← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 37

Sashe 14

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwance take saman ƙayataccen bed ɗin ta da ya gama jin haɗuwar duniya da kuma wani irin gyara na musamman, kai ba kace Mutum ne me Numfashi ke rayuwa a gadon ba.
Ɗan juyi ba da yawa ba tayi kaɗan kafin Ahankali ta shiga ware sleeping eyes nata da suka mata wani kalan nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da take gani acikin su ne ya sanya ta maidasu ta kulle, sosai taji kanta na wani kalan bala'in sara mata, wanda take da ta cikakken tabbacin rashin baccin da bata samu ba ne a daren jiya ya haifar da hakan. dan haka take jin gaba ɗaya jikinta yayi weak haɗi da kasalan jiki ga kanta da taji ya dawo mata da wani kalan fitinannen ciwo. Hannu tasa tana ɗan dafe kan dake mata ciwo kaman zai rabe biyu,still idanunta masu kama da na mashayiya ko kalan like irin wanda aka janye su ɗin nan, Ahankali ta ɗan motsa jikinta tare da soma ƙoƙarin ɗaga kanta da takejin yayi mata nauyi sosai,jingina bayanta da jikin fuskar gadon tayi tare da sakin ajiyar zuciya tana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin bedroom nata. Shower kawai ta sakarma kanta tare da tokare hannuwanta duka biyu da jikin toiletry ɗin. haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kanta, jin numfashinta na neman sarƙewa ne ya sanya ta janye jikinta da ƙyar. idanunta da suka sha ruwa sosai ta buɗe tana furzar da ruwan cikinsu. Ahankali ta ziro fararen sawayenta daga cikin bathroom ɗin, Sanye da rigan wanka ta fito komi ahankali takeyinsa, Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin,kai tsaye ta nufi wurin clothing nata da jibgin kayanta ke ciki, walking slowly take tafiyan fuskar nan babu walwala samm ko kaɗan a saman kyakkyawar fuskar tan,Bakar doguwar rigan Arabian jallabiya ta mata ta sanya. Hannunta riƙe da car key.
Bata tarar da Papiey'n taba ya fita wurin aiki amma kafin ya fita seda ya leƙata a loƙacin tana bacci kasancewan se dab da asuba bacci gwanin iya sata yay nasararn sace ta. Maamah na kallonta ta tabbatar ba lafiya ba. Zama tay a kusa da Maamah ɗin tana furta
"Maamah kaina kamar ze fashe ciwo ciwo ciwoooo yake min sosai!!!" Saurin tarota jikinta Maamah ɗin tayi jikinta harna rawa wajen furta "Subhanallahi amma kuma shi ne kika kwana a haka? Meesherh har yaushe kike son zanci gaba da miki magana akan lafiyar jikinki?" Se kuma ta ɗan numfasa tare da furta "Shi ke nan tashi muje Hospital don ni ban woni yarda da cewan azo gida a duba ki ba nima duk yau haka haka nake ji ma wllh ba daɗi" tsaye ta miƙe a sanyayen itama tana furta "A ahh Maah kiyi zaman ki bara yanzu zanje na dawo IN SHA ALLAH"
"Ke Meesherh anya kuwa duba fa yanayin ki sosai baki da lafiya kidai bari ko driver ne yayi driving naki" Dan murmushi tayi tana ficewa da tsokanar Maah É—in. A Parking car na gidan suka haÉ—u da shi kallo É—aya ya mata ya É—auke kansa yana sake jin bugun zuciyarsa da fitowan nata. Akan Idonsa ta shige car nata tayi reverse tana janta tare da barin gidan ba tare data ko kalla inda yake ba.

