← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 37

Sashe 29

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_ꨄ *Meesherh* Zaune take kan wata arniyar farar cough ta a sanye da top irin wannan wanda daga ƙasansu ake ɗinkewa sai crazy 3½, se kanta da yasha gyara sosai na musamman inda ke tubke cikin wata trap band. iPhone nata ne a hannunta tana duba irin yadda mutane keta sake kallar video'nta, da kuma irin ƙalubalantan ta da mutane ke sake yi. Ƙara lafewa cikin cough ɗin tay tare da ɗora wani ɗan ƙaramin rubutu kamar haka. 0o 0o 0o 0o 0o ꨄ _ꨄThank you for sharing your Videos with the world and enriching our lives with your beautiful FAN'S💃💐. May this special day bring you as much happiness as you bring to others. Wishing you endless love, success and fulfillment in all that you do. ❤️ All my love 😍_ tana ɗora rubutun tun kamin ta fita ta fara ganin kalan yacce mutane suka fara kallar short Rubutun tare da dawoata da amsa. Sharewa tayi tana mike ta nufa cikin domin cikin na kukan yunwa ya fara mata. A hankali take tafiyan tana jin yadda sanyin tyles ɗin da take takawa na ratsa mata ƙafafu. Kai tsaye kitchen ta nufa tana fitowa hannunta ɗauke da chocolate na day&night simsek tare da peanut chocolate ɗin dai tamkar ba mutumiyar dake jin yunwa ba. Zaman tay a wurin hankalinta kwance ta ɓare chocolate ɗin ta fara cin abinta har wani ɗan lullumshe idanunta keyi. Haka ta shirirince a wurin har wajen rana daga nan ta miƙe take ta wo wanka, bayan ta fito ne kuma ta nufa shashen mahaifinta. A zaune ta tatar dashi gaban tv screen yana kallln tashar sunan tv, zama tay kusa dashi tana tura dan cuwal ɗin bakinta gaba, "Me ake ma Autana kuma shalelena ne taga se kumbura take ita kaɗai?" Sake tsuke fuska tayi tana amsa remote ɗin dake hannunsa tana sanja channel zuwa wata tashar ta daban. Bayan ta sanja ne kuma ta duba mahaifin nata tare da furta. "Alhamdulillh papiey yanzu kamm jikina ya gama worworewa inas0n zan koma bakin aiki ne!" Ɗan jim papiey ɗin yayi yana auna maganartan a mizanin daya kamata, don ko shi gaskiya a yanzun ya fara gajiyawa da Film ɗin da take yi ɗin. Amma kuma idan yay duba da kamar cewa Aikin Film ɗin nata tamkar shi ne woni kaso mafi rinjaye na farin ciki daga cikin rayuwarta se yaji sammm baya iya hanata Film ɗin. Ijiyan zuciya ya ɗan sauke yana dubanta kaɗan tare da furta. "Dadai shalele ta bari jikinta ya sake hutawa sosai ba da gaggawa haka ba" shi ma yay maganan da son ta yarda da tsarin nashi. Amma samm taƙi ya wanda hakan ya sanya dole papiey yin magana harda Uncle's ɗin ta JAMAAL JEDAANS dama EL-MUAZ JEDAANS mata magana duk da kasancewan su bama sa ƙasar ne, shi Uncle Jameel Yana Islamabad shi kuma uncle El-muaz yaka ƙasar India acan yake da zama. Wanda dama su biyun ne basu zaman Nigeria sosai su kuma ukun sunfi zaman Nigeria daddy'n Juraij se daddy'n Moh Ameern, se Papiey'n Meesherh ɗin. Sunyi ta lallashinta amma da kyar ta haƙura se nan da kamar 2 Week's haka amma tana fita loƙaci bayan loƙaci zuwa *M.L.P MEESHERH LUXURY PRODUCT* har ranar yau data kasance abokan kasuwanci ta sun shirya mata kwarya kwaryar shagalin samun lafiyanta