← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 37

Sashe 20

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Welcome to Spain and Portugal Specialist hospital analyzing*
 
Dake magana ake ta kuɗi da kuɗi kai tsaye tun a daren ranan aka wuce da ita special screening room da ita. Dr John Amaan shi ne kan gaba wajen fara aikin. Dr Maheer Osman da ya kasance bahaushen ƙasar Nigeria ne tare suka ringa duk wani shirye-shiryen fara ma Meesherh aiki. Farin glass ɗin dake sanye a idanunsa Dr Masheer Osman ya gyara tare da kallar inda Dr John Amaan yake tsaye yana ƙoƙarin haɗa wata ruwan Injection."No Dr ba buƙatan wannan Injection ɗin! *Keep him under anesthesia"* wani kalan waro idanunsa waje Dr John Amaan yayi cikin kamilallen English ɗin daya gama riƙa a bakinsa ya furta.
"Amma His life'd be in danger if we give him an overdose I can'ttake that risk, don haka ba zanyi mata wannan allurarn ba" Wani shegen murmurshi Dr Masheer yayi saying tare da furta "Do as I say?" Kallonsa da jajayen idonsa da suka surku da ɓacin rai Dr John Amaan yayi tare da furta. "Watch and See, it will be really fun and hilarious, Maheer reshe ne zai juye da mujiya kikayi kuma ya koma kan masheƙi,don baka san match ɗin da kake shirin taroma kanka bane. Kasan kuwa ita ɗin wacece? Kasan kuwa ko su waye Asalin JEDAANS!!!?"
Tsaye Maheer ya miƙe tareda murtuke fuska ya furta "Enough... Enough is enough! Enough of it Mana kada fa ka nemi raina min wayo anan john kaine ma wato zaka faɗa min ko su waye JEDAANS ɗin?, To ƙarewanta daga tacan familyn JEDAANS ɗin ne aka bani maƙudan kuɗaɗe dan kawai na kawar da rayuwar yarinyar"
"Uhmmm kaifa Maheer na gama lura baki É—aya baka san zuru ba"
Ɗan ware idonsa Maheer yayi tare da furta "Lallai ba shakka kuwa da dukkan alamu kaima wani daga cikin su ya maka tayin babban kamu ne duk yacce akai" Shima cikin ɓacin rai da ɗaga murya cike da ihu yace.
"But you are the causer Maheer bcoz at ever never naci amanan wani Kona ha'ince woni"
Da sauri  Maheer ya ɗan girgiza kai tare da kwantar da murya yana furta
"Cool down John please ni nasan hanyar da  zamu bi muyi handling ɗin yarinyan ba tare da barin wata ƙofar da za'a iya zargan woni abu ba kawai mu fara aikin"
"Maheer zaka fara  ko? Okay then mu buga wasan aka wanda zai cin ye" ♡ A can masauƙin su Prof Sameer kuwa suna isa aka shige dasu wani lafiyayyan parlour'n jira ko wannensu zama yayi cikin yanayi mara daɗi da yanayi na cunkushewar zuciya. Prof ne ya fara miƙewa tare da dauro alwula ya fara kai kukansa ga mahaliccin sa akan neman sassauci daga garesa, ganin hakan ya sanya ita ma Maah tashi ta fara gabatar da nata duk da bata a mood me daɗi, ko wannensu da abinda zuciyarsa ke saƙa masa.
♡
Around 5:15
Bayan kusan kwanan tsayen da sukai akan Meesherh suka samu numfashin ta ya yakawo sau ɗaya. fitan su da kamar 15 minute wata muguwar ƙara ta karaɗe iyaka room ɗin da Meesherh take. Hakan ya sanya a guje duk wasu manyan dactor's sukai room ɗin a guje. Turus John Amaan ya tsaya yana kallon Maheer dake tsaye kan Meesherh wacce kallo ɗaya zaka mata indai kai cikakken dactor ne kasan cewan tabbas babu numfashi tare da ita.
♡
Kallon me kake nufi John yake ma Maheer Scowl ɗin dake fuskarshi yana ƙara zurfafa, da kuma fuskan mamaki John ɗin ya ɗora da faɗin. "Maheer me ne kai ma patient ɗina?"
Da kalan kallon Mamaki da kuma rainin Hankali Maheer ke jifan John tare da kuma da furta "What is with the look? Kana mun kaman baka san da komi ba? Bayan kuma kaine kace mu buga wasan, toni yanzu ne nawan ya soma don haka in kana dawowa da wanda ya riga ya sheƙa numfashi seka dawo mata dashi ba iyaka allurar anesthesia na mata ba harda crecenial risk na mata" Girgiza ma Maheer kai John yake yana ja baya. A cikin zuciyar kuma yana tabbata lallai duk inda ƙarshen mara Imani yake to kuwa ga babansa don a yau ya sake tabbatarma da kansa cewan Maheer samm baya da zuciya a cikin ƙirjinsa, don ko shi da yake Christian wllh ba zai taɓa iyama ko dabba bane wannan allurar. Cikin wannan goggagan turancin irin wanda se a ƙasar turawa kawai zaka iya jinsa,Dr John Amaan ya juye baki da muryarsa mai tafiyar da yannayin halitar zafin sa kai tsaye irin na ƴaƴan arna ya shiga balbale Dr Maheer da ruwan masifa, domin dama Maheer ya daɗi yana musu irin wannan ɓarnar don kawai saboda wasu ƴan kuɗaɗe da yake amsa. Abu ɗaya ne kawai ya Dr John Amaan ke rufa masa asiri shi ne tsoratamar hukuncin ƙasar su da yake. Amma yanzu tunda shi bai san zuru INSHA ALLAH daga kan wannan patiend ɗin ba zai sake ƙoƙarin aikata woni kuskuren ba. Don haka ya bama Dr *Randeep Hooda* da *Dr Jackie Shroff* umarnin su kama Maheer ɗin. A natse cike da cikata aikin ogansu a fannin aiki suka sanya ƙiran Hukumar Asibitin suka zo suka tafi da Maheer ɗin. Amma dake ɗan bala'i ne memakon kaga ladamar hakan a ransa sema baki da ya taɓe tare da kallon Dr John ɗin yana furta masa zasu haɗe.
Kallonsa shima yayi tare da sauran ma'aikatansu da yannayi na Expression É—in fuskarsa ya furta
"Ban sanya an kama ka don aikata S0n raina bane maheer, kawai dai na yi mamaki ne a matsayinsa na jinin Musulmai kuma a same ka da aikata babbar ɓarna irin haka wajen taɓarɓare addininku, da kuma rugujewar tarbiyar irin ta ƴayán Hausa. Musulunci'n da ya riga da ya gama gina tarbiyyar ƴaƴansa wanda har sauran wasu yaren ke sha'awan shiga cikin ku, saboda yadda tsarin addinin Musulincin ke burge su, to kuwa tabbas irinkune masu danne niyar masu son musulinta da masu muguwar zuciya irin taku"
Ya ajiye maganarsa hankali kwance yana ƙoƙarin ganin ya haɗa wata ruwan allurar da iyaka ita kaɗai idan kaji kuɗinta kan ruguza ƴaƴan hanjinka. Kana ya buɗe wata na'urar computer'n da suka gama rufewa a ɗazun. Kasancewarsa babban likitan da ko a sauran ƙasashe ji ake dashi ya fara sarrafa wasu abubuwa daga cikin ta. tsari irin na wanda ya gama laƙantar abin ya shiga sarrafa ta,seda ya ɗauka wasu lokuta masu ɗan nauyi kana ya rufe yana sharce zubar data gama jiƙa gaban goshinsa wata ƙatotuwar damuwa na rufe shi.