Cikin nitsuwa shima ya shige tashi motar sanye yake da fararen kayansa kamar kullum. Security's ne suka hanzarin buÉ—e may mitar ya shige personal person É—insa na jan motar suna barin gidan.
Dummmmmmm haka yaji zuciyarsa ya buga shan kwanar da zata sada su da inda suka nufa ganin dandazon mutane fiye da dari kewaye a wuri guda. Cikin bugawar zuciya ya bama driver umarnin su tsaya. Cikin kamala da tattako ya nufi wurin cikin cikakken takun ƙarfi na hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi ɗin Matashi ne mai ji da lafiya irin ta da namiji, se hakan ya ɓoye yawan shekarun sa don idan ka kallashi befi ka bashi irin 35 year's ɗin nan ba a duniya, nan kuwa yakai 55 year's a duniyar. Kowa dake wurin ya gaza taɓa komai dake wurin se jinin dake malala ta ƙarƙashin motar data kife kirif da duk wanda yake a cikin ta. Wani irin jiri yaji ya ɗauke sa loƙacin da idanunsa sukai masa arba da car ɗin kokkomeɗe a wurin.
Chakkk yaji numfashin sa ya tsaya amma yay ƙoƙarin taro shi domin bazai iya taɓa barin nashi numfashin ya fita ba tare daya tallafi Tata rayuwar ba.....

😔😔😔😔😔😔

_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un 3 meya faru? Meke shirin faruwa damu haka?_

The comments are dropping. 😔 ko dai baya muku daɗi ne? Naga ba comments ba reactions naku.

LPlease don't be a silent reader. Comment, vote and share. Thank you.

Love you all my mutanena ƴan Amana😘

_Put a smile on my face please. Vote, comment, and share My lovely friend's ana tare_

# Voice of the innocence
# Team Sheikh juraij

_Team juraij meke meke shirin faruwa daku haka?_

_Laaaaa wayyoooooo wayyo wayyoooooo Meesherh ɗin mu😳😳😳😳_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

07085041758

*༺♡𝕋𝔸 𝘿𝘼𝙱𝔸𝑵☆༻*

_𝘚𝚙ҽcⅈɑʟ _
♡
𝙈𝙖𝙧𝙮𝙖𝙢 𝙉a𝙨𝙚𝙚𝙧 ɱⅈ𝔯𝔯ɑһ

_𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃_

𝙋a𝙜𝙚

11&12

https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D

✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

☆༻ Hakan ya sanya cikin wani kalan sassarfar dashi kansa be san yana da itaba ya Isa ga car ɗin. Idanunsa na rarrabe masa be ma san sanda ya zare babban ƴar cikin rigarsa yay jifa da ita ba. Shi kansa ba zai iya cewa ga sanda ya isa ga motar ba abinda kawai ya sani shidai ya ganshi ɗauke da Meesherh ɗin cikin jini kuma bata numfashi, kana duk da kasancewan shi ba me gyaran karaya bane amma yana da tabbacin kusan duka sassan jikin ta a kareraye suke. Ko kallon gabansa bayyi taku kawai yake a farfajiyan filin wurin da mutanen suka zagaye. Idanunsa da farat ɗaya suka sanja ya ɗago yana watsawa wasu daga cikin tsirarin mutanen da suke faɗin kada ya taɓa ta ya sauƙe ta ya bari police suzo. Ko kafin ya isa ga motar'nshi tuni Personal person ɗin sa ya buɗe may motar. Yana ƙoƙarin shiga ya dakatar da shi ba tare daya furta masa ko ƙala ba.
Da wani kalan bala'in gudu na fita hayyaci ya fige motar wanda harya tsorata Personal person É—in sa Al'ameen Hafeez dama wasu daga gurin, tun da ya taka kan motar yake wani irin bata wuta na fita a hankali. Kai tsaye S Power specialist hospital ya nufa, A wani kalan tashin hankali ya taka motar yana fitowa a tsiyace.
Cikin tafasar jini yake takunsa Meesherh ɗauke a hannayensa ganan jini se malali yake daga jikinta. Amma hakan sammm be dame shi duk nurse ɗin da yaci karo da ita tayi ƙoƙarin amsanta amma seya kauce ma hakan amma basa daddara haka wasun su ke sake nufo shi kasancewar sa sanannen mutum da gari dama duniyar ke wani irin karrama shi da girmama shi a matsayin sa na babban malami.
Shi kansa ba zai ce ga randa ya taɓa shiga tashin hankali kwatankwacin wannan ba.
Chapter 14 · 0% Book details