← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 37

Sashe 7

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

★Tun da jirgin su yay landing a babban filin jirgin suka fito har suka fara tafiya Kansa a ƙasa yake hannuwansa kuma tttare cikin cashmere ɗin dake jikinsa, Taku yake yi cikin natsuwa sai dai kallo ɗaya zaka mashi kasan cewa ehhhh lallai Sheikh juraij jarumin namiji ne sosai mai jini a jika wanda kyaun jikinsa ke ɓoye hasalin shekarunsa. duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai sedai yanayin murjewan fata dana jiki kawai wanda hasalin Luxury da Luxury suka gama ratsawa,SE dai Yanayinsa kaɗai zaka kalla ka tabbatar da cewan lallai ba lafiya ba.Amma wannan karamci da kuma tsananin kwarjinin sa suka shanye yanayin san na ɓacin rai, Cikin hanzari Personal person ɗin sa Al-Ameen Hafeez yay gaggawan buɗe masa Toyota Avalon ɗin da yake da tabbacin itan ze shiga. Yana shiga shima yay hanzarin shiga yana amsan driving ɗin daga hannun. Mustapha Haroon da yazo ɗaukan su tare da rakiyan bodyguard nashi. ♡ Se wajajen yamma liss Meesherh ta fito dan tana da wani zaman meeting da company'n *MEESHERH LUXURY PRODUCT* {M.L.P} Wanda tun safe aka so gudanar da zaman meeting ɗin, sedai kasancewar bata tashi da lafiya bane ya sanyata ɗaukan Excuse tun a daren jiya. Sosai Meesherh tasha kwalliyarta cikin wasu dogon wando da riga, malesian dress wandon yana da faɗi sosai kamar palazo, rigar kuma ya fitar mata da shape ɗin ta sosai,Inda rigan yakai har zuwa gwiwanta ya tsaya, sai ɗan ƙaramin veils ɗin sa data rolling sannan rigan irin me igiyar nan ce ta wajen cikinta,se ta ɗaure igiyar a baya hakan yasa rigar ta kara fito mata da shape ɗin ta sosai, flat tummyn nan nata shape nasa ya bayyana, Sosai tai kyau sedai matsalan shape ɗin ta daya fita sosai shi ne ya ɓata mata kwalliyan nata. Cikin yanayin ɗan jin ƙarfin jiki take saƙƙowa daga stairs nata, a parlour'n ta tarar da mahaifiyar nata zaune kan Sofa se kayan fruits veggies in dake gabanta.
"Ahhhhh Masha Allah Baby,kice sauƙi ya samu tunda har kika sama daman fita" Mah ɗin tay maganan fuskanta ɗauke da murmushin ƙaunan yarinyan nata. Ɗan zama tai gefe da ita Apple ɗin dake gaban Mah ta ɗauka tana cin kaɗan. "Ehhhh naji sauƙi sosae Mah! Kinsan yau ina da meeting shi ne ya sanya dole zan fitan" shafa kanta Mah ɗin tayi tare da mata adda'an dawowa lafiya da kuma cimma nasarar ta a koda yaushe.
Ita kaɗai ta fita duk da securities ɗin Papiey'nta sun so bin bayanta amma ta buga musu shegen warning akan karsu daddara su bita. A kuma daidai loƙacinne shima Moh Ameern Saif ke fitowa daga nasu ɓangaren da shirin fitansa tsaff, magana ya soma mata sedai samm ita Bama ta jishi ba haka yata buga mata uban horn amma sam bata san da cewan itane akema hong ɗin ba. Wayarsa dake gaban motar yay saurin ɗauka yana dokama lambarta ƙira bakinsa cike taff da addu'ar ALLAH yasa ta cira, ai kuwa adda'an nashin ta karɓu don ring ɗaya ta daga, wani kasaitaccen murmushi yay tare da sanya woyan a amsa kuwwa yana me furta.