   Kusan a tare Prof Sameer da kuma Maah suka miƙe tsaye ƙirjinsu na wani irin bugawa, jin wannan ƙarar data karaɗe ilahirin cikin Hospital ɗin.Allah sarki cike da raunin rai dana ruhi suka kalli juna sai dai duk cikin su babu wanda ya iya furta wani abu. Kai tsaye suka nufa room ɗin zuwansu daidai loƙacin da kunnuwan Maah da papiey suka jiyo masu wannan mummunan tashin hankalin. A take anan Maah ta zube sumammiya cikin sauri nurse's suka dauketa suna shiga wani room na daban da ita.

A hankali Maah shiga buÉ—e idanunta da take kallon komi dishi dishi.
Hannunta ɗaya ta ɗaga da ƙyar ta kamo na Prof Sameer wasu zafafan hawaye na silalo mata daga cikin idanunta. Cikin rawar murya ta shiga furta ,"Da gaske mun rasata ko? Da gaske mun rasa Meesherh ɗin mu ko" sai kuma ta taci gaba da hawaye tana ɗan jujjaya kanta.
        Ƙasa papiey yay da kansa shima hawayen na ƙoƙarin ciko nasa idanunn. dan baya da tabbacin Meesherh ɗin tana a raye ne ko a mace,Cike da matsanancin tausayin kansu da kansu ya zame hannunsa daga cikin na Maah ɗin ya miƙe. Saurin riƙosa Maah tayi tana girgiza masa kai. "Please Prof ka faɗamin gaskiya wllh ba zan yi komai ba bazanyi kuka ba kaji na rantse ko? Wllh ka faɗa min gaskiya ba kuka zanyi ba"
      Kai papiey ɗin ya shiga girgiza mata cike da damuwa ya shiga faɗin. "Basu ce mana komai ba har yanzun Mamamsu. Tun da aka kawo ki nan suka sake komawa ɗakin har yanzu basu fitoba kuma.... Tun kafin ya ida maganar Maah ta miƙe da sauri, Sai dai ta yi saurin komawa zaune tare da dafe kanta da hannuwanta saboda tsananin sara matan da yayi. Saurin riƙota papiey yayi yana me furta "Please cool down Maah"
      Kanta ta ke jujjaya masa tamkar kuma wacce aka zaburo ta furta, "Bazan iya ba Papiey'n Meesherh inaso zanje na ganta ne a duk yanayin da take a ciki zan iya jurewa Meesherh ta kawai nake da buƙatar gani a halin yanzu!"
Chapter 20 · 0% Book details