Sashe 30
Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saving da hakan, hannunta har rawa yake wurin amsa call ɗin tare da manna woyar da kunnenta cikin rashin gaza samun cikakken nutsuwa ta mata sallama. Daga ta can kuwa ɗan murmushi mara sauti Meesherh ta saki tana furta. "Kodai an sama matsala row number ne!?" Ai cikin wani irin sauri A'isha ta furta. "A ahhhhhh wllh Aunty Meesherh ba row number bace Ni ce! Ni ce A'isha'r da kika bama N0 naki!" "OK dama nace idan ba damuwa musha ice cream a park na lelewal Jedaans" wani kalan waro idanuwanta woje tayi tare da rufe bakinta gudun hana ihunta fitowa tana furta "okk aunty Meesherh da kamar ƙarfe nawa kenan?" Amsa ta bata da cewan 4:40 kasanwan dama shirye take ita tuni, cikin wani sauri A'isha ta nufi ummanta tare da kunna mata Voice recording ɗin da tay na wayanta da Meesherh ɗin yanzu yanzu. Se kuma ummman jikinta yay sanyi tare da mata adda'an fatan Alkhairi. Daga nan ta shige gidan su Rumaisa da suke makwaftan juna wanda ba bata dade da fita a gidan su A'isha'nba ɗazu. Itama kunna mata tayi kamar yacce ta kunnama ummanta na ƴan gidan su Rumaisa ɗin suka dinga zuwa suna jin wai yau ga A'isha'n Rumaisa nayin waya da JEDAANS Sa'a kenan. Wata yarinya ce ƴar matashiya me suna Baby'n Nuwaira tace "Amma adda A'isha'n Rumaisa idan zaku tafi se kuje gidansu yaya Baby ku aro kayanta ku saka don karta renaku kota muku kallon ƙananun yara" Wani mugun kallo A'isha'n ta wurga mata tana me bata amsa da cewan. "Ai idan kana son mutum dan ALLAH da kuma zuciya ɗaya to zaka so shi ne bawai don ka nuna fariya kodai wani abu dan shi wannan abun ya soka ba, IN SHA ALLAH tamkar yadda muka sota dan ALLAH itama haka zata somu dan ALLAH bawai don komi ba.... Tun kan ta rufe bakinta kishiyar babar Rumaisa ɗin ta tarya numfashin ta da futta, "Yo ai gaskiya Baby'n Nuwaira ta faɗa muku ita kanta Rayuwar duniyar ta koma ƙarya ce yanzu idan zaka nuna kanka as ɗan wani ne kai tofa yanzu zaka zama na kowa, kowa kuma ya dinga rubibinka, amma idan zaka bayyana mutane dama duniyar kanka as ɗan Malam Shehu wllh abotar ma seka rasa da wanda zakayi saboda kowa ze dinga gudun kane..... Itama taryan numfashin nata tay ta hanyar furta. "Amma fa karda ki manta Aunty Mardiya ita duniyar ba taruwa duka tayi aka zama ɗaya ba, kowa ba kamar yacce kike tunani bane! Kuma wllh babu aron kayan da zamuyi duk gamunan da kayan har se mun tafi woni aron kaya dan kawai zamuje wurin Meesherh Jedaans" tun kamin kowa ya sake cewa komai A'isha'n tay ficewanta bayan tace Rumaisa ɗin ta shirya itama ta tafi shiryawan. Se gashi kusan lokaci guda suka gimtsa, ita A'isha'n na sanye cikin doguwar rigar kimono blue black ita kuma Rumaisa sanye cikin riga da sket na wani shadda lece me bala'in kyau kalan pink. Ita Rolling Vail nata tay sakamon ita da tayi Normal yafi da mayafin shadda lace ɗin. Sallama suka sake ma umma harsun fito tay kiransu ta basu 1k tace su hau napep. Godiya suka mata suna tagiya. Ƙarfe 4:40 me napep ɗin daya kwaso su ya sauke su a park ɗin daya kasance mallakin JEDAANS ne. Seda aka musu duk wasu aune aune da tsarin dokar