← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 37

Sashe 10

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarar Alarm ɗin data sets duk asubahin duniya shi ne ya farkar da ita. A hankali ta shiga ware lumsassun idanunta da suke cike da barci har yanzun kana suka mata nauyi.da adda'an tashi a bacci ta tashi a bakinta.
A natse ta ziro fararen santala santalan sawayenta kan tattausan canies carpet ɗin dake gaban gadon, ɗan miƙa tayi haɗi da shigewa cikin bathroom. Alwula ta ɗauro tazo ta fara gabatar da raka'atanil fijr,tana nan zaune da Rabbana Arba'in riƙe a hannun ta na Adda'o'i taji wannan amintaccen sautin nashi na ratsa duka cikin jikinta. Cike da tarin nutsuwa take binsu sallar subhi ɗin.
Bayan an idar komawarta kwance tay tana sake shigewa cikin lallausan duvet É—in ta. Ba itane ta farka se wajajen 11:40 kasancewar weekend ce, Kai tsaye bathroom ta shige tana sakar ma kanta shower. Se da ta É—auki sama da 40mins a cikin bayin kana ta fito jikinta sanye da peach cobbler bathrobe a jikinta, Kanta kuma na cikin fari tass É—in towel mini.
A kan stool in dake gaban 1 mirro'rnta ta zaune kanta ta fara busarwa, kana ta shiga tsane ruwan jikinta. very expensive lotions ɗinta ta ɗauka take levelling lower skin ɗin nan nata me kala dana new born baby Wanda hasalin Luxury da Luxury ya gaka ratsawa. Farar powder me hasalin maiƙo ta shafa a face nata daga haka kuma ta shige cikin closet nata don shiryawa.
Sanye ta fito cikin wani mahaukacin milk and coffee colours One Millions all stones yaɗi halp bubu, Yaɗine me shegen kyau da kuma tsada na manyan yaran ƴaƴan gata. Siririn mayanin yadin ta ɗora iyaka gefen shoulder nata na dama.Kai tsaye Phone nata dake jikin Rinlight already ta nufa. Seta cameras na woyan tay ta cikin tiktok nata. Wannan fitacciyar wakar da tay trend a media ta saki ta Ƴar Arewa. Wacce jarumi Sadeeq sale ya saki, har wani ɗan lullumshewa idanunta keyi. Tana gama yin Vedio'n tayi posting nata a duka pages nata na media, take mutane suka ringa likes kan videos ɗin nata kamar kullum.
Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo kamar yadda ta zata duk iyayentan suna babban parlour'n gidan ne. Tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin tan nan ya gama sanar musu cewar me zuciyar j̶e̶d̶a̶a̶n̶s̶ ce gaba ɗaya ke tafe wato 𝘿𝙄𝘼𝙈𝙊𝙉 Ꮇ𝞔𝞔𝘚Η𝞔Ʀ 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 𝕁𝔼ᴰᴬᴬᴺˢ. Daga gefen Mah ta zauna bayan ta gaida kowa dake dining room ɗin. plate ɗin dake ɗauke da donut, pizza se picanto taja gabanta tare da ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta tare. Metres sarvice ɗin dake aikin shirya kitchen Meesherh ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits. Babu jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyi, da akama yanka ƙananu².
Nanameerah ce ta ɗan kalla inda Meesherh ke zaune ƙanwa Moh Ameern Saif ta furta wallh Aunty Meesherh kalan yadda kike gudanar da acting naki wurin aikin ku na burgeni wllh" Ɗan murmushi me faɗi tay tana kallon Nanameerah'n itama tare da furta. "Sosai mutane ke faɗin wllh aikin mu film na burgesu sosaifa Nanameerah" a tare kuma suka saki murmushi wa junan su cike da shaƙuwa. Annie ce ta kalla sashin da Meesherh ɗin take tare da furta. "Aikin me? Ke yanzu har wani abun kirki da alfahari kika ɗauki sana'ar taki, Ko da yake aifa aikin tallata jiki a yanzun kam shine babbar sana'a a Nigeria"
A rene cikin wani É—an iskan renin wayo da rainin hankali ba tare data ko kalla inda Annien take ba ta furta "Nagode!"
Tsaye ta miƙe da niyar barin dining room ɗin. Abba ne ya kalleta da alamun damuwa a ranshi ya furta.
"Mamana ina kuma zaki bayan baki ko kammala yin dinner naki ba?"
Shafafen cikinta da ba kamar yanzu ta gama cin donut da pizza haÉ—i da picanto ba sam kai ba kace ma kwai Æ´aÆ´an hanji a cikin cikin nata ba. ÆŠan shafa cikin nata tay tare da furta.
"Alhamdulilah na ƙoshi ne Abba"
"Ok shikenan Mamana Ubangiji yay Miki Albarka, da ameen ta amsa bayan ta sake musu sallama don yau tana da wani shooting film da za'a ɗauka wanda Film ɗin tane itane da kanta ta tsara abinta.Har taje bakin ƙofar parlour'n kamar daga sama ta tsinkayi muryawan Ama tana me furta. "Takwarata taimaka ki sauƙe min yayanku a gidan gwaggo Haleemah"
Cike da ɓacin Ran daya kasa dannuwa Annie ke kallon Ama data kasance surukuwa a gare su kafin cikin hucin ɓacin rai ta furta
"Haba ama bayan batama zuri'armu suna da tay, duk hakan be isheku ba sema ƙoƙarin dan gan tata da Mutum tsarkakakke kamar juraij da kuke! Don me ake min haka ne eye? Kodan kawai kina matsayin Yaya ga Mahaifiyata? To ni wllh na gaji nima kawai daga yau ki dawo yimin kallon surukuwarki ba ƴar ki b......
"Zeynab!!!"
Abba ya wani irin ƙira sunanta a mugun tsawacen da ya sanya kowa rawan jiki a wurin. Don ba abu bane daya taɓa faruwa a zahirance duk kuwa irin tijara da jalalar da Annie'n keyi akan duk wani abu daya danganci Meesherh ɗin. I'm sorry Abban jur..."
Ta furta muryan ta na rawa.

