Sashe 22
Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ita Rayuwar duniya da kike kallo tana iya juyama ko wanne baya ajin da yake tamkar yacce Rayuwar mutane ita take iya sauyamana a duk lokacin datay niyar sanjawar, People change, things go wrong. Just remember life goes on Sauyi na rayuwa yakan zo loƙaci ɗaya ne. Wasu loƙuttan kuma sauyin kan zo ma na da yarin ƙalunale n rayuwa ne. No one is born with Positive Passion. This Power is ignited by Inspiration!Komai na da alaƙa da yanda tsarin ƙaddararmu take. Ko yatsun hannuwanmu idan kika duba suna da banbanci da junansu. Saboda me mu zamu tsaya ɓatama kanmu loƙaci wajen ja da kaddararmu data zamo iri ɗayace. Gode wa ALLAH ya kamata muyi yayin samu ko rashi. Don bamu isa ja da hukuncin Ubangiji ba, Amma idan mukai haƙuri Allah na tare damu a ko wanne yanayi adda'an mu SAMEESHERH take da buƙata bawai kuka ba!!. Silalewa a wurin Maah tayi hannuwanta da ƙafafunta na rawa ta zame ƙasa tana son tayi koda numfashi me ƙarfi ne amma ƙirjinta ya toshe ya tsaya mata cak wani abu me nauyin gaske na danne mata ƙirji zuwa maƙoshinta. Paah kuwa Idanuwansa ne suka wani irin ja yana kasa hana hawayen sa zuba sosai shima.A cikin su biyun duk aka rasa me rarrashin wani ko me be wani kwarin gwiwa a cikin su, domin kuka suke sosai suna haɗe kansu a wuri guda suna riskar kuka, cikin kukan Maah take furta "Meesherh dan ALLAH karki tafi ki barmu kece sanyin idaniyanmu ya Rabb ka kawo mana ɗauki Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" Jajur idanunsa suka se a yanzu ma yake tunowa da gida dan haka kai tsaye woyan sa ya ciro yana ƙiran babban yayansa thabit Jedaans.
Sanar musu yay halin da ake ciki suma se hankalinsu duk suma ɗin ya tashi don haka suna yanke woyar a washe garin ranar su daddy dama duka sauran families suka biyu Flight zuwa ƙasar SPAIN ɗin. Se ganinsu kawai su Prof ɗin sukai amma juraij be zo ba kasancewan ma ashe shi baya a ƙasar ne ma. A kuma washe garin ranar wanda yay daidai da kwanan Meesherh biyar kenan a kasar aka shiga da ita aikin daya gama kassara jikin kowa. A kuma daren ranan ne Sheikh juraij thabit Jedaans ya dira a ƙasar spain ɗin wanda babu wanda yayi tsammanin ganinsa. Domin kuwa can Ƙasar Sudan ya tafi, tun a daren aka fara mata aikin har zuwa ƙarfe 5:30 na asuba. Kum Alhamdulillh aiki yayi kyau sosai sai fatan farfaɗowanta lafiya da kuma adda'ar ta tashi lafiya ƙalau IN SHA ALLAH. Haka suka dinga fitowa fuskansu ɗauke da murmushin cimma nasara a aikin nasu.Suna fitowa baki ɗaya duka Family'n JEDAANS sune cike a compound na hospital ɗin tamkar wanda suke a Nigeria. Dr John Amaan ne cikin murmushin jin daɗi da kuma ƙaunar Ahalin JEDAANS ɗin ya miƙa ma Prof Sameer hannu yana furta. "Congratulations Sir anyi aiki cikin nasara da kuma dacewa IN SHA ALLAH zata farka cikin hayyaci da nutsiwanta, kana anyi mata gyaran karayan da tayi se nan da Awa shida zuwa bakwai za'a fiddota, daga nan se adda'an fatan farfaɗowarta gaba ɗaya kuma" hannun Dr John Amaan ɗin sosai papiey ya riƙe ya kasa saki yanaji tamkar Meesherh ɗin ce ma gabansa tsaye haka. Dr John na barin wurin su daddy suka ringa rungume ɗan uwan nasu suna taya kansu murna. Ganin irin farin cikin dake kwance tattare da fuskokin kowannensu ne ya sanya wasu hawaye wanko fuskan prof Sameer ɗin. Daddy ne ya ƙira gida Nigeria yana sanarma Ama da kuma JEDAANS TURAKI nasararn aikin da akay.♡
