← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 37

Sashe 18

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

★
Wannan maganar fitan da yaje kunnan Maah itace ta sake saka zuciyarta damuwa da ɗaukan wani irin nauyi tamkar wata zararra haka take jin kanta gani take yi tamkar komi ba a zahiri yake ba, gani take data rufe ido ta buɗe komi ze dawo mata Normal Kamar ba'ataɓa yinsa ba.a take takejin komi na shirin kwace mata kanta kuma na mata wani irin bala'in sara mata, ita kanta bata san sanda ta fasa kukan da babu mai jinsa ba bayan Allah da take fatan ya sassauta ma Rayuwar Meesherh. Don haka dole take son ƙarfafa jikinta kodan ai tafiyarn da ita don tasan halin Sameer akan taurin rai tsaf zaice bazata jeva, ita kuwa a wannan halin da Meesherh'n take ciki bata ga uban da isa hana mata binsu zuwa ko wacce ƙasa bace.
Dake dama already an riga an shirya fitan tun a daren jiya ya sanya
babu ɓata loƙacin komi aka fara shirye shiyen tafiyan.
Daidai da shigan sa cikin room ɗin daidai ake gangaro gadon da take kwance sanɓal ana tura ta dashi, komai nata a rufe ko fuskanta ba'a iya gani saboda kwata kwata tun jiyan ko motsi babu inda yayi a jikinta.yadda jikinta kuwa ya koma iyaka na jikinta kaɗai sune suke iya gane ta, domin kuwa duk kamanninta sun ɓace ɓat.Wani kalan rumtse idanuwansa yayi da suke sake sauyawa ƙirjinsa na wani irin bugu gaske ganin yau wacce yake ma kallon tamkar duniyarsa ce kwance a hali na mutuwa irin wannan, wanda idan aka ɗauke mahaifiya mahaifi a gareshi to kuwa Meesherh itace abu na farko da yake so fiyeda komai a rayuwarsa da komai daya mallaka, duk kuwa da cewan a yanzun duk babu wannan amma yana da tabbacin har yanzu zuciyarsu da ruhiznsu a tare suke rayuwa.
Jin yayi zuciyarsa na neman bugawa dan haka ya sauƙe wani irin numfashi me zafin gaske ya ɗago ahankali ya zubama Gadon da yay masa nisa idanuwansa sai yaji zuciyarsa na sake ƙoƙarin bajewa a wurin.Da hannu yama masu tura gadon alamun su dakata, a gabanta ya tsaya su kuma yana basu umarnin tafiya. zubawa fuskanta da yanzun ya ɗan zama ido yayi yana mata wani irin kallo me cike da tsantsan tausayawa,ƙauna, soyayyar da yake tunanin ta jima da mutuwa babu ita. Tin daga fuskanta yake kallon har zuwa iyaka shahsin daya buɗe ji yayi zuciyarsa na nauyi da kallonta a hakan, ashe dama bugun zuciyar daya taji akan tane kenan? Ashe wannan mummunan ƙaddarrar ce zata faru da ita shi yasa ya gaza runtsawa a daren wancan ranan? Ashe dama ashe dama ashe dama abubuwan da yawa har haka? Ashe ƙaddarorin masu girma ne har haka. Ta ita ya fara tafiya yana gungura gadon yana wuce sauran family's nasu. Duk suka rufa mashi baya suna jin tamkar abu mafi muhimmanci na shirin rabuwa dasu ne na har abada.