wurin kenan ba'a shiga se anyi check out mutum, ɗan dube dube suka shiga suna son kallar ta inda zasu hango Meesherh ɗin. Wani maaikaci ne a wurin ya ƙaraso yana furta "Are people's that you are talking with madame?" saurin geda masa kai sukai suna furta. "Yeah" Iso ya mudu har zuwa woni tsararren wurin da tamkar ba'a cikin park ɗin yake ba. Kamin gilmawan ido se gashi an cika musu gabansu da kayan motsa baki. 4:57 Diamond Meesherh Jadeens ta bayyana a wurin wanda dama already ta riga da yasan wurin da suken tunda itane ta ware musu wurin zaman ta sanar tun a woya. Suna kallon isowanta duk suka miƙe tsaye suna ganin kamar ba haka bane kamar zata ce ne bata sansu ba ko kuma ta ƙirasu ne d0n buga musu mugun worning akanta. Duk dai jikinsu ba kwarin gwiwa haka harta ƙara so garesu, inda take sanye cikin wasu Fendi riga da wando na mata lightgreen colour. Se fancy goggles ɗin dake manne a idanunta ruwan makuba.Musamman yanda ƙaton gilashin data sanya ya kusan mamaye rabin fuskar tata da sake haskaka farar fatarta. Se wasu shegun fitinannun Heels ɗin dake sanye cikin fararen sawayenta irin me igiyoyin nan ya dauku ba ƙarya, Sosai tayi wani kalan masifan kyau na bugawa a mujalla. "Peace be open you my friends " ta firta cikin daddaɗan Sweet voice nata. A natse cikin kama kansu suka amsa mata suna jin tamkar tasu kolliyar a bola suke dan kawai iyaka Heels ɗin dake ƙafarta sun san sai ya sayi suturar dake jikin kowannen ninki uku uku wai ma fa kar ace sunyi ƙarya ne hakan. Santalelen farin hannunta ta miƙa musu sukayi musabiha, da Rumaisa suka fara yin Musabihan se A'isha'n wacce take ta noƙe hannunta jin da tayi hannun Meesherh'n ɗin wani kalan laushin da yake da ga woni gumi gumin da taji hannun na tarawa, hakan ne ya sanya tay ta ƙoƙarin janye nata amma Meesherh taki sakin mata hannu, se kawai ta ceci kanta ta hanyar furta"Aunty Meesherh barka da yamma" ɗan murmushi tayi tana zama kan royal blue royal icing chairs ɗin da suka zagaye inda suke zaune. Gefe kuma ga tight securities na gidansu dake zagaye da wurin dan tsoron lafiyan Diamond Meesherh. Sosai suka gaisa a mutumce cikin girmamawa daga nan suka ɗan taɓa abubuwan da aka jere a wurin wanda bisa tilas tawan Meesherh ɗin ne ma har suka ci Chocolate tare da juice. Daga nan ita da kanta tayi musu pisc tare da video a woyanta wasu sabbin kwalaye guda biyu ta ciro cikin hand bag nata tare da tura duka pisc da video's din ta cikinsu tabe ko wannensu sabuwan iPhone Wanda ya sanya jikkunansu daukan rawa a tare a lokacin da take sanar musu Gifs nasu ne ta basu suma cikin abinda ta samu a yau ɗin wurin taron da aka hada mata, zamansu babu jimawa wasu arnayen manyan motaci kusan guda biyar suka danno kansu Cikin wurin. Tun daga yadda taji yanayin bugun numfashin ta na sanjawa tasan cewan shi ne ya zo wurin. Daidai lokacin da ya sako kai a natse yana fitowa a car din cikin wani irin kamewa da kwarjinin da yake da, wanda duk girman mutum idan Sheikh juraij na tsaye wuri baka isa ɗaya ido kai masa kallon Ido cikin Ido ba.cike da girmamawa kowa dake wurin sukai ƙasa da kawunansu hatta kuwa securities