da kuma murnan dawowanta bakin aiki. Tsaye take a wurin da gurds nata sukai parking tsadaddun motocinta daga ta can harabar Hall ɗin da taron zai kasance, Shigowar Diamond Meesherh cikin hall ɗin shi ya sake haukata hall ɗin da sake ɗaukar hankalin kowa suna sake fasa ihun murna na wanzuwar ta kawai tsaye akan diga diganta. cikin takun ta me kama dana ƙasaita take tafiyar fuskarta me ɗauke da shade Glasses yalwace cikin kyakykyawan annuri. Duk wasu wanda suka kamata suna zaune ne a first cough na wurin don kawai kallar yadda Meesherh zata gudanar da Shooting show nata kawai na celebrate ɗin samun lafiyanta da wasu ƙusoshi suka shirya mata. Gaba ɗaya duk kowa da kowa sun bada hankulansu ne ga Diamond Meesherh Jadeens, A natse aka fara gudanar da wasan bayan ta gabatar da kanta tare da jinjina da tarin godiya wa mabiyanta datai cikin harshen English se ɗan sirkin Hausa kaɗan data ɗan hada. Tuni show ɗin ya fara ɗaukar ɗumi fa, masu aikin videorizing kuwa suma nata fama dama photographer da suke ta aikin yin pisc. Gaba ɗaya wurin ya sake ɗaukan shiru kowa hankali da tunanin sa naga Diamond ne. Wasu shigarta kawai datay suke kalla wacce take nan tamkar ƴar sarkin Islamabad ce, saboda yadda tafi kama da ƴan can hakan, domin kuwa dama su ba ƴan hasalin Nigeria bane. Hasalin shi Jedaans ɗin haifaffen ƙasar swizland ne wanda harkan kasuwanci ta kawo shi kasar Nigeria ɗin. Daga nan yazo ya kafa iyalansa dama da komai da komai, amma zaman Lagos suka fara SO kuma dai daga baya me ya dawo Kd ɗin da zama. Cikin salo na jan hankali da tafiya da imani Diamond taci gaba da gabatar da wasan ta tamkar kullum tamkar yadda ta saba, sedai a jinin jikinta yau ɗin take jin wannan Meesherh Sameer Jadeens ɗin dake tsaye gaban dubban al'umma ba waccen Meesherh ɗin ba ce wannan wata sabuwar halitta ce tsaye gabansu. Amma dake abune daya riga da ya zama Real life nata takejin shauƙi da kasancewarta hakan na har abada. Ƙarfe ɗaya da kwata daidai wasan ya tashi kasancewar komi ake yi indai da ita ciki to kuwa indai loƙacin sallah yayi to kuwa tabar ko miye ɗin. Kana tana da wani ɗabi'a sammm ita nata tsarin babu wannan yawace yawancen kwanan su Hotel's haka dadai sauran wurare da wasu actress ɗin keyi samm ita babu wannan a cikin tsarin jaddawalinta. Daga nan masu aikin jaridu da videorizing suka ci gama da naɗar komai har akai komai aka gama aka kuma bata award ɗin da suka shirya mata. Daga nan wasan ya tashi bayan ta ɗan yi dogon bayani da da harshen turanci na godiya wa mutanen da suka shirya mata taron tare da FAN'S nata. Kai tsaye ta sanya aka wuce da ita gida tare da jibgin gifs nata data sama. ♡ Wani irin uban ihu A'isha ta saki wanda ya janyo hankalin Rumaisa dake wanke kanta daga can baya kaɗan dasu. "A'isha kefa yanzu a rayuwa baki ɗaya baki da hankali notikan kanki sun gama kwancewa yaseen" Rumaisa ta faɗi tana maida kanta tare da jan tsuƙa. "Hmmmmm Rumaisa ba zaki gane ba ne kawai wllh amma fa A gaskiya wannan show ɗin ya ƙayatar ya kuma tafi dani sosai, Bara ma ki gani Wllh yanzun zan ɗaura a account nawa na Tiktok da Facebook kai wllh harma da Instragram duk saina ɗaura ɗaukar nan