← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 37

Sashe 12

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don ganin Papiey'nta da tai zaune cikin car ɗin, duk da cewan ba abin mamaki bane a wurinta amma na yau ɗin se ya fi koda yaushe bata mamaki. Wata kyakykyawar ajiyar zuciya ta sauƙe me ɗan ƙarfi tare da nufo car ɗin ita da jaruma Khadijah yobe. Itane ta buɗe mata gaban motar kusa da Papiey'nta ta, car key nata ta miƙa mata bayan ta gaida Papiey'n tare da cewa tayo dropping car ɗin zuwa gidan su tun da dama ba sa da woni tazara sosai. Itama Khadijah yobe ƴar masu hannu da maiƙo ce sedai idan dasu Meesherh Jedaans a wuri babu Powerful ɗin kowa da ke aiki a kafff ma faɗin garin Kd da zagayenta.
"Papiey yau ka tuna dani kenan?" Shi ne tambayar data fara jefa ma mahaifin nata Duk da tasan cewan tasan kwanan zancen ba zai wuce sake kwantar mata da zuciya da zai yi ba. Left hand nashi da baya driving dashi ya sanya yana kama nata tafin tare da jimƙewa a cikin nashi, cikin tsananin jarumta da ƙarfin hali da kuma son kwantar mata da hankali ya furta. "Baby ita Rayuwa da kike kallo komai yana zuwarma bawa ne ga bisa umarnin abinda ya tsara a cikin tarin Rayuwarka! Ina son kici gaba da shanye komai da zakici gaba da fuskanta daga can gida, amma ba ta yadda komai ɗin ze zama illa wa taki Rayuwar ba. Insha Allah wannan karan komai ya kusa daidaita da yardan me du ka wato Ilahu Sarki ALLAH, Sarkin da babu kamarsa buwayi gagara misali ina..jin... Ina...jin...ina.........jin matuƙar ciwo sosai da ɗaci kan aibantamin MY BABY'n Papiey da ake...
Muryan shi ce ta soma rawa da ƙoƙarin karyewa dan haka yay shiru yana sake damqe hannuwan Meesherh ɗin da ɗan ƙarfi yana qasa da idanuwansa da suke neman cikowa da hawaye. Don sosai Maganan Anniey ya buge shi se dai samm baya taɓa damuwan komi akan face nashi kan duk wani mahluki dake cikin estate ɗin nasu koma na ce family.
Jin rauni ya wanzu a cikin muryan papiey ne ya sanya ta itama É—in sake kame hannuwansa cikin nata ta na kasa cewa komai dan tasan kuma ba zai iya ci gaba da maganan ba kenan.
Ɗan lumshe fararen idanuwanta tayi A bayyane kuma ta shiga furta adda'ar "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata tare da sauran adda'o'in da duk suka zo cikin bakinta. Ajiyar zuciya me sanyi papiey ɗin ya sauƙe a natse yanajin hankalinsa na dawowa jikinsa take yaji dacin zuciyarsa ya ragu sbd yadda adda'o'in data karanto ɗin suka ratsa shi sosai tare da zuciyarsa.
slowly kuma ta shiga ware idanunta tare da sake sanya hannunta tana jinginar da kanta jikin papiey ɗin nata, daga haka tafiyan nasu ya koma na kurame har suka ƙara so mahaukacin estate ɗin su, Shi ya fara fita jikinsa duk a wani kalan amma yadda yake tafiyan cikin nutsuwa kai kace babu abinda ke damun Rayuwar sa nan. Lugagge bag na papiey kawai ta dauke se handbag nata tana bin bayan mahaifin nata. tana tafiyar ne kuma tana ɗan shedding tears nata zuciyan ta na ƙara yin nauyin abubuwa da yawa da suka kanainaye cikin rayuwarta.
