← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 37

Sashe 26

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Yaya jikinki" loƙacin da yake ƙara sa saƙƙowa cikin parlour'n.
Kallansa kowa yayi dukkaninsu duk da ba sauti yayi maganar cikin natsatstsen Sautin sa. Ɗauke kanta Maah tayi tana miƙewa ta nufi upsaid nata. "Mama kun dawo lafiya? Ya kuma sauƙin jikinta" haka ta tsinta muryansa da ameen kawai ta amsa tana ƙara sa barin wurin. Mameey ce ta zo ta kama hannun Meesherh'n dake daskare a wurin tana haurawa sama da ita, don wani mugun baƙin cikene taji ya turniƙeta ganin yau dai a gaban idanunta bayan tsayin shekaru masu ɗan dama sun yi magana, wanda a da ko gaisuwa bata haɗa su. Kai tsaye bata zauna a ƙayatacen falonta da aka sake gyara mata shi ba ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom nata kai tsaye.
Ita kuma Mameey'n tana fita zuciyan ta na raya mata kamar tabi Meesherh ɗin kawai ma ta shaƙeta harse ta mutu. Duguwan rigan jikinta kawai ta sutale tana faɗa cikin Lafiyayyan toilet nata da yake da girma sosai komai kuma a tsare, ƙamshi ne me sanyin daɗi da nutsuwa yake tashi a cikinsa. Ruwa masu ɗumi ta haɗawa kanta tana fara yin wankan a natse ƙamshin shower gel ɗinta me kyau da tsada yana sake tashi, haka harta gama wankan ta kashe shower ɗin tare da miƙa hannu ta janyo towel ta ɗauro a jikinta ta fito cikin Lafiyayyar bathtub ɗin ta nufi gaban mirror'n daya kusan cike rabin bangon toilet din ta tsaya cak ta zubawa kanta fararen idanuwanta da suka sanja sakamakon ruwan da suka shiga cikin su. Hannunta na dama ta sanya ahankali ta dora daidai setin Heart nata tana jin zuciyarta dake bugawa akan a hankali. lumshe fararen kyawawan idanuwanta tayi tana sauƙe numfashi ahankali me dumi. ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta ta fito, Anutsen ta ta zauna kan stool na mirror, blow drying gashin kanta fara yi tana kama lallausan gashin kanta tayi parking nashi cikin woni mini riboms, wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta ɗauka ta feffesa ma gashin, sannan cikin sanyin da jikinta yayi ta shafa lotion masu sanya laushi tayi. Ko inda parfumes suke bata kalla ba domin bata a mood me daɗin da zata iya tsayawa zaman sanya wan.
Cikin clothes na kayanta ta shige wasu nude riga da wando dogwaye masu ɗan faɗi ta sanya. Wow ko Ni AMMEY LAYLERH saida nace ma sha ALLAH dan there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka akan ta ba, don wani kalam masifar ƙyau tayi cikin kayan tamkar wacce taje hutun honeymoon ta dawo dan yadda farar lafiyayyar fatar ta ke ƙyalli cikin kayan, tabbas Meesherh me ƙyau ce idan nace ƙyau ina nufin ƙarshe maƙura kenan. Kan lafiyayyan gadon ta kwanta tana Sake lafewa a cikin lallausan fari ƙal ɗin duvet cover ɗin ta.
Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji abinda yay mata tsai a zuciya na komawa ya kwanta luff cikin tsaƙiyar Heart nata. Moh Ameern ne ya shigo har cikin bedroom ɗin kasancewan se yanzu ne shi yake dawowa daga wurin aiki. Zama yayi dap da ita sosai yana ƙoƙarin yaye duvet ɗin da take ciki. Saurin ƙanƙame duvet ɗin tayi se a yanzu nema take sanin da mutum ya shigo mata ɗakin. Cikin matuƙar ɓacin rai da gajiya da ire-iren abubuwan da Moh ɗin ke mata ta furta.
"Shin babu zuciyane a ƙirjinka wai Moh Ameern? kokuwa dai kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?, Ji ina ƙarshen haɗuwana dakai last worning na ƙarshe dana maka akan kusanta kanka gareni ne! Na ce ma banaso banso bana so to ka ƙyaleni mana"
Meesherh ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai. Kafe ta yay da idanunsa da suke kamanceceniya da nata kasancewar kusan duka family's din kwayar idonsu kala ɗaya ne fara ƙal seda na wani yafi na wani haske.
Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin shegen eye glasess ɗin da manne idonsa dashi, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba ko nuna yama ji zafin maganar nata se ma furta. "Hope jikinki yayi sauƙi kenan tunda har kika sama bakin tsiya haka"Ya sake faɗa a hankali yana janye idanunsa akanta. Kin sake yanka shi tayi sai kawai ma woyanta data ɗauka tana manna Bluetooth a kunnenta ta doka ƙiran syster Ashley Agar da tayi babbar aminiyar datai acan ƙasar SPAIN.
