← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 37

Sashe 36

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Down town mall*
Akai Akai take yawan duba hanyar mall ɗin da sama da 50 minutes. Wanda kai tsaye Aunty Ummeterh ce da take shirin komawa garinda da take da aure tace Meesherh ɗin ta kaita mall don ALLAH. Tun da ta kawota taƙi motsawa ko ina wanda ada zaune take a cikin car ɗin saɓanin yanzu da take jinge da jikin car nata.
Sanye take da wata tattausar exclusive atamfa da bata tara yawan tarkacen kololi ba,hatta da zanen jikinta kuwa baida wata hayaniya sosai SO simple ne, Sai kalolin da suka dace da yanayin jikinta da aka raɓama atamfar, ɗinkin doguwar riga ne daya buɗe sosai daga ƙasa,daga saman kuma ya zauna mata cas kamar dama can don ita kaɗai aka halicci atamfar dama ɗinkin jikintan gaba ɗaya. Ta lulluɓe kanta da wani madaidaicin mayafi wanda yayi set da kalan shigan dake jikinta, Amma duk da hakan sai da Wannan kwantaccen gashin dake zagaye daga gaban kanta ya fito luf luf abinsa,wanda duk bayan minti ɗaya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin tana sake rufe gaban kan nata da kyau, domin ita ba mutum bace me son bayyana gashin kanta wai don ado ba. Wannan hali nata na tsantsan tsare dokokin ALLAH shi kaɗai ke sanyaya zuciyan duk woni Masoyinta dake mata soyayya ta don ALLAH.
Wasu lafiyayyun plate shoes ne a ƙafarta Heels masu shegen kyau da matuƙar tsada mahaɗin ƙaramarn handbag ɗin dake a hannunta ne wanda suke mahaɗin company guda na Dior lv.
Tana tsaye jingine da jikin car nata hannunta ɗaya na riƙe da wayanta amma duk da hakan bai hanata harɗe hannayen taba a ƙirji, kyakkyawar fuskar nan babu digon fara'a ko kaɗan sai ma ɗan ƙaramin bakinta da take motsawa kaɗan bada yawa ba, alamun dake nuni da cewan magana take yi amma kuma cikin bakinta dake mamulawa.
Har yanzun guri ɗaya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa da kallon wurin da take ba har ranta na neman ɓaci, domin a rayuwanta abu mafi muni da tafi tsana shi ne wasting time. Wanda take jin wllh badon Ummeterh bane da tuni ta bar wurin shi yasa ita samm bata sayayyar kai tsayen nan tafi son komai tayo oder nashi tana kwance daga cikin gidansu. Cikin abinda bai wuce 20 minutes ba sega wata rantsatstsar black RR car nan ta shigo cikin wurin. Wani irin harbawa taji zuciyanta yayi a take hakan yasa bama tasan lokacin data lula Duniyar tunani ba, Sai kawai wannan unique ƙamshin da tun garkon haɗuwansu na farko ta gaza mance kalansa ba ne ya bugo yana kawo mata ziyararn kai tsaye. ɗago idanuwanta masu kyau tai tana kallonsa. Sanye yake da Ash balmains na wata crazy shirt me shegiyar tsada da straight wando sai tsadaddun cover shoes ɗin dake ƙafarnsa na ballies wanda kodan yawan sanyasu ɗin da yake ne ya sa kai tsaye zaka gane cewan shi ɗin soldier ne. ɗauke kanta take son yi daga face nashi, sedai ta gaza hakan don wani irin sabon kyaun da take daɗa iya kalla me kyau, wanda kyaun yafi yanayi da irin morning beauty ɗin nan ko ko dai muce morning freshness. Duk yacce taso ɗauke kanta daga kallonsa gaza hakan tayi domin kuwa fin ƙarfinta zuciyarta tai ta kasa ɗauke fararen idanuwanta akansa tana masa wani irin kallan da ita kanta bama tasan tana masa ba. Shi kuwa tunda yay tozali da kyakkyawan face nata tsananin azabtuwan da zuciyarsa yay akan sonta da yaƙi barin Heart nashi ne ya sa ya kasa ɗauke idanuwansa daga gareta harya yana ƙoƙarin loosing control nashi gurin bayyanar da hakan har idanuwansa nason cikowa da wani abu da yafi kama da hawaye kai tsaye. Fitowan Aunty Ummeterh daga cikin mall ɗin ne ya katse shi daga buɗe bakin dayay da niyan mata magana ita kuwa Aunty Ummeterh'n ba tare da tama lura da wanda ke tsayen ba ne ya sanya tace "I'm so sorry bestie mun tsaida k......
Se dai bakinta yay shiru ganin wani a tare da Meesherh É—in, hakan ya sanya ta naÉ—e sauran maganan datay niyan yi É—in kuwa. Shi kuwa Ahmed xm kallo É—aya yama Ummeterh É—in ya fahimta cewan Aunty nata ne don haka cikin wayewa da class me aji ya gaida Aunty Ummeterh'n tana amsawa tare da kallon Ummeterh É—in tana furta. "Meesherh wannan kuma fa?"Cikin basarwa ta furta "Ban sani ba aunt nima kawai ganinsa tsayen nai kamar yacce kika ganshi" Tayi maganan tana mai sake ignoring nashi Dawn.
ꨄ
*Sheikh juraij*
Farkawan kenan daga baccin bayan la'asar ɗin data konta hakan ya sanya ta tashi a ɗan hanzarce don sanin yanzu duk inda yake ya dawo. Duka ɗakunan gidan ta shiga dubawa sedai babu shi hakan ya sanya ta leƙa compound, sesai ganin car nashi daya fita da itane ya sanya ta sake komawa tama sake dudduba sauran ɗakunan. Da kyar ta sama ganinsa a cikin wani Master bedroom nashi tayi masararn samun shi wanda yake kwance kan tsakiyar Raoun bed nashi me tsananin laushin da kai tsaye idan mutum ya kwanta yake yin luf ya lafe cikin bed ɗin. Kana sanya ƙafarka kuwa a cikin parlour'n abu na farko da zai fara maka maraba, Shi ne sassanyan ƙamshin turaren da humidifier ke bayarwa. Wani gajeren numfashi Samha ta ja yana nufar kan bed ɗin. Har zata tashe shi se kuma ta tuna da ya hana mata tashinsa se kawai ta juya bayan ta gama bin jikinsa da mayen kallon da bata sama gani ba dake lulluɓe da dubet tabar room ɗin. Shi kuwa ashe duk abinda take yana jinta kawai ya sama kan sane a wani yanayi na daban wanda tun jiya Meesherh taƙi barin tunani da kuma kansa. Inda yaki wani mayen feelings nata kamar ze kashe shi amma ya danne hakan. So da dama har gani yake kamar shiya ɗorama kansa hakan na rashin feelings ko wacce macen dake duniya se ita kaɗai. Gani yake kamar ALLAH se iya tashinsa da laifi akan hakan, wanda a daren jiya bayan ya dawo shi da kansa yake har room nata da niyar kasancewa da ita tunda yaji feelings nashi ya motsa. Sedai tamkar abin asiri yana shiga room ɗin nata kallo ɗaya kawai ya mata yaji farar ɗaya feelings ɗin na ɓacewa ɓatt. Wanda hakan yaso tashin hankalin sa sosai domin yana tsoron ALLAH ya kamashi da hakkin Samha a kan sa, Shi ne abinda ya hana shi fita duk a ranar yau ɗin. Kuma da ko tuna sunan Meesherl ɗin yayi se yaji abun ya motsa masa kamar ya karshi. Bayan fitan ta da kamar 15 minutes ya miƙe a natse bada garaje ba yana faɗawa cikin toilet.