ɗin dake zagaye da wurin saboda tsananin kwarjinin da yake da kuma tsananin girmamawa a gareshi. Ita kaɗai ce wacce bata janye kallanta a kansa ba sema wani abu me kama da sanyi da taji yana sauƙa a zuciyanta yana mamaye ko ina nata kamar koda yaushe. Domin kaff duniya bata da abinda ya fiye mata kallon pa'apahh ɗin ta daɗin kallo fiye dashi Wani kalan rintse idanuwanta tayi ahankali wani mashi me tsananin zafi na sukar tsaƙiyar ƙirjinta ganin wata koɗaɗɗiyar budurwa ta fito a cikin motar biye dashi tamkar wata bindi ata bayansa. Hakan ne ya nema toshewan numfashin ta ƙirjinta na da zafi da neman jin numfashinta tamkar ya na neman yankewa ne da gangar jikinta Idanuwanta kuma na mata wani kalan yaji yaji, akan kirjinta ta ɗora hannunta ahankali tana karɓan azaba da gashin da zuciyan ta ke mata. Amma duk iya bi kokof ɗin ka baka isa fahimtar ko a wanne yanayi take a ciki ba, hatta kuwa su wanda suke tare da ita harda ma isowan Sadja data kasance tamkar Aminiya ƙwara ɗaya da take da. Cikin tarin nutsuwarsa yake tafiyan zuwa inda babu hayaniyar jama'a sosai kafin ta gama sayayyar da Anniey'n shi ce dole ta tilas mata se yazo lallai lallai ya kawo Samha ɗin. Ta seti da inda suke zaune yazo ze gitta ba tare daya ko san su waye a zaune wurin ba kasan cewan idanunsa ba a kan kallon kowa yake ba. Cike da girmamawa da rawar jiki kaman zasuyi masa sujjada su duka suka miƙe tsaye suna gaida shi cikin nuna girmamawansu gare shi. Dai dai isowan Samha ɗin wurin don ta dudduba bata ganshi ba ita kuma yau ɗin take son burge ƙawayenta da nuna musu cewan lallai Sheikh juraij Jedaans mallakin tane ita kaɗai shi ya sanya ta saka Mommah nata dole ƙiran ƙanwar nata akan cewan lallai maza maza jurai ɗin yazo yakai Samha ƙarashen sayayyar da ba'a mata ba ko park na Jedaans ne. Ai kuwa tana kallonsa tsaye a wurin ta wani taho a fusace tare da tarin friends nata dake take mata baya zuwa inda juraij ke tsaye harma yana niyar tafiya. Ganin Meesherh wurin shi ya sake hassala Samha ɗin domin kuwa kaff rashin jituwar dake tsakanin su ta sani haka ma duk soyayyar dake tsakanin su tun ta yarinta duk tana da labari akan haka. Fuskan Meesherh ɗin kuwa ba ɓoyayya bace a gareta duba da cewan ita ƴar Film ce yar wasan hausa. Tana zuwa babu wota wota ta ɗauke fuskan Meesherh Jedaans da wani kalan shegen marin daya gigita su Aysha da Rumaisa har dama Sadja. Kafin ace Samha ta sake yunƙurin komai taji Saukar mata lafiyayyan marin akan kuncinta tasss, kafin ta dawo hayyacinta ta sake jin an sake wanke ta da woni lafiyayyen marin daya kusan tashin duniyarta. "Babbar magana" Cewar Sadja tana miƙewa tsaye. dafe da kuncinta ta ɗago tana sauƙe idonta a cikin na Meesherh dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi. Mamaki al'ajab da tsantsar ruɗanin su suka taru suka hana su Aysha cewa komai don ma duk jikkunansu rawa ya shiga yi. hatta ita uwar gayyar kuwa wutar kanta ɗaukewa tayi domin abinda batayi zata bane idan tay duba da yacce kowa ke yabon Meesherh ɗin ana faɗin babu ruwanta ita samm. Hakan ya sanya A fusace Samha ɗin ta sake kai hannu da nufin shaƙota Meesherh ɗin,