Woyarta ta shiga yi da Syster Ashley Agar tana ma mantawa da woni halitta kusa da ita. Shigowan Maah ɗauke da plate na farfesun tsokar Mana datai ne ya sanya Moh Ameern tafiya.itama ta sanja kayanta daga wanda tazo dashi zuwa plat riga da zani na less mara nauyi ko kaɗan.zama tayi kusanta tana ɗan rungumo Meesherh ɗin zuwa jikinta, woyar ta nuna mata alamar woya take. Sunan kuma Ashley datay ne ya sanya murmushin Maah sake faɗaɗa domin Ashley da families nata ba mutane bane da zasu iya mancewa dasu cikin sauki don sune suka maye musu gurbin Family'n JEDAANS tattare dasu. Amsan woyan Maah tay tana furta. "Ashley doter se kika fara ƙiran bestie Mee taki kenan kafin Maah ɗin ko?" Har yanzu fuskanta ɗauke da murmushin. "Wllh Maah ba haka bane Besty Mee ita ne ta ƙirani Maah tambayar ta kiji ma" dariya kaɗan Maah ɗin tayi nan dai suka ɗan tattauna dangane da yanayin jikin Meesherh din. Daga nan suka yanke woyan ita da kanta Maah ta tayar da Meesherh ɗin zaune toilet ta kaita ta sake ɗaurayo mata bakinta ta sake dawo da ita tana bata naman a baki. A haka papiey ya shigo ya tarar dasu tare da tsokanar Meesherh ɗin da Shalelen kowa. Murmushi kawai tayi ƙaunar mahaifin nata da duka Family'n tan ma na sake zagayeta da jin alfahari dasu a ko ina take kuwa.
♡
Se bayan sallar Isha'i kowa da kowa ya sake fitowa zuwa babban parlour'n gidan. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda juraij sedai shi be juya ba tamkar yadda sauran su suka juya. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance a cikin jinin jikinta yake, wanda ba koda yaushe ƴan jiji dakan ke tashi ba se ko in woni ya taɓo ta koya ɓata mata rai. To kuwa duk yanayin da take a ciki bata jumrewa se asalin jiji da kan na da gadarar sun motsa tabbas. ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya tana jan idanunta ta lumshe su luff tana jiran taji me mata magana daga cikin tsageru da marasa haƙurin gidan tsaff ta tsefe su don daidai take jin kanta dasu. Wani shegen murmushin Mugunta anniey a zuciyarta ta saki a cikin ranta tana furta.(shegiya dan ubanki yanzu kuwa zanyi maganin ki, dama wannan ranar nake ta dokon jira).
Kallon inda juraij ɗin yake zaune tayi cikin son ta ɓakanta ran Meesherh da uwarta ta furta. "JURAIJ amma yau ya kamata ka leƙa gidansu Matarka *SAMHA* ko?" Ta ƙare da alamar tambaya. Duk parlour'n babu wanda be ɗago ya kalleta ba idan ka ɗauke Maah dama ita kanta Meesherh'n, bawai don maganar bata shige ta ba a ahhh wani irin mugun bala'in bugun zuciya hakan ya haifar mata wanda har kusan sarƙewa numfashinta yayi amma ta yi saurin daidai ta kanta, Shi kuwa juraij yi yay tamkar bema jita ba hakan kuma dayay seyama daddy daɗi, don ba ƙaramin kunya Anniey'n ta bashi ba gaban Prof ɗin duk da kasancewan ƙani yake gare shi amma ai ba daɗi hakan. Duba da cewan a yau ne ƴarsa ta dawo daga zaman jinya har wata ƙasa, dan dama already kowa da kowa dake gidan ya rigada ya san da zancen Auren juraij ɗin, wanda uwarsa ce ta jajirjice har seda maganan tayi ƙarfi. Idan ka ɗauke Meesherh da uwar dan hatta Mohan Sameer yasan da maganar auren Sheikh din. Kuma wani tsantsan rashin kunyan ma ga anniey a loƙacin data tunkari mijinta da maganar ya mummunan ɓata mata rai akan kada ta yarda ta sake tararsa da zance me colour da wannan yayi, seta koma gun papiey'n Meesherh.wanda shi ne ya shige gaba akan komai har aka tsaida maganar watanni biyar masu zuwa gashi yau har anci kusan 3 Months kenan, wanda a lissafi bikin befi saura nan da 2 Months ba inma ze zarta to da ƴan sati kai ne.
A natse ya miƙe daga zaman cikin tafiyarsan a natse ta zallar nutsuwar da ALLAH (S .W. T) yamar ya fice daga parlour'n baki ɗaya. Wanda har Annie ta so yimay magana amma wani kallo da Daddy ya mata ya sanya ta gimtse bakinta ba shiri.
Don ba haka taso wasan ya tsaya haka nan ba.
Chapter 26 · 0% Book details