Kayan dake jikinsa ya zare lafiyayyar farar fatarsa na bayyana tana ɗaukan ido saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. shower ya sakarma kansa ruwan dumi yana rufe idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna dumama jikinsa a hankali.
Ya jima sosai sosai yana wankan kafin ya fito ɗaure da babban towel me kauri brown jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Da Mini clean blue towel ya shiga tsane jikinsa a natse. kafin ya shiga shafe jikinsa da bodymilk da mix na oils na diamon dia da suke saka jikinsa glowing da kyan gani da wani irin soft ya shafa perfs dasu bodyMist da sauransu, kafin ya gyara fuskansa yai brushing gashin kansa dayake a kwance da santsi irin na asalin ustazan larabawa.
Bai woni ɗauki loƙaci ba sosai ya shirya kansa cikin wani brawn cashmere daya nutsu a jikinsa saboda tasan kuɗin da ya lasa. A cikin tarin tsadaddun designer agogayensa dake jere a doguwar glass drawer'n ya buɗe yana ɗaukan ɗaya ya saka a hannunsa da gargasa ke kwance luf luf gwanin birgewa.
A natse ya fito shirye fess zuwa ainihin parlour'n sa da ko ina a parlour'n yake neat ba hayaniyar komai a parlon komai is so gentle unique simple and luxuries ne kawai ke magana a parlour'n kawai. A babban parlour'n ya yada zango yana ɗaukan ipad nashi ya shiga duba jerin schedule ɗin da aka turo masa ta cikin Gmail nashi. Anan yaci karo da bayanan da ya bada cikin sirru a duba masa dangane da accident ɗin daya faru da Meesherh. Duba komai yayi zuciyan sa na ƙona ganin sunan Moh Ameern dumu dumu a cikin jerin list na wanda aka lissafo masu hannu a cikin case na accident ɗin.
Idanunsa yaja yana lumshewa abinda ke ƙoƙarin taso masa yana maidasa da ƙarfin adda'a.

ꨄ
Chapter 36 · 0% Book details