fuskar matashin Chocolate beauty ɗin dake duƙe a seti da inda take. Shi kuwa yadda ta tsaida fararen idanuwan tan cikin tsaƙiyar nasa idanunn ne ya sanya shi janye kallonsa daga gare ta.
Wani irin kwarjininta me tarin yawa na bebayeshi karon farko kenan da ya fara jin irin haka kaf tsayin rayuwarshi mace ta masa kwarjini, ɗan numfashi ya fesar kyaunta a zahiri na sake kashesa domin kenan ita Camera's na ƙarama wasu kyau to yau yaga ainihin inda Camera's ke rage kyaun mutum shida akan Diamond Meesherh Jadeens yayi imanin a irin kyan da ALLAH yayi mata ba kowanne namiji bane zai iya tunkararta da sunan Love.
"I'm so sorry Cwty mebi banzo a loƙacin daya dace bane dan haka ki tsimayi dawowana gareki a ko wanne loƙaci" ya faɗi hakan ne yana ajje mata rafas na Dollars.
Yana É—ara wurin Sadja tayi saurin motsowa kusa da Meesherh É—in tana furta. "Ahmed xm Mahmoud Abbas kin san waye shi kuwa? Ai nasam
Sadja ta jefa mata tambayar cikin kwantar da murya da salon da babu maiji sai su ya su. Tamkar ba zata tanka mata ba sai kuma ta motsa laɓɓanta a hankali bayan ta kafe Sadja ɗin da idanunta kyawawa.
"Ban damu da nasan koshi waye ba! Haka kuma bana buƙatar na sani ɗin Sadja right?" Ta yi maganan a sadda take janye idanunta akan Sadja ɗin. "Amma gaskiya kyautu ace kin disga mutum kamar Ahmed xm Mahmoud ba....." Ta gaji da saurarn zancen Sadja ɗin da haka ya miƙe tsaye tare ɗaukan pakega na Chocolate peanut brittle.
Inda kyakykyawan farar ƙafarta dake fes ta bayyana.....
    
_Wannan labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irin sa ba, don kuwa wannan labarin ƙaddarar ne akan wata irin soyayya me tsayawa a zuciya da kuma saka shauƙi a duk a zuƙatan masu karatun amma fa bayan mun gama shan ubanmu ato kaidai kawai abinda zan iya cema shi ne kawai tsammaci abin da baka tsammata ba inji malam bahaushe. Don wannan karon ma AMMEY'NKU tafe take muku da wani salon Rubutun na musamman💐💐💐💪
Heart beat♥️ Heart attach💔 Heart broke 💘_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

*༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻*

_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _
♡
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

𝙋a𝙜𝙚

23&24

https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D

✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfan xz iti da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

Waɗanda suke buƙatar samun litattafan *AMEEY LAYLERH* za ku iya shiga shafin ta na Telegram don samun su kai tsaye daga wurin ta.

Ga link nan ga masu buƙatar shiga
👉https://t.me/ammeylaylerh_novel

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Chapter 34 · 0% Book details