acikin series car aka jagoranci tafiyan nasu su uku kawai, Shi kansa uban gayyar se kuma Maah data dage dole itama se taje. Thabit Jedaans ne yace ma Sameer Jedaans ɗin kawai a tafi da ita daga nan se itama a duba ta tunda jikin nata babu daɗi itama. Hakan kuwa akai kai tsaye ta Lagos jirgin nasu ze tashi tacan jirginsu ze lula zuwa ƙasar Spain ɗin. Seda gaba ɗaya katafanin ahalinn Jedaans suka ma su Prof Sameer Jedaans rakiya har Lagos. Buɗe idanuwansa yayi ahankali tareda zubawa jirgin su daya fara landing na tashi yana kasa tantance a wanne mataki ya kamaci ace ya dauki hakan. Zurfafawan da dole dole yake son zurfafa Kansa ne ya sanya Wani irin ciwon kai dirar masa irin na loƙaci gudan nan. lumshe idanuwansa da suke masa zafi yay Mohan Sameer ne ya taimaka mashi wurin kaisa cikin car ɗin
♡
Tunda suka baro cikin airport ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe suma. Bakinsa ne kawai ke motsawa alamun tasbihi yake a cikin zuciyarsa.
        Duk yanayin da yake a ciki Mohan na kula ta cikin mirror'n hakanne ya sake sanyaya zuciyarsa akan du abubuwan da suka ringa faruwa. Haka dai sukaci gaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai da ruhinsa.Hakan ne ya sanya Mohan sake gudun motarsu sosai kai kace Jigawa suka nufa ba Kaduna ba. Tun kan 4pm tayi suka isa gida kai tsaye seda ya fara biyawa ɓangaren anniey kai tsaye loƙacin tana sama wurin Daddy, se kawai yay kwanciyar sa kan lallausar doguwar kujerar parlour'n ya fidda woyarsa yana saka ƙiran Hafeez Al'ameen a woyan. Babu jimawa kuma sega Anniey'n ta fito daga saman sanye cikin shiga ta alfarma kamar koda yaushe. Zaune ya tashi daga kwancen da yake gaidata yay ta amsa shi sama sama, daga haka taja bakinta tayi shiru se can kuma tamkar wacce aka tsikara ta ɗan dubeshi tare da sake tamke fuskanta me kyau sakk kalan tashi ta furta. "A ina maganar mu ta kwana" wani irin janye idanunsa daga kanta yayi yana jin yadda tambayar Anniey'n ta taɓa har cikin tsaƙiyar ƙirjinsa, uwa uba ga ciwon da kansa ke mai. "Anniey pls mubar wancan maganan don ALLAH!!!" Ya kai ƙarshen maganan cikin raunin murya sosai. "Auren Ƴar ƙanwar tawa kake cewa na ƙyale juraij, to wllh³ bara kaji na rantse sau uku to wllh seka auri Samha kuma nan da kwana kusa" fuuuuuu tabar wurin don sosai kanwar nata keta faman mata naci akan batun tare da sake hurata da rura mata wutar tsanar Meesherh da uwarta a cikin zuriyar ta. Sheikh kan tun da ya fita a gidan be sake dawowa ba se araoun 10pm wanka ko zaman dinner yau be yi ba tunda be shigo gidan bama. Ransa a jagule haka ya shigo gidan ko inda sassan mahaifansa suke bai nufa ba yay wucewansa nashi ɓangaren.
Tura ƙofar bedroom nashi yayi ahankali sanyin a/cn da kuma ƙamshin turarensa da baya taɓa ɓacewa na sake gauraye room ɗin baki ɗaya, kai tsaye bathroom ya wuce ya shower ya sakarma kansa ya fito jikinsa sanye da bathrobe. Fararen riga da wando na bacci dogaye ya sanya kai tsaye kan lafiyayyan gadonsa ya yay kwanciyansa yana dunƙulewa cikin fari ƙal ɗin duvet cover.
Kafin kuma Ahankali ya sanya hannunsa ɗaya ya janyo ɗayan pilonsa ba tareda ya buɗe idanunsa ba ya toshe kunnuwansa dashi saboda yadda kawai yanayin jikinta ke sake damun zuciyarsa, wajen karfe biyu da rabi na dare ake magana amma ya gaza yin bacci don haka ɗaura alwula ya dinga jera nafilfili tare da jera mata adda'o'in samun sassauci wa rayuwarta, ƙarfin ciwon da kansa ke masa na sake hauhawa.
Chapter 18 · 0% Book details