← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 37

Sashe 1

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH

*♡SPECIAL☆*
_Ta daban_

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
~Na Maryam Naseer Mirrah~
_AMMEY LAYLERH_
Page 1&2
_ÆŠAN ÆŠANO_

*NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA*. _NIMCY LUV_ Ban manta kalan gudun mawar da kika ringa bani ba a littafi na na baya wato MIKIYA. TO haka za wannan ma da Salonta labarin ze fara SEY MA SHA ALLAH.Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humi darling, my Mummy'na, my support system, my role model, i love you_
*_Special Thanks to:_*
Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke
Love you all 💞💖💘💗💝
♡♡♡♡♡♡♡

The official trailer for *SPECIAL* {Ta daban} (2025) introduces Novelist to a chilling😄💃, suspense-filled Power Romance thriller set in an isolated, post world. Directed by MARYAM NASEER MIRRAH *AMMEYLAYLERH* SHEIKH JURAIJ THABIT JT follows.
*♡SPECIAL☆*must evade capture while uncovering hidden truths about her past and her connection to the cult’s terrifying leader. The trailer teases
In a world where trust is a luxury and survival is the only rule.

Alhamdulillah masoya na Asali am back dawo muku da wani fitacce kuma ƙayatacce ƙasaitaccen labarin dazai ƙayatar daku💃, Bazan iya misalta muku meya ƙunsa ba sai inhar kun biyo alƙalamin AMMEY LAYLERHbAnan ne kaɗai zaku fashimta inane alqamin ya dosa🪷, fatar baku manta da ƙayatattun littatafan nan nata ba irin su.
*MIKIYA*
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*ƘAUNA BIYU*
*SANYI YA HAIFA WUTA*
And Ongoing
*♡SPECIAL☆*
Fatan baku manta da yadda kuke nishanÉ—an tuwa da duka littatafaina na baya ba. Iyaka waÉ—an da suka karanta littafinta na MIKIYA to kuwa sune zasu fi kowa bada yadda waccen tafiyar ya kaya. Se dai wannan ma is not free book shima yazo ne a paid amma kafin nan akwai free page da zan ba *MASOYA* Masu bibiyana.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
*_KADUNA MARAFA_*
~012 Alongside films shot~