saboda abin sosai ya tafi dani" Wata tsokar Rumaisa taja tana furta. "Ai wllh dama na sani tunda naji kinyi ihun nan nasan cewan bazai wuce akan wannan Meesherh ɗin ba, Matar dake cewa zata ƙira ƙi se yau tashin zance karyar banza kawai" "Ke wllh ni da banji haushin taba ai irin waɗan nan mutanen uziri ake musu kodan ayyukansu da baya karewa, buhh ALLAH Sarki Wllh haushin kaina da kaina ma Ni nake ji da ban ko duba matar nan ba wllh, abin da ciwo sosai." Tana fadar hakan ne kuma tare duba wayarta wanda yayi daidai da sake sakin uban ihun murnar data saki me ƙarfi a karo na biyu, sakamakon duba wayartan da tayi taga yadda cikin ƙanƙanin lokaci hakaa amma mutane sama da 1k sun mata like harda masu comments ma akan video'n Meesherh kawai data ɗora. Kamar kuma da wasa kamar a mafarki taga Diamond Meesherh Jedaans cikin jerin masu mata like harda ɗan takaitaccen comment. Kafin ta wani yi baya luuuuuu kamar zata faɗi kwance daga zaunen da take tana dafe setin Heart nata, da ƙarfi kuma kamar wacce aka zabura ta furta. "Na shiga ɗaka na kasa fitowa ni A'isha yau wacce kalan Sa'a gareni Umma! Umma!! Umma!!!" Haka ta shiga kwalama mahaifiyanta ƙira kafin kuma tamkar wata filfilwa ta falla a guje har tana kusa kaɗe mahaifiyanta da itama ta fito ɗin a tsorace jin uban ƙiran da ƴar nata ke mata tamkar tashin duniya. Har rige rigen ƙarasawa gurin ta Ummih da Kilan keyi domin ganin abin da ke cikin wayar nata da ya sakata ihun murna haka. wani cafka Kilan takaima woyar dake a hannun Aysha ɗin, dake dama already tana cikin Tiktok ɗin ne ya sanya Kilan ƙanwarta me bi mata kallon komi. Wata nannauyar ajiyar zuciya Ummih ta sauke lokacin da take kallan abinda ya sanya ƴar uwar nata murna da ihu haka loƙaci guda Ita dai Ummah tana daga gefe tana kallon ikon Allah don ma ta gaza ƙarasowa. Ƙara zaro idanu woje Kilan tayi ganin uban likes da comments ɗin da yayar nata keta ƙara samu a take se sake shigowa suke babu ƙaƙƙautawa. "Aunty Aysha Ina harda FB kika daura kamar dama Instagram ma ko?" Da kai kawai ta mata alaman ehhhhhh ita kuma tana shiga sema taga ashe likes da comments ɗin dake cikin facebook da Instagram ɗin ma har na neman fin na Tiktok ɗin kuma dai shima Diamond Meesherh Jadeens tayi mata like duka. Ɗagowa tayi cike da zallan farin ciki ta buɗe baki kenan da niyar yin magana ta hango Ummah tsaye daga inda take daskare tamkar wacce akayi Freezing nata. Da hanzarin ta kilan ta ƙara sa ga umman tana me furta "Ummah wllh zo kiga Ikon Allah" tsoki kawai ummansu A'isha'n ta buga itama kamar dai Rumaisa ɗin tana komawarta inda ta fito, don dama tana kitchen ne tasha ma wani mummunan abun ne ya faru lokacin dataji irin uban ƙiran da ake kwakwara mata. 4:15 duk zaman ya ishe ta haka nan kawai taji tana son zuwa park ta hutawanta, tamkar kuma wacce ake umarta haka ta sama kanta da cll na No ɗin yarin yan Ranar data amsa tun a wancen ranan, tamkar almara tamkar a mafarki haka A'isha da take zaune tana ta aikin dudduba yawan like da comments na jama'a taga ƙira na shigo woyanta me ɗauke da sunan *Sweet Diamond* tun a wancen ranar data bata Id card nata tayi
Chapter 29 · 0% Book details