"I said get out my friend!"

ya sake buga mata wata uwar tsawar da tafi ta farko ba shiri ta haɗiye maganar da bata ƙarasa taba tana barin wurin don A yadda ta ji muryarsa a kausashe kam ta tabbata babu wasa a cikinta.
Jiki a sanyaye kowa ya shiga darewa banda Mah da jikinta har wani jijjiga jijjigan ɓacin rai da baƙin cike take yi, Sa'ar ta ɗaya sunan ALLAH ne ya fara zuwa bakinta kafin komi shi yasa ta dinga nanata sunayen ALLAH'n a bakinta.

Meesherh kuwa tana fitowa compound na gidan ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama tana riƙe ƙugunta. Nainarh ce tsaye ƙaramar autarsu Sheikh juraij jingine da jikin motar ta. Wani irin kallo Nainerh take watsama Meesher'n tare da furta. "Har ke wa ce ce a cikin gidan nan da har zaki ringa mahaifana meda yawu akan ki gaban mutane?"
Wani kalan sheƙeƙe Meesherh ta mata "Kin ga kenan ke da kanki kin ba kanki cikakkiyar amsarn cewa Ni ɗin wata aba ce me girma a cikin gidan nan, Idan kin gama bani hanya ta zan wuce"
Tay maganar tana kama murfin car nata tana ɗora haɓarta akai, ta buɗe baki kenan da nufin sake watsoma Meesherh ɗin wata rashin kunyar idanunta ya sauƙa akan babban yaya wato Sheikh juraij thabit Jedaans. Babu shiri ta gimtse bakinta tana haɗiye sauran maganar data saura a cikin bakinta. Tamkar kiftar ido haka Nainerh ta ɓace a wurin. Zuciyanta a cunkushe ta shige Motan tana zama mazaunin Driver yayin da ya zauna gefen mai zaman banza. A natse tasa hannunta farare ta kunna motar cikin yanayin nutsuwa take driving nata, Yayin da shi kuma yake gefenta zaune. Ahankali yake ƙarema zara-zaran yatsun hannunta dake kan stearing tana juyawa kallo,me kama da kalan nashi don sosai abubuwan su suke ɗibar kamanni harta da sawayenta kalan nashi ne futiƙ,wani ɗan numfashi ya fesar tare da furta.
"Bani motar nan b.... Ji yay ya tsinta kansa da kasa ƙarasa sunan Babyn da yay niyar faɗi.Se ma lumshe idanunsa dayay tare da shaƙan ƙamshin humranta daya cika motar. Ita kuwa bata kawo komi a ranta ba sema kallon yanda ya lumshe idanunsa tay se taga ba ƙaramin kyau ya mata ba. A jikinsa yaji kallonsa take se kawai ya gyara fuskan da kyau yana jingina kansa da jikin motar, Kamar kuma ba zai yi magana ba buɗe lips inshi a hankali yay tare da furta. "Kallon fa?"
Kanta ta ɗauke wani munafikin murmushi ɗauke saman fuskanta. "Pa'apahh!!!" Ta ƙira hasalin ainihin cikakken sunan shi gareta tun yarinta.Hakan ne ya sanya Idanunsa dake lumshe ya shiga motsasu ahankali yana son buɗe su tare da faɗin. "Buddies kiyi abinda ke gabanki, ko kiban motan!"
Buɗe idon ta da yanzu ne ta lumshe su dama tare da juyowa ta kalli inda yake zaune, iyaka muryansa kaɗai da taji ya sauƙar mata da samun nutsuwa. "Pa'apahh to kace ka yafe min pls" tay maganan da alamun rauni sosai tattare da ita. "Da ki kamin me kenan fa?" Yay maganan cikin ko in kula. "Everything forget itt" Kansa ya dauke a kallonta yana maida shi can kusa da closed windown motar, Itama se bata sake furta komai ba don tasan bayi son maganar kenan.Nuvel script ɗin ta dake gefe ta ciro me ɗauke da photon'nta tana budewa ta ɗaura shi saman gaban motar. A duka sassan jikinsa ya soma jin banbancin yanayi.
Sake buɗe idanunsa calmly akanta yay, wacce ta nutsu wurin driving nata a kuma daidai loƙacin suka kawo ƙofar get na wani makeken ƙaton get. nitsatsassun fararen idanuwan ta da suke nan sakk nashi kawai ta zuba akansa. tamkar wacce bata da wata matsala a rayuwarta tamkar babu abinda ke damun zuciyarta ta furta. "Pa'ap.... Bai bata wani dama na ƙara sa ambatar sunan shi da tay shirin yiba ya fi ce a motar. Wani irin shiru tay tana me binsa da kallo da raunatattun idanunta. dan Shiru tayi na wani loƙaci kana taja kan motar ta tay reverse tana shan kwanar da zata bi. Cikin son shanye komi cike da nitsuwa take ci gaba da tafiyanta kamar daga sama taga wata babbar mota tayo kanta. Tamkar wacce aka bugama guduma haka taji amon muryansa cikin wani shuɗaɗɗen lamari yana furta "Babyyyyyy.....
A wani irin tsiyace ta taka wani mahaukacin birki tare da juya kan motar ta zuwa ɓangaren gabas, wannan babbar motar da tayo kanta na bugar wata motar daban ba ita ba.

★★
Chapter 10 · 0% Book details