 ✯ Ranta a mugun ɓace bayan ta zagaya ta bayan asibitin ta ɗauki woyanta kai tsaye tana dokama Dr Maheer da yake can a tsare ƙira.Domin kuwa sunyi da shi lallai Meesherh bazata tashi ba se kuma gashi taga saɓanin hakan. dan sun gama yi dashi zaiyi duk abinda zaiyi ya kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar ta katse ba'a ɗauka ba. Maida akalar ƙiran kan wata nurse da zasu aikin tare tayi tana jin yadda zuciyar ta ke tafasa, Ba ƙaramin sake haukacewa Mameey tayi ba kuwa ganin itama ba amsa. Hakan ya sanya ta ringa zazzaga bala'i, Ita da tazo ganin yadda iyayen yarinya'n zasu zauce hankalindu ya tashi daga nan suma in yaso su haɗiyi zuciya su mutu, Domin ita macece data rayu da tsantsan kishin Maah da papiey, kasamcewarn sune gaba ɗaya ƙarfin tattalin JEDAANS ɗin. Kana sunfi kowa Power a cikin family dama sauran dangi duka. Wannan shi ne dalilin da ya sanya ta rayuwa da ƙiyayyar Maah da papiey, dama sauran yaran da suka haifa se kuma akalar tsanan nata ya koma kan Meesherh a loƙacin data gama fahimtar Meesherh ce ta kasance zuciyar kowa daga cikin Jedaans ɗin. Hakan ne ma ya sanya ta cusa babban ɗan ta Moh Ameern Saif shiga ƙarƙashin Meesherh ɗin shi kansa ba tare da yasan mi hakan ke nufi ba, domin Mameey irin makiran matan nanne masu shegen iya takunsu da taka tsantsan wajen iya tuggunsu. A zahiri ma idan kai rayuwa a JEDAANS kai tsaye itace mace ta farko da zaka fara sheda da cewar ita kaɗai ce mace ta kirki akan sauran matan. A loƙacin da ta buɗi ido kuwa taga kalan shaƙuwan dake tsakanin juraij da Meesherh zaucewane kawai batayi ba. Tun daga loƙacin ta shiga ta fita seda taga ta raba ƙarfin alaƙar dake tsakanin su kana hankalinta ya kwanta. Itace nan ta sanya a kan garar mata da Meesherh ɗin hakan be yiyuwa ba, shi ne ta sanya aka ɗora mata masifan don kiɗe kiɗe kuma bayan hakan bawai ta barta bane don so tayi ma ta zama tantiriyar karuwa lamba ɗaya,Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne kuma ba azzalumin bawan sa bane, dan hakan data aikata sai hakan beyi tasiri akan Meesherh ɗin ba. Bata so hakan ba amma ya ta iya dole ta haƙura. Kuma itace take sake sanya muguwar tsana me ƙarfi tsakanin Maah da kuma anniey To yanzu kuwa inhar ba ganin gawar Meesherh tayi ba to kuwa lallai zuciyarta ba zata huta mata ba.
Tun Meesherh na yarinya Mameey ta gama ruguza rayuwarta wanda badan tsarewar Ubangiji ba da tuni wani zancen ake ba wannan ɗin ba. Don bayan a sanya mata jin tsanar juraij ɗin harda taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa Mameey ta sanya a sakawa Meesherh ɗin duk ita kaɗai. Duk loƙacin da taga ƙarfin aikinta ya soma rawa zuwa take ta sanya a sake rura wutar tsanar dake tsakanin juraij da Meesherh, Anniey da Maah, sedai bokan nata sau tari yakan faɗa mata cewar destiny ɗin Meesherh da juraij a sarƙe suke kuma daɗi da ƙari shi duk wani aiki da za'a buga a kansa baya ko tunkarar inda yake balle har yay tasiri akansa, Sedai sunyi amfani da rashin jin maganar ta da kuma daɗe gangarar da Iran da suke shi ne salon aikin kawai dake tasiri a cikin aikin juraij ɗin yana sake jin Meesherh ɗin na ficewa a ransa gaba ɗaya. Da yadda itama baza'a bari ta so shi kamar dai baya koda kuwa na minti guda ne, Kai hatta mahaifinta mameey bata bari ba seda taso sanya mishi tsanar ƴarsa ta cikinsa wanda jinin dake gudana a nashi jinin shi ne ke gudana a cikin nata jinin jiki. Dan haka ƙarfin jinin dake yawo yana zagaya tsakanin su ya hana mata cimma burin ta, se gashi ma a maimakon kowa yaƙi Meesherh ɗin se ya kasance kowa tamkar an buɗe zuciyarsa ne an ɗiga masa mugun ƙaunar Meesherh ɗin ne, dan ta kasance ma tamkar itane zuciyar JEDAANS ɗin baki ɗaya. Sa'ar ta ɗaya shi ne kawai dama can akwai ƴar tsama tsakanin Maah da kuma anniey wanda kuma dama irin dan faccalanci ɗin nan ne haka, se tay amfani da wannan damar ta sake rura musu wutar tsanar junansu haka kawai, sedai aikin ma kusan zamu iya cewa iyaka akan Anniey'n ne ke tasiri kawai don ita Maah bawai tsanar Anniey'n take ji ba abinda kawai bata so shi ne a wulaƙanta ko yaranta. Wanda dama hakan kuma can ɗabi'ar Anniey'n ne kodan ita ta kasance jinin Ama ce oho wacce take ganin ai ita dasu daddy'n duk abu ɗaya ne,tunda mahaifiyarta ita ce ta kasan yaya ga Ama ɗin dan hatta Auren ta da Daddy Ama ɗin ce ta haɗa, kasancewarn daddy'n Juraij ba mutum bane shi me ƙin biyayya ga mahaifansa hakan ne ya sanya shi amsan Auren Anniey'n babu musu. Da shigowarta gidan ita kuma ganin ƴar uwace garesu ya sanya take son seta mulki sauran matan dake gidan tunda ita ɗin jinin suce.