"Meesherh Sameer Jadeens laifin me nayi dana cancanci wannan horon?, Tun jiyan kin sanya zuciyata a tsoron kodai na aikata ba daidai gareki ba!"
Wani Banzan numfashi irin na ɓacin ran nan ta fesar still taƙi yin magana. Shi kuma hakan ne ya sanya shi sake furta "Meesherh"
"Naam" Ta amsa a karon farko tunda farkon fara woyan nasu. "Pls ki tsaya muyi magana don Allah" kitt kitt kitt haka yaji ƙaran kashe masa woya da tay. Samm bata san biye yake da ita ba kamar yadda bata san shine ya ƙirata ba kasancewan amsa woyan kawai tay ba tare data ko duba me ƙiran ba. Cikin wani kalan ɗan iskan driving taci gaba da mirza steering car nata hankali kwance, idan ka ɗauke ɗan ciwo² da kanta ke mata har yanzun amma bada yawa ba kaɗan kaɗan yake harba mata. A kyakykyawan Parking car ɗin da aka tanaja domin Parking motaci ta Parker nata motan. Tun kamin ta gama daidai ta Parking motan ta ma'aikatan wurin suka zagaye motan ta cike da girmamawa. Iyaka Lugagge bag nata dake ɗauke da system nata ta ɗauka a motan, se eye glasses ɗin ta data maida saman face nata, Cike da kuzarinta da kuma kwarin gwiwan ta ta ziro da fararen sawayenta tana fitowa gaba ɗayanta.
Fitowan ta a car in kenan taku ɗaya tay ana biyun taji an wani irin riƙo Hannuwanta. Ai a wani irin fusace cike da tsantsan ɓacin rai da tashin hankali ta jiwo don ganin uban daya aikata mata hakan. Sedai idanunta be sauƙa ana kowa ba se akan Moh Ameern Saif. Aikuwa Babu tantamar komi ta wanke kyakykyawan fuskanshi da marin daya cilas tashi janye hannunsa dake cikin nata. A kausashe a kuma faɗace ta shiga nunnunashi da manuniyar yatsarta. "Ina son wannan ya zama shine karo na ƙarshe da gangar jikinka zata ci gaba da baka haɗin kan sake kusanta kanka gareni Mohammed Ameern Saif" ta ambaci full cikakken sunan shi. Wani kalan shegen kill smile ya saki ya ɗan yin luuuu da idonsu da suka jaaaa na ɓacin ran shima, Sake matsowa dap da ita yay tamkar ze shige jikinta se kuma ya sake sakin wani shegen murmushin irin na cikakkun ƴan barikin nan masu aji.
"Na sani! Na sani!! Na sani ba sekin sake maimaita min ba Meesherh Sameer Jadeens tana dakon soyayyar wanda yake mantawa da itama a tashi rayuwan, nasan duk waɗan nan abubuwan da kike yi pretend ne kawai kike a gaban mutane sedai ki sani rainin hankalinki samm ba zai yi tasiri a gareni ba, saboda ina son ki tuna da cewan tare kike da Moh Ameern Saif Jedaans wanda ya gama sanin sirrinki tsafff don haka care your manner take a good calamity" yay maganan da raɓata yana komawa cikin car nashi fuskansa ɗauke da Murmushin cimma nasarar shi gareta.
A hankali cike da jin ciwon abinda ya aikata mata haka taci gaba da ratsa cikin company'n, cikin yanayin nutsuwan data zame mata dabi'a,tana takawa a hankali ƙamshinta da kuma yadda shigar ta amsheta kaɗai na sake jan hankulan jama'arn dake cikin company'n.
Yadda take ɗaukan hankulansu haka kwarjininta ke sake baibaye masu kallon nata, gashi dai a zahirance dai ita ce Wannan shahrriyar jarumar da kullum suke kallonta a poster ko a photo ko video, sedai yau da sukai ido biyu da ita duk se wasu da suke jin suna da kwarin gwiwan mata magana da haɗa ido da ita harma da tarar ta se kowa ya gaza yin hakan. Saboda yadda tsananin kwarjinin ta ya riga da ya gama baybayesu da ɗi da ƙari yadda fuskanta take a tamke. Tamkar irin kunun ƙanwar nan da aka dama ba'a haɗa shi ba haka fuskanta yake a wannan loƙacin.
Tun daga nesa ta hangi Muhsin Aliey Yahaya zaune cikin tanfatsesiyar car nashi, ya zubo kafafunsa woje hannunsa riƙe da kwalbar da ta tabbatar da cewan wine ce. Sosai taji ranta ya saƙe ɓaci a karo na biyu tana jin mi yasa abubuwa da yawa ke son yawo da kuma wajiga rayuwanta haka?. Tamkar bata san da wanzuwarsa a wurin ba haka tazo ta gitta shi ta fice abinta. Sedai shi ɗin ma ko taku cikakken uku batay da gitta shin ba yasha gabanta. Tun daga sama har ƙasa ya shiga binta da fitinannun shegun idanunsa haka harya sauƙe daman ƙirjinta da kuma cikinta dake lafe cikin shigan riga da wandon dake jikinta. Wani shegen numfashi yaje a sanda ya shaƙi ƙamshin mayen tularenta da yake bala'i bala'in ƙauna kamar me, cikin dakakken sautin amsa amo da kuma kuwwa ta furta. "Muhsin Aliey bani hanya na ce!!!" Ja baya yay kafin a hankali ya fara motsi da jajayen laɓɓansa, cikin muryan da ya fara tafiya da maye yake furta. "Meesherh kince na baki loƙaci na baki, kince na kaucewa ganinki a ko ina na kauce kince kince kince abubuwa da ya wa duk nabiatakan amma kuma loƙacin da kika ɗibar min sun cika kuma kinƙi bani damar taya kike tunanin zan baki amsa ba tare da kin amshi tayin soyayyar da nake mahaukacin yi miki ba!" Kanta ta kawar gefe zuciyanta na tafar fasa kamar me don wani loƙacin ita kanta bata san yadda ake take gaza sarrafa fushinta akan koma waye ba, kamar few minutes ɗin nan data ɗauke fuskan Moh da zazzafan marinta da babu wasa. Babu zata haka ta fisgen kwalbar wine ɗin dake riƙe a hannun sa tana buga mai a fuska tana raɓa gefen sa ta wuce bayan tama security ɗin umarnin su fitar dashi a company'n kar kuma su bar kome kama dashi ya sake shigowa. "Meesherh don nace ina sonki shine har kike jin kina da kwarin gwiwan wulaƙanta Ni Muhsin Aliey Yahaya jarmai, to wllh kin yi kuskure mafi muni a cikin rayuwankin kan wulaƙanta nin da kikai" daga haka yay wurgi da securities ɗin ya faɗa Motarsa yana ɗibarta da gudun hauka ya fice gaba ɗaya daga harabar company'n.
Chapter 7 · 0% Book details