A bakin entry na babban parlour'n gidan sukayi kiciɓus da Moh Ameern Saif inda ita ta tura shi kuma ya turo. Kin sakin ƙofan tayi tana kuma ƙin kallonsa, sake murɗa handle door ɗin yay yana jan ƙofar baya ya kuma ja ya tsaye yana ƙare mata kallo tun daga samanta zuwa ƙasa. A ɗan kausashe ta furta "Moh Bani hanya"
Ɗan girgiza kai yayi kawai tare da ɗan taunar lisp nashi, Wani shegen killer smile yayi tare da ɗan shafar gashin ƙeyarsa yana me furta "Ohh Ohhh beb wai cikin sauƙi haka?" Yay tambayan cikin ɗan iskan salon jan hankali da kuma rashin mutumci. Chakkk ta tsaya daga ƙoƙarin raɓa gefen Moh Ameern ɗin da take niyar yi. Sakamakon tausasan hannuwan da taji ya raba tsakanin su ta hanyar janye ta daga niyar shigan, ko bata juyo ba ZUCIYAR TA ta riga da ta gama sanar mata ko wa ne ne. Hakan yasa ta jan idanunta ta lumshe su gaba ɗaya. Moh Ameern daya ƙame cike da tsoro da kuma kafe Sheikh juraij ɗin da ido yake kallonsa, Shima idanuwansa da suke a rufen ya buɗe tarrr akan Moh Ameern. Kafin ya saki wani murmushin rainin wayo tare da zamar da ƙasan lips nashi ya furta. "Shi kuma wannan ko a cikin wanne hadisin ne ko sura ohooooo, amma ko ba komi abin ya bada gitta da ƙyau Sheikh babban salo!!!"
Haka muryan juraij ɗin ya dake shi Sheikh juraij ɗin. A natse ba tare da garajen komi ba ya rabata da jikinsa yana jefawa Moh Ameern ɗin wani kalan mugun kallo me tattare da cikakken gargaɗi. Ita ne ta fara barin wurin tana jin yadda ƙirjinta ya ɗan ƙare mata tare da mata wani kalan nauyi wanda dama har yanzun bawai ta gama warkewa bane rass.
★A ƙaton parlour'n su wanda yake ɗauke da duk wani nau'in jin daɗin rayuwa ta tarar da duka su Maamah har dama ƙarin babbar yayarsu ummeterh. Da sauri ummeterh ta nufo ta tare da riƙe hannunta fuskanta ɗauke da kyakykyawan Murmushin da ya sake fidda tsananin kamanninsu kasancewar su duka Ukun kamanninsu ɗaya. "Ma sha ALLAH Dear lallai jiki yayi sauƙi tunda har aka iya fita shooting yau" ɗan murmushin yaƙe tayi tana shafa kan baby'n nuwaira da ita ma ta nufo su fuskanta cike da farin cikin ganin Aunty Meesherh ɗin. "Dama ay duk laifin Maamah ne banda haka ai naji sauƙin sosai!" Maama'n da itama ta taso daga idda take zaune ne ta dawo ɗayan gefen Meesherh'n ta zauna ahankali tare da dafata fuskan ta da ɗan murmushi ta furta "Ko yanzu nasan babay'n papah ba ta da cikakken lafiya kawai dai kina danne hakan ne na sani"
"To banda abinki Mamman'su Karfa ki manta Meesherh fa ita ma ce ce wata rana haihuwa zatay, tun daga yanxun idan bata koyi ƙarfin hali ba se yaushe kike son ta koya?" Papah ya bata amsa da hakan yana hayewansa sama. Mohan Sameer da shigowansa kenan parlour'n shima yama kansa mazauni akan ɗaya daga cikin expensive chairs da suka ma parlour'n ƙawanya. Yana ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana fuskantansu su duka cike da farin cikin ganinsu su dukansu. Aunty Ummeterh ya fara gaisarwa kana ya sake gaida Maamah duk da kuwa cewan babu jimawa suka Hausa ɗin. Lil juraij dake riƙe da hannun Mohan ɗin ne ya zame cikin wayonsu irin na yara kai tsaye ya nufi inda Meesherh take, duk kuwa da yadda take ƙoƙarin ɗauke fuska daga yaron,cikin muryan gyaranci ba sosai ba ya ce "Otty kin ga ni paap ne ya bani kuma yace karna fatawa kowa ma" yay maganan cikin gwaranci ba sosai yana mata nuna da wani Rolex watch na diamond gold me kyau kalan na yaran nan me shegen tsada da kyau. Ɗan taɓe baki Maamah tayi tana juyar da kanta daga kallon yaron tana maidawa kansu Ummeterh da Mohan da suke wata maganar daban.