Cike ƙaton hall ɗin yake da mutane babu ko masakar tsinke.kowa ka kalla zakaga fuskansa na ɗauke da annurine. Dan kuwa kalla ɗaya zaka ma fuskokin nasu ka gane lallai suna cikin farin ciki ne matuƙa. Se dai wasu tsirari daga cikin jama'ar dake cike tab da hall ɗin suka soma kallar wrist watch ɗin dake ɗaure da hannayensu suna jan tsuƙa can ciki ciki. Wasu kuwa suna a cikin yanayi ne na shiru fuskansa suma yana fara sanjawa zuwa na damuwa. Domin kuwa idan har akace yauma Babbar jaruma kuma fitacciyar ƴar wasan Hausan nan wato *DIAMOND MEESHERH* ba zata samu halartar wannan shooting trailers ɗin ba Lallai kuwa da akwai babbar damuwa. duka mutanen dake zaune a hall ɗin zaka kalla lallai yakai ya kawo ya kuma taka wani matsayine tabbas, ko daga yanayin murjewan jikkunansu da kuma uwa uba tsarin da hall yake da.
Wani shahararren tallane na ADD companies Wanda manyan ƙusoshi suka haɗaka wajen gina shi, Tsaye tsammm shi kansa shugaba a companies ɗin ya miƙe ganin wasu har ransu ya soma ɓaci. Ehhhh lallai tabbas kuwa da haushi ace yau har kimanin kwanaki uku kullum a jere suna taruwa iwar haka amma haka suke bajewa ba tare da an gudanar da TRAILER na ADD companies ɗin ba.
A dai-dai loƙacin ne kuma wata farar mota samfurin ƙirar Toyota Highlander ta yi parking a harabar hall ɗin. Cikin yanayi na sauri² wata farar matashiya amma ba can ba ta fito daga cikin motar tana sanye cikin wani baƙar
pleate skirt sai farar oxford shirt wadda ta ɗora maroon suit a kai,wuyanta saƙale da tie se silver band ɗin dake kanta, gashin kanta wanda ya ji gyara an ɗaureshi cikin pony rail ya zubo har gadon bayanta. ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers. A kuma daidai loƙacinne hall ɗin ya ɗauka wani kalan ihu na tarin masoyanta, har wasu na tsalle wanda suke daga waje basa da ikon shiga ainihin inda za'a gudanar da Trailer ɗin.Hotuna wasu suka fara ɗaukanta wasu na aikin video wasu na ɗaga takardu masu ɗauke da sunanta me haɗi da tallar ADD companies.ɗaya daga cikin security female ɗin dake zagaye da wurin ne tayi saurin isa ga DIAMOND MEESHERH tana saƙala mata Symbol na tallar da zata gudanar.
Cike da mutsuwa take tafiya Fuskarta rufe da mask, ta rufe fuskar ne kuma saboda bata son takurawar jama'a, duk da kasancewarta mutum me nuna so da ƙauna ga masoyanta, Fuskanta da kai tsaye ba'a gani ta zare mask ɗin dake kan fuskan nata ganin ta faranta wa masoyanta Rai. Wani twisting na ihun murna mutanen suka sake saki suna jin ƙaunarta na sake ratsasu. A natse cikin wannan ɗan banzar izza da mulkin da duk wani ahali daya kasance ɗaya daga cikin ahali na *JEDAANS POWER MENTION* to kuwa kowa yasan *_Respect and peace_* ake ƙiran duk wanda ya fito daga wannan Ahalin. Tafiya taci gaba dayi harta dangana da kan stage na hall ɗin. Tun kamin ta kai ga shigar manyan mara masu gwara kan nera yaran ajebor suka ɗauka wani kalan ihu suma harda ma waɗan da suka ɗan manyan ta bi ma'ana dattijai masu rukunin ADD companies kenan. Microphone ɗin da wannan macen security ta farko ta sake maƙale mata ne ya sanya sakin kyakkyawan murmushi tan nan me kyau. Nan aka soma gudanar da duk abinda ya tara sun bayan ta nemi afwan su akan cewa wani uzirine me girma ya ɗan riƙe ta. Seda ta ɗan rumtse idanunta sakamakon tunowa da musabbabin hanata fitan kai tsaye. Bayan masu camera's sun gama haskata kana suka buƙaci data ɗan gudanar musu da show haka koda ba me yawa bane. Cike da wannan fara'an da son farantama masoyanta Kamar yadda suma suke faranta nata ranta ta soma gudanar musu da wani zazzafan show ɗin daya sake haukata ƙaton hall ɗin. tana tsaka da gudanar da show ɗin ne kuma Moh Saif Ameen turaki ya bayyana shima cikin hall ɗin nan sukaci gaba da gudanar da show ɗin a tare. Sosae yanayin ya musu daɗi Kamar yadda suma fam nasu suke jin daɗin show ɗin na yau, dan burin ransu ne ya cika A yau gasu ga manyan masoyansu,Suna gudanar musu da show a tare wato *DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* da kuma *MOH SAIF AMEERN JEDAANS* Cike da jin daɗi da kuma farin cikin kasancewar su a tare Masoya suka shiga ihun murna. Tsitttt kuma hall ɗin yay sakamon tsaya wa da sukay suna kallon masoyan nasu.
Ihun murna masoyansu sukaci gaba dayi haka har taron ya tashi, Moh Saif ne ya zagayo ta inda Diamond Meesherh ke tsaye bayanta zagaye da security. Hannunta ya kama bayan mutane sun gama murnar yin pisc dasu kai tsaye har inda tay parking car nata ya kaita seda ya tabbatar da shiganta kana shima ya koma yana jan tashi motar ya rufa mata baya. Sun zo daidai shan kwanar
Mobil filling station na round about wani shegen goslow yay blocking na hanyan.
Ɗan tsuki kaɗan tayi tana jin gundura da zaman motarn baki ɗaya hakan ne kuma ya sanya Meesherh Jedaans fita don ganin ko me yay blocking hanyan har haka. Duk da kasancewar face nata rufe yake cikin mask amma hakan be hana wasu ƴan mata biyu da suke cikin napep kasa gane taba. Wacce face nata ke waje tana leƙen woje ta window'n napep ɗin ta furta "Laaa A'isha kalla can ki ga kamar Diamond Meesherh Fa?” ta faɗi cike da ɗaukin ganin babbar jaruma kuma sananniya a duniya. Da sauri wacce aka ƙira da A'ishan itama ta dawo da kanta setin inda ake nuna matan, "Wllh kuwa Rumaisa itane da da gaske!" Ta faɗi tana ɗan zaro idonta woje alamun mamaki.
Cike da zumuɗi wacce aka ƙira da Rumaisa ta sake furta.
"Kinga tashi don Allah muje muy photo"
Ɗan numfasawa A'ishah tayi tana sauƙe numfashi tare da duban Rumaisa tana me furta.
"Ki na ganin zata yarda kuwa Rumaisa? Karfa ki manta cewa Diamond Meesherh ⭐ Cikakken sunanta *Meesherh Sameer Jadeens* wannan shine full name nata bayan haka kuma role models da duniya jeji da ita gaba da baya. A yanzu haka ita kanta Meesherh Jadeens na ɗaya daga cikin world billionaires da duniya ke ji dasu ta gama zama cikakkiyarn attajira a loƙacin data mallaki manyan company's dake tashe a ƙasashe daban daban. Bare azo ga ahalinta kai tsaye kuma. Kana ƴa ce ga Sameer Jedaans Kuma sanin kankine kamar cewar Meesherh Sameer itace zuciyar duka alhalin Jedaans baki ɗaya! taya kike tunanin ma zata tankamu bare ma harta kula mu?.Sannan kuma kin manta cewan duka wasu campanies da zaki kalla na *MEESHERH LUXURY PRODUCT* Ina nufin M.L.P fa nata ne ko kin manta kamfanine da suka lashe maƙudan dukiya wajen ƙirƙiran campanies ɗin kawai.
Wanda bako wanne kamfani yasamu irin wannan shaharar ba bayan latex cars da campanies nata suke ƙera ma duniya. Kana tana da hannun jari da wannan shegen campanies ɗin nan da ake sarrafa laptops, iPhones da suke ƙerama duniya da duk wasu nau'o'in na'urori kolo daban daban. Wato babban Ɗa ga JEDAANS kuma me Jedaans ɗin baki ɗaya wato *SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS*"
A'isha ta ƙarishe maganan tana fesar da numfashi me ɗan zafi daga bakinta.
Chapter 1 · 0% Book details