Miƙewa tayi da niyar tafiya amma lil juraij ya maƙale mata duk yacce ta so data yagar dashi kuwa. Gashi zuwa loƙacin kanta sosai taji yana juya mata gashi wasu masallatan harsun fara ƙiran sallah, dole dashi ta tafi sama yana maƙale da ita. Duk da ido suka bita kafin Mohan ya kalla Maamah tare da furta "Maamah don ALLAH Meesherh ta dakata da aikin nata don yanzu kamata yay ace tana gidan aurenta, Ki duba fa tana age na 24 year's ba ai yaci ace ma tana da nata babay'n itama" tunda ya soma maganar Maamah ta kafe shi da ido ko ƙiftawa batayi seda ta tabbar da ya gama ta furta.
"To sannu ubana da wannan ai kamata kawai yay ka bani umarni, ka ga Mohan ka fita ido na In rufe idan har kaima ba zaka iya bin Meesherh da fatan Alkhairi ba to kamata yayi kaima ka janye idanuwanka daga gare ta" ta ƙarasa maganan a fusace tana miƙewa tare da barin parlour'n baki ɗaya, don Maamah irin iyayen nan ne masu shegen S0n ƴaƴansu wanda basu ganin laifinsu ko kaɗan, se dai sammm bata barin ko waye daga cikin yaran nata ya aikata ba daidai ba kuma ita mutum ce da bata iya ƙunbiya ƙunbiya da abu ba ita ɗin karan tsaye ce ƴar kai tsaye me gaɓa². Ko waye ya taka ta to kuwa lallai itama zata taka shi don bata ɗaukar raini kamar yacce itama bata raina kowa se har in mutum shi ne ya fara shiga hurumin ta da wata sigar ta daban, to kuwa lallai anan ne zaka gane ko kai ɗin wane ne.
Ajiyar zuciya me tattare da damuwa Ummeterh da Mohan Sameer suka sauƙe kusan loƙaci guda kan kalaman mahaifiyar nasu, duk kuwa da cewan ba yau bane suka saba fuskantar hakan daga gareta. kawai abinda suka sani suke kuma so shi ne suga sun inganta rayuwar Autar nasu, sun gaji da ce ce kucen da ake akan Meesherh ɗin daga media harma da nan cikin gidan nasu kuwa. Tabbas hakan na masu ciwo da kuma matuƙar ƙona musu zuciya.
†
*Sheikh juraij*
Tunda yabar wurin kai tsaye cikin garden yay shigewansa, sanyi da kuma iskan dake kaɗawa a wurin na ratsashi wanda har yake jin kamar fatar jikinsa ce ta bude kai tsaye sanyin yake ratsa masa ko wanne sassa na jikinshi yana daskarar da duk wata magudanar jini ta jikinsa, kamar kullum yana sanye cikin shigar farin yadi me azabar laushi da tsada ɗinkin jumper cables irin na zamanin nan amma kuma ba masu sherp da yawa ba irin na matasan yanzu. Sumar nan tasha gyara na musamman se fidda daɗdan ƙamshin take yi gami da daukar ido. Sajen nan yay luf luf abunsa har wani kalan shine blue yake bayarwa daga nesa.
Sanyi haɗi da daɗin iskar ne ya sanya shi kasa zama wuri guda don haka ya shiga zagaye cikin garden ɗin,Hannuwansa goye a bayansa daga can ƙasan zuciyarsa kuwa yake furta.
_Subhanallah,wal hamdu lillah, wala'ila ha ilallahu wallahu akhbar³_
Chapter 12 · 0% Book details